← Book details Hamshaƙiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 31

Sashe 31

Hamshaƙiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Lallai fushi ba nawa bane. Na dake nace ka fadawa Azima domin ita zaka yi wa kishiya ba ni ba. Yace "In fada mata itace zata biya min sadaki? Nace Hakkinta ne ta sani,
yanzu sauran kwana nawa daurin auren? Yace ba a tsaida ba ni dai ina so da wurine sabosa gaskiya a takure nake. Nace Ta kura kamar yaya baga baga Azima ba. Yaja tsaki tare da fadin bana gane mata gaskiya ke kinsani ke kadai ce me maganin matsalata, kin bani mamaki dan kin haihu kike gudu Baby bayan nasan kin warke, banda kullum sai na roki Allah ya yafe miki da yanzu ki na cikin tsinuwar mala'iku."
Nace na gode da ka yafe min.
Yace yauma hakura zanyi kenan? Nace kasan Allah tsoro nake kar in kuma samun ciki domin har al 'adata ta dawo. Yace ki samu mana ke zaki sai min ragon suna? Nace jikina wahalar da zan sha ga baby.
Yaga dai da alamun bazan yarda ba. sai naga ya tashi ya shiga ciki. Jim kadan ya fito sanye da kananan kaya yaki kyau kamar wani matashin saurayi. Ya dauki wayoyi da makullin mota yace " Mu kwana lafiya. Nace bangane ba, har zai yi magana sai kuma ya fasa ya fita. Na tashi da sauri na bishi ya nufi mota. Na dawo na goya Junior na dauki makullin mota ta na dauki wayata da mayafi na fito har ya harba motarsa a gate na nufi tawa na dauka nima na bi bayanshi. Na kalli agogon shadaya na dare. Ina ta binsa na dan bada tazara kar ya ganni har muka isa wani Katafaren gini wanda na tabbata Hotel kafin in karasa ya shige, nima ina zuwa na amshi number na shige. Naje mota ta kusa da tashi. Ina zuwa Reaseption nace akwai wanda na zo gunsa Aliyu yanzu a shigo. Sai naga sun kalli juna. Suka ce ya sunana na fada musu suka rubuta suka ce bari a kira shi a waya. Jim kadan wani ya ce bari ya rakani. Muna kwankwasa kofar ya bude sai ya zaro ido alamun mamaki, yace me ki ka zo yi? Na zata Ashanti ce wadda mukayi waya zata zo ta same ni wai ya ki ke son in ne Baby kin tauye min halas na taho neman haram shime kun biyo n. Nace wacece Ashanti? Yace ki shigo mana. Me ya sa kika fito da wannan daren? Kin zo kin bata min shirina." Hawayen da bansan ko na menene ba suka soma zubowa. Na kwance ya ro na shinfide shi a kan kujera na soma cire kayan jikina ina jifa da su, na cire tas na nufi gadon na kwanta. Yazo ya zauna duk ya gigice. Gaskiya na dauki alhakin Shamaki domin har kuka ya min akan kar in kara yi masa irin wannan horon. Amma fa nima na gayawa yan garinmu. Yarona kuma sai Allah ya dora masa bacci.
sai da Asbashi bacci ya dauke ni. Bai tashe ni ba, cikin bacci na ji ana shamin Mama ashe wai Junior ne ya tashi shine ya zo yana bashi nono. Na tashi da sauri nace banyi wanka ba ba a ba yaro nono jiki da najasa. Yace ban sani ba. Nashiga wanka na fito nayi salla sannan na dauke shi. yace "Baby inje in dakko mana kaya mu dan kwana biyu a nan? Nace kasuwar fa? Yace Hutu zan bata. Nace yarana fa? Yace me zai cinye su? Ga Rahin ga su Juma. Nace to Azima kuma fa ai zamu shiga girkinta. Yace "Kai! Wannan Azima tana takura min fa, Allah ni na kalle shi. sai ya ce "Tom shike nan mu kara kwana daya shike nan? Bani da mafita dole na ce to amma in kaje gidan ka hadani da Juma zanyi mata magana. Yace "Ba damuwa duk yadda ki ka ce haka za ayi." Nace ka fada min kuma wace ce Ashanti? Yace ga ki nan ai nasan zaki biyo ni dama ba wata Ashanti kawai wayo na yi miki." Na yi Murmushi har na ji dadi. Da mota ta ya tafi. Nace kai namiji ma dai sai abarshi. Yana shiga Juma ta tare shi Uban daki na lafiya Ina 'yarnan ta shige ne na juye ruwan zafi bata ba dalilinta dan ma baya nan. Yace gata a waya za ku yi magana. Muka gaisa tace ga ruwan zafi an juye. Nace nayi wata yar tafiya sai gobe zan dawo, ayi komai yadda ya kamata sannan a kula min da yaran nan a lallashe su musamman Anisa yar Mommy na san sai ta yi rigima. Abinda babu a tambayi Azima zan kira ta a waya. Tace to ba komai amma dai lafiya ko? Nace lafiya lau tace to acan za kiyi wankan kinsan haihuwar fari sai an kula.Ya amshi wayar yana fadin Juma wane kuma wanka ai ta gama wanka. Juma ta bishi da kallo baki bude tana fadin ikon Allah Uban daki Haihuwar farice fa lokacin mu arba'in biyu ake yi. Ya shige dakina yana fadin dama Juma ta zigaki ko? Ina dariya nace ba ruwan Baba Juma. Na fada masa duk abinda nake bukata ya dakko min shima ya dakko nashi ya shiga gurin Azima ya fada mata zai yi tafiya. Sanan ya sa Bala direba ya kai shi sai ya bar motata a gida. Haka muka yi gayu cikin kaya masu kyau da yaronmu muka sauka gurin cin abinci na Hotel din muka ci sannan yace mufita. Ni ke tuki shi kuma yana rike da yaro muka yita yawo guraren shakatawa sannanmu kaje gurin cin abincin mutanen kasar Labanon. Sannan mukayi siyayya muka dawo Hotel Muka yi salla muka sha Soyayya muka sake fita. Shamaki yana ta kokarin nuna min irin son daya ke min kuma yana lallashi na da in yarda mu fita kasahen ketare acan ne akwai guraren shakatawa. Nace Zamu fita ka bari sai na yaye wannan yaron don mu barshi a gida. Yace dashi zamuje ke dai ki yarda kawai. Nace mu tafi har Azima da kuma yaranmu. Yace an fasa. Haka dai rayuwa ta ci gaba. Hajiya Zaliha tana ta turo masa yarta. Na gaji nace muje a ne mi auren nan dai ko na huta ni suke ta zagi wai na hana.Yace Baby ke kin sani ke kadai nake so dubi Azima hakuri ta ke yi dadi, dan Allah kada ki kawo maganar wata, nacc barta ta shigo. Rana daya na kwashi yara da shi muka je gidan Hajiya Zalihar. Ta shiga zare ido muka gaisa nace zance muka rako Dady taje yana jiran ta awaje.Mamaki ya kama Hajiya Zaliha da kunya. Na'ima ta fita gunsa muka ta shi muka yi mata sllama muka fita. A mota suke nace ku fito ku bamu guri ko? Suka fito na dura ya'yana muka shige amma kishi hankalina yana gurin su. Na fito nace hirar ta isa haka zo muje na kalle ta nace sai anjima, Shima yace mata sai anjima na tura shi mazaunin direba nace kai zaka tuka yanzu. Ta saki baki tana kallonmu Ni dai tun daga wannan zanca ban sake jin maganar ba. Na san dai na sha tsinuwa.
Su Umma suka tare a gidansu ya keru, na canzawa su Jamila makaranta. Gashi su Umma suna cikin jerin masu zuwa aikin Hajji bana har sun yi passport komai abin shi a wa.

Sai da nayi addu a sannan na dauki tsinken gwajin na shiga bandaki bayan nayi fitsari ciki roba sai na tsoma. Take ya gwada min cewa ina da ciki. Na fashe da kuka sai na fita da gudu zuwa dakin Shamaki. Ya baje yana kallo kwallo, naje fa masa tsiken ina fadin shike nan ka yi min ciki ga jaririn yaro ka huta. Ya tashi da sauri ya rungume ni wai da gaske?Allah na gode maka sai muje gurin likita ya bamu shawara yadda zamu kula da Junior da kuma cikinmu. Na gama mana komai ranar talata jirginmu zai tashi zamuje Istanbul daga can kasashe goma zamuje. Na bude baki zan yi magana ya sa yatsa ya rufe min tare da fadin mun gama magana da Azima ta yarda. Yara zasu koma gidan Maman Umar har mudawo.

Alhamdulillah!
*ALHMDLLH, ALHMDLLH Allah Nagode maka daka bani ikon kammala littafin nan lafiya, Allah ka yafe min kurakuran dake ciki, Allah ka bamu ikon amfani da darussan dake ciki.*

*Masoya makaranta littafin HAMSHAKIYAR UWA Nagode da haƙurin bibiyar labarin da kuka yi, waɗanda na ɓatawa a cikin ku ina roƙon su yafe min,ɗan Adam ajizine amma banida nufin ɓatawa kowa*

*Game da jinkirin posting da aka rinƙa samu kuyi min uzuri saboda wannan shine littafi na na farko a online, amma insha Allah next littafi idan zan ƙara yi bazan fara posting ba sai na gama rubuta shi. Nagode Nagode🤝😍🥰*
.
Chapter 31 · 0% Book details