Sashe 24
Hamshaƙiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tace "Gaskiya nifa bazan tafi yau ko gobe da ka ke magana ba. Ya aje jakar da ya gama hadawa sannan ya zauna tare da daukar wayar sa yana kara danna kiran Hajiya da Baby. Kamar kullum dai layuka a rufe. Sakna ta maimaita cewa ita fa ba yau zata tafi ba. Yace kina iya zamanki mana, bani da matsala akan haka. Tace zaka biya min kudin Hotel din kenan da abinda zan ci abinci da wanda zan kashe? " Yace akan wane dalili kenan zan yi hakan? Tace akan dalilin cewar kaine ka kawo ni." Yace ni dana kawo ki maidaki kawai zan iya yi amma ba wai in dauki nauyinki ki zauna kici gaba da karuwanci a nan ba. Ta fusata, nice karuwa? Ya dago a fusace to fada min sunanki matar aure? Ta lumshe ido cikin ta kaici sannan tace na gode ba laifinka bane. Shamaki ya yi tsaki ya tashi ya fice daga dakin.
Hajiya ta juya ta kalli likitan tace zaka iya lafiya, sannan maganin da nake sha ya kare, yana taimaka min gurin rage radadin da jikina ke yi. Dr yace Hajiya kiyi hakuri maganin ba zai ci gaba da amfani a jikin ki ba, mana ana ko kinsha nazai yi amfani ba saboda matakin da kika shiga. Amma akwai abu daya, zan zo da wani magani zamu sa shi a ruwa sai mu jona miki, anyi gwajin maganin a jikin wani balarabe kuma ya samu sassauci. Hajiya ta daga kai kawai. Sai lokacin na lura da wata rama da baki wanda Hajiya ta yi. Tafiyar da take yi a hankali nake kallon kasaita ce ashe karfin haline. Tana zama kusa da ni sai na fashe da kukan da nake kunshewa. Na dora kaina a kafadarta ina fadin Hajiya da gaske ne wai baki da lafiya? Ni fa banyar da ba, suna karya ne, Allah shine kadai yasan ranar mutuwar ki kawai ki tashi mu koma gida. Insha Allahu bazaki mutu yanzu ba. Na sauka na soma hada kayan mu ina fadin ki daina sauraron su. Na sauke akwatuna ina kuka ga hawaye ga majina. Hajiya tana ta kallona cikin yanayin da bazan iya fassarawa ba. Na zo na kama hannunta tashi Hajiya mu tafi gidanmu. Hajiya ta janyo ni tare da fadin zo nan Rabi'atu. Ta zaunar da ni kusa da ita, ta kama gefen mayafinta ta share min hawaye, tace yi hakuri ki yi shiru za muyi magana ne
Na dora kaina a kafadar Hajiya ina ajiyar zuciya tana shafa bayana tana fada min cewa "Kiyi hakuri muyi magana, na zo da ke nan ne domin mu tattuna abinda ya kamata, ina son ki sani ba karya likitocin nan suke yi ba, ilmin ne Allah ya basu, ciwona na Cancer ya bayana ne tun a ranar da na haifi Shamaki. Babu wanda ya sani daga ni sai mahaifinsa, Kafin rasuwar mahaifinsa ya tada hankalinsa sosai saboda likitocin su fada mass cewa canser a bakin mahaifata yake, za a iya yanke ta, sai muka amince aka yi aiki aka yanke kamar na samu lafiya lokacin Shamaki yana guje gujenshi ya fara wayo sai ciwo ya dawo. Lokacin da likita ya fadawa mahaifin Shamaki cewa Cancer nan ce ashe ta yadu a wasu sassan jikina hankalisa ya tashi kuma ya gama likitan ya fada min, ya dage gurin nema min magana. Na gargajiya daba bature. Na samu sauki ba tare da nasan meke damunka ba. Har zuwa lokacin da Allah ya yi wa mai gidanta rasuwa bani da masaniyar ciwona. Soyayyar Mahaifinsa na tara ta a kansa, munyi wata irin shakuwa wadda ta sa har 'tan uwansa suke min mita akan nafi sonshi. Gado daya muke kwana har sai da yakai matakin balaga sannan na yakice shi. Dakyar ya fita waje karatu lokacin da ya kai matakin Jami'a, bai zauna ba sai da na bar komai naje muka kama gida na zauna da shi tsawon wata uku.....
.....
, Hajiya ta ci gaba da fadin. "Bayan ya gama karatu 'yan uwanshi duk sun kama dakunan su, nice nake kula da kasuwancin dukiyar Shamaki da kuma tawa. Allah cikin ikonsa ya gama karatunsa yazo ya kama kasuwaci. Iyaka biyayya Shamaki yana min, addu'a ta kullum a gareshi ita ce, ta samun mace mai hankali wadda zata kula da rayuwar shi bayan mutuwa ta.
Shekaru biyar da suka gabata ciwona ya sake tashi ya tsananta lokacin ne
aka fita da ni aka kawo ni nan kasar. Likitan ya gano cewa Cancer ta riga ta cini, Kafin ya yi magana da su Shamaki nace masa nasan ina da ciwon Cancer ina rokonsa don girman Allah kar ya fadawa duk wani ahalina zasu rayu a bikin damuwa kafin in mutu, ko menene ina son muna magana da shi cikin sirri. Yace min nan da shekaru biyar zan iya mutuwa na yi tsawon rai in shekara biyar zuwa watan uku kamar dai irin wannan watan.
Ina matukar kaunar yarana ina tausayin su, ina soyayyarsu irin wadda Allah ya dora min kamar yadda ya dorawa ko wace uwa akan yaranta. Na kan shiga daki inyi kuka sosai domin nasan mutuwace take tinkaroni kuma zata rabani da su, dan haka sai na damu da lamarin Shamaki, wanda zai tattara dukkan soyayyarsa ga matarsa gashi bai iya kai matsalarshi ga wani abokin shi bare 'yan'uwan shi komai nice abokiyar shawarar shi. Ko zai iya samu wadda zata tallafe shi ta yi hakuri da shi a duk yadda ta same shi? Farko ni ce na bashi dama ya memo wadda yake so, suka hadu da Maman Meema a bikin abokin shi Shamsu. Na samu kaso shidda a cikin goma lokacin dana sa a gabatar da bincike akan yarinyar, na hakura ya aureta aka soma zama, amma sai na yi kokarin gwada halayenta ta hanyar gwaji. Sai na gano cewa ba itace matar da ta dace da shi ba, bata da rufin asiri ko kada, ga son kanta kuma bata shiri da 'yan uwansa, bugu da kari ga ta sai ta dauki wayar sa ta yi transfer na kudi masu yawa daga bankinsa zuwa nata, kuma tace ba ita bace. Dan haka na sa shi ya bata takardarta ya kuma bata ba tare da ya nemi jin daliliba. Kasancewar bamu da ishasshen lokaci saboda kwanakin mutuwata kara kusantowa ya ke yi. Sai na saka Kawata Hajiya Zaliha ta memo masa mata, ta so ta bashi 'yarta, amma sai na nuna mata ta hakura bana son yara su shiga tsakanin zununcinmu, na fada mata haka ne domin bazan iya kara akan Shamaki ba. Dan lokacin da ya rage min ina son in nuna masa duk wata soyayya ta. Dole ta hakura ba domin ta so ba. Maman mubina. Ita kuma banda kokarin azurta kanta da danginta bata komai, duk lokacin da nayi mata gwaji akan wani abu kamar sadaka ko zakka ba ruwanta da dangin Shamaki kanta ta sani. Gashi bata san girma ko darajar kowa ba. Tana son ta yi mulki har da ni. Abinda yafi daga min hankali shine yadda ta ke tauye masa hakkin sa na kwanciya wanda hakan ne sanadin nitsawar. shi a neman mata.
Shima na sa ya rabu da ita. Kuma bai tambayi daliliba Na ci gaba da yi masa addu'a Cikin haka ya samo Maman Anisa yana sonta itama tana son shi amma sai tana kula tsofafin samarinta, har ta taba ziyartar gidan wani saurayinta wanda bani da sheda akan abinda ya faru, sannan tana waya da maza daban daban. Har zuwa yau batasan na sani ba, haka kuma Shamaki bai sanI ba domin ban fada mishi ba kar ya fara zargin ko ma 'yarsu ba tashi bace.
Ya jinjina kuma ya girgiza lokacin da na ce masa ya sake ta. Dan yana sonta, tsabar ladabi da biyayya har zuwa yau bai taba tambaya ta me ye dalilin sa shi ya saki matansa ba.
Abinda ya yi Imani shine bazan taba cutar da shiba. Gashi zan mutu bansan takamaiman gurin wa zan bar shi ba. Muryarta ta sarke hawaye suna kwaranya a kan kumatun ta, na sa hannu ina share mata hawayen, ga nawa suna kwaranya.
Na kama hannunta. Nace Hajiya ki barshi a hannun Allah ki barshi a hannu na. Ta saka hannunta ta damke nawa ta ci gaba da fadin Na yanke shawarar in bashi Azima wadda ta zama raino na ce, kuma sai ina kallon zatabi duk wani tsari nawa, sai Allah ya nuna min ban iya ba, wayo da dabarata, ba su isa su sani in samu biya bukata ta ba.