← Book details Hamshaƙiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 31

Sashe 7

Hamshaƙiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Haka aka ci gaba da bikin salla, nace yaushe zamu gida? Yace in jira "yan uwanshi su zo. Sai uku ga salla suka zo, muka sha yini. Shine ya kawo min sabbin kudi 'yan ɗari biyu wai goron salla na shi kuma inzo in bashi nashi. Na zata wasa yake sai naga ya maida makullin ɗakina ya murɗa, yana faɗin yau a ɗakin nan nake shi'awarki, ga ƙamshin ɗakin ga ƙamshin mai ɗakin zan rufe ne saboda yaranki da zasu zo suna kiran Momy."Ni dai Nayi murnar kuɗi ina ta godiya har sai da ya fara nuna rashin ya ɓaci. Nace amma dai ka bari su tafi zuwa dare sai in baka goron sallar ka ɗin. Yace har yau kin kasa gane cewa mu maza in shi'awar mu ta taso bata komawa ko?"Na faɗa jikinsa,a zuciya ta ina faɗin kar a kaita wajen matan banza. Bayan na fito sai na koma gurin su,Maman Nana tace "Wai ina ki ka shige bacci ki ka yi ne ki ka share mu ana hira." Maman Umar ta ce "kai! Ke kuwa kin cika bincike, agabanki Shamaki ya kira ta f." Sai ta ce "O haka na manta,sai suka sa dariya. Na yi ɗan murmushi tare da faɗin kai Anty ba wani abu bane fa, saƙo ya bani. Maman Umar tace "E ai mun sani." Cikin kunya
Na ja Naman Iman gefe nace Anty Maman Iman dan Allah Hajiya tace duk abinda ake yi muku da salla in kuzo a yi muku,shine nake son ki faɗa min abinda ake muku? Tace ba a mana komai ai kin mana komai anci ansha anyi wasa da dariya ai shine abin daɗin. Karki damu. Yara dai take bawa ɗan goron salla na sabbin kuɗi." Nace Nawa nawa? Tace duk yadda ya zama rabon su." Haka na ɗauki kuɗin na rabe musu dubu ishirin ɗin,amma da niyyar zan ciri kuɗina a wancan account ɗin tunda Nima ai zanje gida. Washe gari na tambaye shi yaushe zanje gida? Yace "inje, duk lokacin da na shirya. Na fara murna sai ya ce, "Amma kina ganin ya dace ki tafi Hajiya bata dawo ba? Kinga gidan nan a hannun ki yake,in Hajiya ta dawo baki nan fa?" Nace ai zata faɗa in zata dawo ko? Yace "Inji wa? Hajiya sai dai a ji kiranta tace aje a jirata a filin jirgi ƙarfe kaza zata sauka. Ni ina zaton ma yau zata dawo." Nace to shike nan,na haƙura zan jira.Yace Kama gefen kumatuna yace, "Daga cikin abinda ke ƙarawa mace daraja a idon miji shine rashin gardama." Na ɗora tafin hannu akan nasa nace Insha Allahu zan riƙe wannan karatun. Ya sunbaci goshina kin haddace wannan Baby." Nace To ina godiya Malam.

Yana fita na tafi ɗakin shi domin ci gaba da karatun littafin nan

Babi na gaba na shiga. Wanda ya ke magana akan Hajiya Zeena Amadu Shinkafi.

Hajiya Gwamma ta sa anje har Shinkafi ta jihar Zamfara an yo mata bincike akan Zeena. Tamkar dai shi Ali Baita
Itace 'ya ɗaya tak da Ubangiji ya baiwa maihaifinta kuma ya bata ilimin zamani dana addini. Sai dai kullum yana cikin damuwar rashin samun ɗa namiji wanda zai hutar da shi in ya kai matakin wasu shekaru. Zeena ta fuskanci damuwar da mahaifinta ke ciki don haka sai ta sawa zuciyar ta cewa zata share masa wannan kuka. Ta kuma nuna masa a zahiri ta karanci fanin kasuwanci. Dan haka data ƙare taci gaba da jagorantar wani ɓangare na kasuwanci sa.

Abinda ya ba ni mamaki shine daga daidai nan gurin sai aka sa wani abu mai kama da farin fenti aka goge rubutun aka ɓata shi har zuwa Babi na uku wanda yake magana akan cewa an Ɗaura Aure Zeena da Ali Baita kuma an kawo ta garin Kano. Me aka rufe a can? Na tambayi kaina baya na buɗe shafu kan na koma baya na duba,hakan dai suke ba ido na bane. Dole za a samu kwafi mai kyau a gidan nan koda babu a ko ina za a same shi a gurin Hajiya.

Na buɗe shafukan gaba duk dai bayani ne akan dukiyar da ya mallaka da tallafi da yake bayarwa sai hotunan karramawar da ya yi ta samu daga ƙungiyoyi da jam'i o'i sai hotunan su Shamaki da yayinsa an rubuta 'ya'yan Ali Baita. Na kasa ci gaba da karanta wannan littafin ina bukatar mai kyan. Na maida shi na aje.

Ilai kuwa a ranar sai ga kiran Hajiyan Shamaki a waya, yace min a sanar da direba yaje filin jirgi ya jira Hajiya suna Lagos.

Nace to na fita da kaina na faɗa masa.
Na kira wayar Juma kwanan ta biyu taje gida. Nace Hajiya na hanya ta dawo domin ita ce tasan wanne irin girke girken da za a yi domin tarbar Hajiya.

Cikin rawar jiki sai ga Juma ta dawo,tace don Allah in Hajiya ta dawo karki in ce mata taje cikin gari saboda zata yi faɗa, tace min kar inje tunda bata nan. " Nace ba komai karki damu bazata sani ba..Ni dai burina ki shirya mata abinci wanda ki ka san tafi so zata yi marmari. Ni kuma zan shiga ɗakinta da kaina in gyarra mata shi, amma ina son ki Kunno turaren da ya fi yi mata daɗi ki biɗe gidan da shi lungu da saƙo.

Cikin mamaki tace 'Yannan ke ta daban ce sauran in Hajiya taje wani guri zata dawo sun dinga takaici kenan wai takura zata dawo. "
Nace Ni kam ina farin ciki da dawowar Hajiya wallahi Baba Juma ina son Hajiya har cikin zuciya ta, kin san dalili? Tace "A'a. Nace ta haifa min Shamaki wanda nake masa wani irin so mara misaltawa. Kullum ina mata addu'a Allah ya sa ta gama da duniya lafiya tare da mu gaba ɗaya. Juma ta saki baki tana kallo na, nace yaya dai Baba Juma? tace, 'yannan ashe Kema kikan taɓa rashin kunya ashe. Na yi dariya wuce na nufi ɗakin Hajiya. Ta biyo ni har ɗakin tace "To zan baki wata shawara, komai nata ki barshi a inda yake karni canza masa guri." Nace Juma zan gyara ɗakin nan kamar yadda zan gyara ɗakin mahaifiya ta ne zan iya canza komai zuwa inda ya dace. Tace To shikenan. Na canza zanin gado da labulaye. Na wanke banɗaki na share na goge komai na kuma canza mata shirin wasu abubuwan. Na duba durowoyin ta ina neman kwafin littafin nan ban samu ba, zan fita sai na kula da wata durowar ta ƙarfe ina ganin irinta a finafinai. Wandda ake buɗe ta da lambobin. Nace tabbas ya na cikin nan,in kuwa haka ne to abin yafi ƙarfina.

Nafita nace Juma ta saka turare a cikin ɗakin.

Shamaki dama ya tashi da azumin sitta shawwal sakamakon matsa masa da nayi akan ya fara kawai, kuma fa nayi haka ne saboda na duba wayar shi naga alƙawuran haduwa da wata da suka yi da zarar anyi salla da kwanaki kaɗan. Na yi ta mamaki,nace anyi ibada kuma daga yin salla za a bi ibadar da zunubi.

Yace "Wai me yasa na damu ya yi azumi ana cikin bikin salla. " Nace saboda ka saba da azumin kafin cikin ka ya buɗe kayi kayan ka in yaja Lokaci ƙila ya yi masa wuya.

Yace Gaskiyar ki kam domin bara haka ce ta faru, ina ta furta zanyi amma ban samu na yi ba." Ni na tashe shi ya ɗauka.
Hajiya ta iso gida lafiya muka tare ta da murna da farin ciki Ni da yaran. Ta ji daɗin yadda ta samu gidan muka bita har cikin ɗaki, ta yi turus ta dubi Juma mai riƙe da jakar Hajiya. Tace "Wanene da wannan aikin ko maman Umar ta zo ne?" Juma ta kalle ni, tace 'A'a ɗiyar ki ce dai ta yi gyaran. Hajiya ta kalle ni, sannan ta zauna baki gado. Muka fita domin ta kimtsa. Ina falo ta fito ta yi wanka ta shirya tsaf cikin doguwar riga. Sai lokacin na buɗe mata kujerar zaman ta wadda na saka wani farin kyalle na rufe, ko masu shara sai dai su kakkaɓe su share su mayar su rufe. Ta zauna tace Alhamdulillahi Allah mun gode maka, ya Allah ka amshi ibadarmu.

Muka ce ameen. Sai da ta yi salla sannan Juma ta soma gabatar mata da abinci. Na zauna ina zuba mata. Tace Juma sannu da ƙoƙarin wannan hidima. Juma tace matar Shamaki za a yi wa godiya ita ce ta bada umarni a yi komai.

Hajiya ta ɗaga kai ba tare da ta dube ni ba.
Shamaki ya shigo, cikin murna yana yi wa Hajiya sannu da zuwa. Ya zauna suka gaisa. Ta gama cin abinci na soma matsa mata ƙafa, tace a ɗakko maganin nan domin ƙafafun sunyi tsami.
Na je na ɗakko lokacin da na dawo na samu Azima ta na zaune a gaban Hajiya. Hajiyar tana cewa Azima. "Kina nufin baki ji ba duk wannan hayaniyar kusan awa biyu da suka wuce? Tace "Wallahi ni dai banji ba." Hajiya tace shike nan. Na zauna na ci gaba da matsa mata ƙafa.
Chapter 7 · 0% Book details