← Book details Hamshaƙiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 31

Sashe 3

Hamshaƙiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tace "To abinda za ki yi ƙoƙari ki gano shine waɗanda za a baiwa wannan dubu ɗari ɗarin domin tabbas na wasu ne daban kuma ana haɗa musu da kayan abinci sauran mutanan kuwa sai ki kira su tunda akwai suna da kuma lambar waya sannan ki tabbatar ba ki ba wani naki ko mu wannan kayan abinci da kuɗi ba."

Nace Haba Umma hauka ake, duk yadda za ayi dole in cire muku kuma,shirme kenan zan yi cewa fa aka yi duk yadda nayi daidai, banda ma tsoron Allah harni sai na ɗauki kashi ɗaya. Umma tace "Baki da hankali, ko ƙwayar gero kar ki sake ki aiko mana da shi. Ki bi list ɗin da ta baki, abinda za kiyi kawai shine ki ki fara da kiran lambar farko kiji waye a haka sai ki ware waɗan da zaki ba kuɗin, amma ki bari sai ranar lahadi tunda kince baya fita da wuri." Nace to zan yi haka amma zan kira su kafin ranar in sanar musu

Da safe da naje gaida Hajiya bayan na gaishe su har zan miƙe sai tace "Ranar yaushe za ki yi rabon zakka?" Na sunkuyar da kai nace ranar Lahadi. Tace "Nan da kwana hudu kenan me yasa ki ka kai shi har wannan kwanakin?"
Nace ina son in gano suwa za a ba wannan kuɗin ne. Ta ɗan yi jim sannan tace shike nan Allah ya taimaka. Shamaki ya matso kusa da kunne na "Jiya me ki ka sha ne na yi miki tashin duniyar nan amma ki ka kasa tashi?" Na rage murya nace na yi shaye shaye jiya irin su ruwa da lemo.muka sa dariya.
Nace na jira ka har kusan ɗaya baka shigo ba,bacci mai nauyi ne kawai. Yace "Dama maganar da kika ce za mu yi ce na so in tashe ki." Da gefen ido na kalli Hajiya kuma na gane hankalinta yana gurinmu. Nace ba fa wani abu bane,kawai ina so ne inji muryar ka, ko zanji sanyi a zuciya ta. Yace "Zafi ta yi a lokacin?" Nace ƙunar sonka ba. Ya ɗan kai min dukan wasa,yace Me wayo zaki faɗa min gaskiya bari in shigo. Na tashi na koma ciki.
Na ɗauki takardar ina ƙara kallon ta. A fili nace banda Hajiya ta so wahalar da ni, ai da sai tace kawai da sai ta faɗa min cewa kuɗinna wane da wane ne.

Na kira lambar farko Na miji ya ɗauka kuma da alama dattijo ne. Muka gaisa, nace daga gidan Alhaji Baita ne don Allah da wa nake magana? Sai aka ce "Da liman ne mai jan salla a masallacin gidan. Nace to ranar Lahadi za ka karɓi saƙo. Yace to Allah ya kai mu."

Bayan mun gama waya nace ina ruwa na Allah duk wanda yake sahun farko shi zan ba kuɗi kuma in haɗa masa da abinci.

Na kira na biyu shima na tambaya kamar yadda na yi na farko. Akace wacece baki gane da wa ki ke magana ba? Nace Matar Shamaki ce. Sai yace auto Babanku ne ƙanin Hajiya. Nace Baba ranar Lahadi za a bada saƙo, yace to "yar nan mu zamu zo mu karɓa? Nace Baba ya ake yi muku ne kawowa ake yi ko ku ke zuwa? Yace "To shekarun baya dai can kafin rabon ya koma hannun matan Shamaki direba ke kawo wa Bama sanin cewa za a bamu amma daga baya sai ace mu zo mu karɓa."
Cikin zumuɗi nace acan baya ɗin me ake baku ne Baba? Yace "A can baya dai dubu dari da buhun shinkafa da suga da gero. Nace to Baba bana ma ba sai ka zo ba, za a kawo maka kamar yadda ka lissafa. Yace to Allah ya yi albarka. Nace Ameen yace akwai wani ƙanenmu a ƙauye shi an daina bashi ma gaba ɗaya,kuma da har shi Hajiya ke bamu. Nace to za 'a bashi ya zo ranar lahadi ko shima kauyen ake kai masa da? Yace A'a gidan yake zuwa. Nace to.
Wato ashe dai lissafin Umma haka ne da nayi ta bin lambar har shi na ƙauyen nan na samu lambar ɗansa, sannan sai ga su Juma na kira ta ɗaga tana cewa wacece? Na ɗauki murya nace Baba Juma ce tace e, sai kawai na kashe domin na gane. Munan duk makusantan su ne 'ɓangaren Alhaji Baita da ita Hajiya Zeena, sannan 'yan aiki.
Bayan na gama da ishirin ɗin nan sai na koma in gano sauran me za a basu, nace irin dai wancan tsarin zan bi innaji a bakin mutum ɗaya shike nan.

Na kira wayar na ishirin da ɗaya. Muka gaisa mace ce, nace an kirata ne daga gidan Alhaji Baita,tace to Hajiya ce ina yini,ta sake gaida ni cikin girmamawa. Nace na san kin sani zakkar abinci ce ko? Tace e nace me ake baku ki faɗa min gaskiya domin akwai waɗanda za a soke sunan su in sun faɗi ba daidai ba.

Tace tsakani da Allah da dai can ana bamu shinkafa gero sai suga mu biyu buhu ɗaya ni da wata itama 'yar uwarmu ce, kuma ana bamu taliya. Nace kuma 'yan uwan Hajiya ne? Tace a a mun yi aiki shekarun baya can tare da Hajiya Gwamma mahaifiyar Alhaji Baita lokacin muna ƙananan yara, shine Hajiya Zeena ta riƙe alƙawari ake bamu, duk shekara sai anzo har gida an karɓi lamba. Amma 'yan shekarun nan gero ake bamu da shinkafa. Wannan lambar ki ce? Tace ta jika ta ce. Nace ku zo ranar Lahadi tace sai dai in turo jikata Dan ni sai bakin da kunne ba ido ba ƙafa, Nace Kaka ya sunan jikar ta ƙi? Tace "Mairamu zan turo ita mijin ya mutu ya bar ta da 'ya'ya." Nace ki faɗa mata in tazo tace tana son ganin matar Shamaki. Tace to zan faɗa mata, inaha Allahu 'yar nan ke ce matar Shamaki ɗin?" Nace E ni ce Kaka. Tace Ikon Allah ɗannan tun yana goye rabon da in gashi. Na yi dariya muka yi sallama. Haka nayi ta kira ina sanar da su suzo ranar Lahadi har na gaji na yi makin ɗin inda na tsaya.

Washe gari sai da na gama komai mijina ya fita sannan na koma na ɗora, zuwa washe gari duk na gama sanar da kowa.

Ranar asabar na idar da sallar azahar ina kan sallaya ina danna waya na ga ansani a wani group na duba admin ɗin sai na ga wata 'yar ajinmu ce ta boko Basira Ashiru na sake duba sunan group ɗin sai naga an saka Gandu 2019 nace la group ɗin 'yan makaranta, gaskiya na ji daɗin domin za a sada zumunci.

Wayar gida ta katse min tunani da ƙara, na san Hajiya ce, na daga na gaishe ta. Ta amsa, sannan tace, "Kina ji na ko?Ki fito ga waɗanda zasu taya ki aikin gobe sun zo, ki zo ki basu Umarni yadda za su miki aikin." Nace To. Na samu maza majiya ƙarfi su biyar. Suka gaishe ni cikin girmamawa har naji kunya. Hajiya tace ki je ki basu abinda za suyi su fara tun yanzu, bana son sai gobe a cika mana gida kamar kasuwa fatan kuma ki fidda tsarin da wani ba zai amsa so biyu ba. Nace Insha Allahu.

Na dube su nace muje can gurin da kayan abincin suke. Suka fita dan su zagaya. Dama da hijabi na na fito sai na koma ciki na ɗakko takardar sannan na ɗakko wata takardar da biro na dawo na bi ta kicin na ce da Baba Juma ta zo muje...
🖊️🖊️🖊
️Na nuna musu abincin nace ina son su ware min buhun shinkafa guda tamanin, ko wanne su saka taliya da makaroni da gero sannan ina son su ware min suga buhu arba'in. sannan su cire min ashirin, shima su ware su sa taliya da makaroni da gero da buhun suga in sun gama ina son su faɗawa Juma ta sanar da ni.

Juma ta kalle ni. 'yar nan jiran su zan har su gama kafin in koma ciki?"
Nace kije za su sanar da ke in sun gama.
Tace "Ko da dai bari in tsaya in yi gadi domin kar ace ba wani buhun lissafi ya sha banban." Ɗayan ciki yace tsohuwa nan da ki ka ganmu duk ciki babu ɓarawo, da sana'ar mu inda halin mu ke nan Hajiya ba za ta ce Alhaji ya turo mu ba, duk shekara mune ke yin wannan aiki. Kuma ko a kasuwa mu ne 'yan dakon kayayyakin Zeena. Tace to naji Allah ya baku haƙuri amma dai ina nan sai kun gama. Na tafi ina dariya. Nace Baba Juma ho!
Chapter 3 · 0% Book details