← Book details Hamshaƙiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 31

Sashe 13

Hamshaƙiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Wata asabar ta karshen mako, ya fita motsa jiki da safe, lokacin da na fita gaida Hajiya baya gurin, na zauna na gaishe ta, ta amsa, zan tashi tace ina da magana da ke, gaba ya fadi, na koma da sauri na zauna. Tace "Da anyi babbar salla da sati daya za a daura auren Azima da Shamaki. Na hadiye yawu da kyar, tace gaba, "zai aje ta a daya daga cikin gidajensa dake unguwar nan ko kuma wata unguwar dake kusa da wannan, amma kije ki yi shawara in ke ce ki ke son ki zauna a can to na baki kwana biyu ki yi tunani ki zo ki fada min . " Na ce ba sai na yi wani tunani ba, duk yadda ya yanke ai shine mai gida.
Hajiya
Tace "Kije dai ki yi tunani karki yanke shawara cikin fushi, yau saura kwana arba'in a yi biki, bana son danasani ne a rayuwa, kuma bana son yin abu ba hujja shiyasa na baki dama, kiyi tunani kuma ki yi shawara a inda ki ke da yarda da aminci. Bana son jayayya ba halinki bane kije sai na jiki.
Na ce to na tashi na nufi daki jiki ba karfi. Nafada kan gado na saki kuka, bansan ina son Shamaki har haka ba. Hajiya bata san zafin kishi ba tunda ba ayi mata kishiya ba. Shiyasa take fada min maganar auren mijina kamar yadda zata fada min abin arziki. Na dau lokaci ina yi sannan na lallashi kai na, na nufi dakinsa don inga ko ya dawo. Ya kashe wayoyin sa ya zube su a kan gado. na kunna wadda nake bincike na shiga ina bi, har yanzu dai yana nan akan halinshi akwai wadda na lura sun dinke da alamu yana matukar son ta kuma ya nuna ya matsu su hadu. Na dakko wayata na dauki lambarta. Na saka wayata na kashe masa na koma daki. Ina ta shawara in kira ta ne ko kuwa in goge, me yasa nafi kishin wadannan matan wajen akan Azima wadda zai aura.
Nasan yana fada min kalamai, amma meyasa baya fada min irin wadanna. Me yasa ina masa duk yadda yake so koda ni bana so amma hakan bai hana shi bin matan baza ba.
Na kira Umma muka gaisa na fada mata cewa maganar auren Shamaki ce saura kwana arba'in yau. Sai naji zuciya ta ta karye, na soma kuka. Umma Cikin sigar lallashi tace menene abin kuka, ki share hawaye mu yi magana. Nace Umma wadda aka yi wa kishiya kawai zata iya gane me nake ji a halin yanzu. Umma tace, "Ni dan ba a yi min ba shine yasa bazan fahimci radadin da ki ke ji ba? " Cikin kuka nace Umma kirjina kamar zai fado, ni sai inji ma kamar ince masa ya sawwake min, ina cikin damuwa Umma. Tace "Amma ban taba jin ance wata ta fadi ta muru dan kawai anmata kishiya ba. Dan haka kema bazata gagare ki ba, abu ne ma kowa ya zauna da halinsa. Shi mijin naki ya canza miki ne? Nace A'a bai canza ba. Shi ko maganar so daya ya min, Hajiya ce tana fada min kamar mai fadin alkhari ko a mijinta. "Umma tace alkhari ne mana insha Allahu. Ke dai ki kwantar da hankalin ki kar ki nuna cewa abin ya dame ki ko da wasa. Ki zuba ido akwai Allah Karki yarda ko da kalmar magana ki cutar da wani, ki sa zuciya daya tsakanin ki da kowa, kuma gara a ce kai aka cuta da ace ka cuci wani. Nace insha Allahu. Yanzun ma Hajiya ce tace wai wani gidan za a kai Azimar amma in ina son ni a kaini can to inyi shawara ni ina ganin gara in bar gidan nan domin Hajiya ni ba wai ina son ganinta bane tunda ta min wannan maganar.
Umma tace ko kusa karki matsa ko ina. Hajiya tana bukatar ki kusa da. Ki nutsu ki fahimci maganar, Zai aje amarya a wani gida, amma in kuma na so sai ke ki koma can. Ina fatana kin gane cewa can din ba naki bane. Nace shikenan zan zabi nan din. Tace yawwa Allah ya miki albarka ya baku zamavlafita dukanku. Na cw ameen. Na dan samu sauki da Umma ta taushe ni. Idanu sun min jawur fuska ta kumbura. Na koma kan lambar yarinyar nan. Na yanke shawarar in kira ta. Na kira tayi ringing ta katse a na biyu sai aka daga, bance komai ba na yi shiru sai naji ance "Waye ne.? " Gaba ya fadi kunsan muryar wa naji??

Muryar Azima naji wadda na yi sauri na kashe jiki na ya kama rawa yanzu Shamaki saboda Allah ya yi wa kansa adalci kenan? Na yi shiru ko zan iya tuna kalaman da suka yi musaya na batsa. Na mike na nufi dakin dan in sake dubawa, muka ci karo da shi a corridor din dakin. Muka kalli juna. Yaune na fara jin wani abu na tsanarsa a zuciya ta na kauda kaina sannan na juyo Yace "Baby/" Na tsaya can ya tako zuwa gurin ya kama kafada ta ya juyo da ni, ya dago fuska ta "Kukan me ki ke yi? "
Nace ni banyi kuka ba. yace "kar ki yi min karya ga nan fuskar ki a kumbure." Na ce bacci na tashi. Ya ja hannu Na muka nufi dakin shi. Bakin gado ya zaunar da ni wai in fada masa me aka yi min. Na kafe akan ba komai har ya fara fusata, yace shine nan tashi kije tunda kin kafe. " Na mike na nufi dakina, dama ni zantukan shi sun dame ni. Na kwanta ina mai bankin cikin auren Shamaki da na yi. Yanzu banda ta'addanci me zai sa ya lalata rayuwar Azima. Aure za su yi amma yana son ya lallaba ya lalata auren ta hayar kwanciya da ida. Wai shi baya jin kunya ne sam? Wannan ce rana ta farko da na ki fita gurin saka musu abinci domin kowa na gidan haushi yake bani. Na kwanta na rufa.
Chapter 13 · 0% Book details