← Book details Hamshaƙiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 31

Sashe 18

Hamshaƙiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ban fito ba sai da nayi wanka na saka riga da siket na atamfa na daura dankwali na zubo da gashin kaina a kafada. Ina zuwa sai na samu tana zuba musu abinci. Kamar in juya amma sai na fasa, na shiga na ce sannunku. Duk suka amsa har Azima, sai na kasa zama na nufi kicin duk da cewa babu abinda zan dauka a can din. Juma tana goge goge tace "Uwar dakina wani abin ki ke so? " Nace yau bana jin cin abinci, me zan samu ne mai dan romo? Tace da akwai kayan ciki a freezer ko a dumama ne, kuma naga da kina ta zakwadin cin farar shinkafar nan" . Nace ji nayi kuma duk ta fice min a zuciyata.
Ta dakko ta zuba nace ta barshi haka, tace shima dai ki ce "Dantabawa zaki yi ne kenan? , Ta matso wai kuma me yarinyar nan ta zo yi?" Nace wa fa? Tace Azima mana. " Nace ita da gidansu. Baba Juma tace "Ko gidansu ne ba an aurar da ita ba, ki bi a hankali dai yarinyar nan tana da makirci, nifa ba a banza ki ka ga ina shakkar ta ba, ta iya hada zance taje ta fadawa Hajiya abinda ba a yi ba. Hajiya ta hau kai ta zauna daram. Sai dai in anyi a gabanta. Nace Allah ya kyauta amma ni ban dauki wannan a bakin komai ba, domin ta yi min kadan a kishiya. Juma tace "Na raba ki da wannan tunanin ba karami a kishi zage damtse ki karbi mijinki dan hakin da ka raina shi ke tsole maka ido, amma fa kar ki tsorata, ki fiddo da wannan wayon naki ki yi amfani da shi a matsayin ki na uwargida ki rike kambun ki gam.
Nace ina godiya Baba Juma zan kula. Na fito da kayan ciki a plate, suka bini da kallo, su duka ukun har kaman in tambaya ko lafiya? Amma sai na share na zauna a gurin da nafi zama a kan kafet. Sam ba dadin abinda nake ci nake ji ba, amma bani da yadda zanyi domin bana son su gane halin da nake ciki.
Na maida kaina ga kallo TV amma inzaka yankani bansan me ake fada ba. Hankali na yana kan su, duk sun yi tsit, sai ma na ji zuciyata ta zargi ko dai yi da ni suke yi da nazo suka yi shiru sai karan cokulan abincin su, ita ma Azima sai cin nata take yi.
Na gama Juma ta zo tana tattara kwanuka. Na ce Hajiya zan shafa maki magani da wuri yau domin ina son inyi bacci da wuri. Shamaki ya kalle ni, yau dai kinsan a nan nake." Na kalle shi, har yanzu haushi yake bani, nace Au gashi ban gyara maka dakin ba." Na kalli Azima nace ko zaki gyara masa? Da sauri ta ce" To" Zata mike Hajiya tace "Jimana. " Ta kalli Azima zauna mana." Azima ta kalle Shamaki. Ya ce baki ji me tace ba? " Ta zauna nikam share su na yi, dama latsawa nayi domin da sun barta taje bansan wane irin hali zan samu kaina ba. Hajiya da Shamaki suka kama lissafin kasuwanci su. Na shafawa Hajiya magani sannan nayi musu sallama.

Ina shiga dakin na tsaya ina kallon ta yadda zan fara, domin tun ranar da ya bar gidan ban shiga dakin ba shi kuma yana shiga in ya zo duk ya birkita ko ina. Na gama kwashe kayan wanki na gyara durowa, sannan na koma gado na canza zanin na kunna borna ta turaren wuta. Na fito falo da nufin in tafi daki na, turus na yi ganin su zaune shi da ita a falon....
.....
Wani takaici ya zomin iya wuya, narasa me ya kamata in yi. Na tako ta gabansu zan wuce, yace "Baby zo." Yi nayi kamar banji me yake fadi ba, na wuce har na kai bakin kofa ya taso da sauri, wai ina magana kina jina Baby? " Na kalle shi, nace me zanyi kuma bayan na gama gyara muku gadon.? Yace "Kina da matsala ni ba maganar gyaran gado bace, zanyi magana da ku ne ke da ita, ya kama hannuna muje ki zauna." Ma bishi fuska daure cikan fushi da tsananin kishi. Ya zauna a mazaunin shi da ya taso, ya zaunar da ni kusa da shi,. ta dube ni, ta taba baki. Sai na gyara zama a kusa da shi din, ita dama ta zauna ne akan
Kujerar da ta ke daf da tashi. Ya kalle "Dan jawabi zanyi muku ba mai yawa ba,
Ya kalli Azima yace "Azima da ke zan fara magana, ina son ki sa hankalin ki ki kuma san wacece Baby a gurin ki bana son fitina ki rike ta kamar yayarki., ina nufin ki yi mata biyayya. Ya dube ni, ke kuma hakuri zan baki, ina mai kuma baki hakuri a karo na ba adadi. Nasan cewa ba sai na fada miki cewa ki zaune lafiya da ita ba domin nasan zakiyi haka, Allah ya hada kanku a zauna lafiya. "
Duk da ina jin haushin sa naji dadin jawabin na shi sosai. Har na rage jin haushin sa. Ya sake kallonta "Ki tashi kije ki kwanta kuma in har ki ka sake na ganki online cikin dare ranki zai baci." Ta mike ta nufi hanyar Bedroom, yace "Ina za kije? Kina da gurin kwana anan ne? " Tace Ina zanje to? Yace dakin ki na da mana. " Ta zaro ido ka san haka ne ya baka barni na kwana a gidana ba ka ce sai na biyo ka! Yace "Dan iska ne ni da zan barki ke daya a gidan kimin jaye jaye." Na zaro ido don mamaki ina kallon shi na kalle ta ta turo baki ta fice.

Na kalle shi, kasan ma a'nar abinda ka fada kuwa? Yace na sani mana inhar kin fahimta to nufiana ke nan." Nace Kana zarginta fa kenan.Kuma in har haka ne to ka tafka kuskure, domin an hana zargi a cikin aure. Yace "Ai ba wai maganar zargi bane, zata iya janyo min wani kato gida. " Nace Ta taba kawo wani ne a tsawon kwanakin nan bakwai da ku ka yi? Yace bata kawo kowa ba amma bazan samu kwanciyar hankali ba zan fadawa Hajiya cewa ta bamu Tabawa ko Juma domin a saka mata ido, kin san Allah bana iya fita da wuri, in na fita din ma Allah-Allah nake in koma, sai ina ji a zuciya ta kamar zan samu wani a gidan tunda ita dai ballagaza ce." Yanzu na sake fahimtar cewaLallai kuskure ne babba ki yarda namiji ya rike koda hannun ki kafin aure domin zai tafi yana zargin ki cewa kowa ya zo zaki iya ba shi hannunki ya rike.Ya katse min tunani da fadin. "Menene ki ka yi shiru abinda na fada har zuciyata na fada miki.

" Nace Amma dai Babban bako tsakani da Allah kai ka yaudareta kuka yi ta sharafin ku kai da ita, yanzu kuma sai ka ke zarginta? Yace ta yaya bazan zarge ta ba, kaddara ni nazo nace mata ina son muna fita sai kawai ta yarda mu fita? Ta yaya zuciya ta zata nutsu dan na aureta, da aurena sai wani ya ganta ya taya ta sallama mishi. In kece zaki bini Ko fuskar da zan taba yatsanki ban gani ba lokacin da nake zuwa gurin ki. " Nace to ai ita yarinya ce karama kuma banda haka tana sonka zata so ta faranta maka rai. Yace "To kema ai kina sona sai dai ki kirani ka tambaya ta da gaske zaka aure ni? Ina jin kamar zan mutu in ka fasa aure na." Ya yi maganar cikin kwaikwayon muryata da tsokana. Na dan kai masa dukan wasa ma ina fadin its dai yaudararta kayi. Yace "Ke Lauyar ta ce shike nan amma dai har abada bazan iya bata amana ba tunda taci amanar kanta ma."
Nace itama ai haka taza kalleka a yadda ka ke kallon ta. Ya kamani ya mike tsaye don Allah ki bar maganar ta muje ki biya basukan da ke kanki kema din.
Abin mamaki Shamaki kamar wanda ya dawo daga tafiya, sai kace ba daga gidan amarya ya dawo ba.

Da safe kamar yadda muka saba haka komai ya tafi normal.

Na kuma gane Azima bata da wata martaba a gurin shi dan haka sai na sauke duk wani fushina na rungume mijina. Haka kuma wannan mummunar dabi a ta bibiyar wayar sa na nake yi ban fasa ba, haka kuma ban daina ganin takaici ba, domin har yanzu da neman matan sa.
Zuwa yanzu kuma na gama koyon duk nau'in na girkin da Hajiya ta ke so. Na kuma karbe girkinata a hannun Juma, har nama na fahimci tafi jin dadin nawa, tunda ga su Juma za ta kirani tace in sada mata abu kaza.
Yaran gidan nayi nasarar janyo su zuwa jikina, ta hanyar yin ruwa da tsaki ga bukatun su tare da jure amsar korafinsu da kuma yin sulhu tsakanin su, har ya zama in sun kai wa Hajiya kara zata ce ku tafin gurin Mommy ku.
Chapter 18 · 0% Book details