← Book details Gurbin Ido Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 113

Sashe 98

Gurbin Ido Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yanzun ai ni nake tanbayarka bawai su ba,me tayi maka,ka gayamin ko mene ne,sai asan yadda zq'a gyara abun" kai ya girgiza

"Abbi.....banajin zai gyaru"

"Meye wanda bazai gyaru ba?" A nutse ya gaya masa dukka wani abu daya taba sani a baya akan unaisan,da kuma abinda ya farun yanzu da binciken da yayi da hujjojin da ya samu.

Sosai abbin ya kadu,don bai taba kawowa yarinyar haka ba,duk yadda suke takatsantsan wajen samawa 'ya'yansu maza da mata abokan rayuwa na gari,amma duk da hakan bai nunawa ja'afar din ba sai yace

"Ka barni da kaina zan sake bincike"

"To abbi" ya fada hankalinsa a kwance,tunda dai ya sani,koda abbin din zaiyi binciken zai binciko kwatankwacin abinda shi ya samu ne koma wanda ya fishi.

Zuciyarsa ce ta dinga raya masa ya yiwa abbi zancan maimunatu,sai kuma yaga bazai iya ba,don haka ya share batun,yasan dai akwai lokacin daya dibama koma meye anni ta shirya.

Sassan amma suka wuce shida abbin din gaba daya,saboda yace yunwa yakeji,yau da wuri zaici abincin darensa,baya wasa da girkin amman,saboda yadda ta qware sosai wajen sarrafa abinci,tarin masu aiki ko sarauta ko arziqin da take dashi baisa ta sako abincin mijinta ba hannun yara ko masu aiki,har yau har kwanan gobe ita keyi,saidai a tayata.

Amma na shirya musu abinci suna fira sama sama,bayan ta gama itama sai ta samu kanta da zama a cikinsu,abinda ba kasafai takeyinsa ba,duk da ita bacin abincin take ba,tana ta dai serving dinsu ne,daga baya saiga hisham ya shigo shima yayi joining dinsu, khadim ma sai gashi,da yake sau tari sai ya baro abincin ammi ya taho wajen amma ci,duk da itama ammin gwana ce,amma shi dan dakin amma ne.

Bai waiwayi sassan anni ba sai da ya dawo daga sallar isha'i ya kusa wucewa gida,tasan ya shigo gidan sarai,kuma batayi mamakin rashin shigowarsa ba,sanda ya shiga tana zaune a falo tana shan damammiyar fura data sha sugar,don annin ba daga nan ba wajen shan zaqi,kanta ta daga ta dubeshi sannan ta tabe baki ta maida kanta ga abinda takeyi,ya samu hannun kujera ya zauna yana gaidata,a yatsine ta amsa masa,yadan zubawa tv ido sannan ya miqe

"Wannan sugar din da kike yawan sha fa yana yawa,shekarunki sun ja" dama jiransa take,saboda haushin qin shigo matan da baiyi ba,saboda ta saba anan yake sauka ko yaushe bayan ya gama gaisawa da kowa

"Kai arcannnn.......kayi ta kanka malami,mu jikinmu ba irin naku bane, sugar abin banza ba abinda zaiyi mana,haka zamu mutu ras da lafiyarmu in sha Allah,damu da mazanmu ba irinku bane,wanda sai mace ta shekare a gidansu su kasa yi mata ciki sabodq tsabar raggwanta" dole ya dora idanunsa akan fuskar anni,tirqashi😂, abun yazo harda gori?,ya tabbatar dashi take,shi takema gorin baima maimunatu ciki ba,don yasan itace tata,da ita ta damu.

Murmushin gefan baki ya saki yana cusa hannuwansa a aljihun wandonsa,shima bari yayi mata ta 'yan zamani

"Me kike ci na baka na zuba anni?,ba tsallaken shekara daya bane?,to itama za'a ciketa,ki rubuta ki ajjiye biyu xa'a baki ko uku,nex year mu sake maimaitawa" daga haka ya juya yana ficewa daga falon,sai ta bishi da kallo,tana jin sanyi qasan ranta tare da cewa

"Ameen ya hayyu ya qayyumu,'yan ameen su amsa ya rahman" can qasan ranta,amma a fili sai tace

"Ahhh waima,zamu gani".

Yana mota yana tuna matter dinsu da anni,sai kawai ya samu kansa da sakin murmushi,tare da imagining diyoyi daga wajen maimunatu,wanne irin kyau zasuyi?.

Duk guje gujensa yau dinma sai da yasha baqar wahala kafin ya samu bacci ya daukeshi
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 76

A hankali ta rufe bangon littafin dake gabanta gami da sauke ajiyar zuciya,zuciyarta na wani irin karyewa da kuma samun rauni,a hankali ta zubawa wajen da afra suke zaune suna hira kallo,tun dazun suka ce mata ta bar karatun tazo tayi joining dinsu amma taqi,saboda bata da wani karsashi ko farincikin hirar,tunda ta dawo sati biyu cikin na uku zuciyarta a quntace take,ba wani walwala ko farinciki.

Wayarta ta zaro ta sake kallon fuskar wayar,cikin sarewa da gajiyawa ta dora wayar saman table din data aje littafin nata sannan ta zame ta kwantar da fuskarta saman table din,daga dawowarta zuwa yau batasan sau nawa ta duba fuskar wayarta ba,haka kawai taji tana tsimayin kira daga gareshi,saidai ko sau daya bai kirata din ba,tana ta sanya rai taji ance tazo gashi,duk da tasan ba bari ake azo ganin naka ba idan bada wani babban uzuri ko dalili ba,amma tata zuciyar nata shauqin jin hakan,saidai shuru,lumshe idanunta tayi tana jin yadda zuciyarta ke tabuwa,ba zata taba kiransa ko sau daya ba,sabida tayi alqawarin jan ajinta da mutuncinta,zata kuma cika burin anni in sha Allah

"Maimoon,lafiya?,me ya sameki?" Taji muryar afra saman kanta,sai ta bude idanunta da kyau a kan fuskar afran

"Me kike gani?"

"Kuka.....hawaye fa kike?" Bata yarda da zancan afra ba sai data sanya hannu ta shafi fuskar tata sannan taji danshinsu,abinda ya sake sanya zuciyarta karyewa,kawai sai ta saki kukanta sosai tana kifa kanta a table din.

Da sauri afrah taja kujera dab da ita ta zauna tana fadin

"Innalillahi,wai menene yake damunki maimoon?,meye matsalar?" Bata bata amsa ba,sai kawai tasa hannu ta zare wayarta dake gefe,tasan me zatayi mata.

Contact ta shiga ta fara laluben sunayen soyayya data sama wata contact,saidai babu ko daya a ciki data gani,haka ta haqura,ta sanya ainihin sunansa saiga number din ta fito,kallon maimunatu da batasan ma tanayi ba tayi taja qaramin tsaki,wai itakam yaushe zata bude zuciyarta ta yarda soyayya takeyi?,ta kuma gane ita ke wahalar da ita?,kawai saita canza sunan dake kan number zuwa honey bee,sannan kanta tsaye ta danna masa kira.

Dai dai lokacin yana kwance a wajen hutawa daya ware cikin office dinsa,tunda yazo yake zaune a wajen,ya gaza hassala komai,baisan me yake damunsa ba,gaba daya tunda ta tafi ta tafi da walwalarsa,hannunsa daya bisa fuskarsa,sai yaji shigowar kira wayarsa.

Har tayi ringing dinta ta katse bai dauka ba,ta sake shigowa ta kuma katsewa,ya shareta yana ci gaba da kwanciyarsa,har sai da yaji qishirwa,sannan ya miqe zaune ya jawo wayar yana son duba lokaci,don da wuri zai fita daga company din yau,saboda ya lura bazai iya aikata wani abun kirki ba.

Ganin miscall da number ta yasa ya tashi ya zauna sosai,bai zaci wayarsu na amfani ba a school,daga sama kuna tex ne

_ka kira pls yaa ja'afar,qawar maimoon ce_

Bai gama karantawa ba ya fita a saqon ya kira number din,yana jin yadda zuciyarsa ta tafi gaba daya ta kuma afu gason jin muryarta.

Da sauri afra ta duba kiran sannan ta dan matsa gefe kadan daga inda maimunatu ke zaune ta daga

"What's happening?" Ya tambaya kai tsaye,jin ba muryar maimunatun bace

"Kuka dai takeyi,na tambayeta taqi magana"

"Bata wayar" ya fada cikin jin wani tashin hankali yana shigarsa,meye ya sameta?,itace tambayar daya fara yiwa kansa.

"Yaa ja'afar ne" ta rada mata a hankali,kafin ta gama fuskantarta har ta nana mata wayar a kunne

"Angel" ya furta cikin wani irin taushi,da zuzzurfar muryarsa data aike mata da wasu saqonni lungu da saqo na jikinta karo daya,wani nauyi taji zuciyarta tayi,hawayenta kuma ya dauke cak,ta zuqi numfashi sosai tanason fesarwa amma kamar ya riqe

"Hello.....angel,my moon" ya sake fada very softly,wannan karon fidda numfashin tayi gaba daya,wanda ya zame mata kamar ajiyar zuciya mai sauti,batasan sanda tasa hannu ta dafe wayar sosai a kunnenta ba,har yanzu idanuwanta suna rufe tana sauraren saukar numfashin sa daga cikin wayar,da alama shima ta taba zuciyarsa sosai

"Say something mana angel,bazan iya jurewa ba,meye ya faru?"

"Zazzabi" ta fada muryarta a mugun narke,kuka mara sauti me dauke da hawaye yana kubce mata

"Ya salam......jirani gani nan zuwa" ya fada yana katse wayar gaba daya.

A gaggauce ya maida takalminsa ya kira PA yayi cigiyar key din motarsa,ya karba ya fice ba tare daya tsaya sauraren kowa ko kuma meeting dake gabansa awa daya mai zuwa ba.

Kasa motsawa tayi daga wajen,sai kunnuwanta suka shiga maimaito mata abinda yace

"Ta jirashi gashinan?,da gaske zuwan zaiyi??" Zuciyarta dai ta cika da wasi wasi,amma duk da haka sai tayi likimo taci gaba da kwanciya a wajen,har zuwa sanda ta tsinci muryar afra na kiranta irin kiran gaggawa,idanuwa kawai ta bude tana jiran isowarta

"Ana kiranki office din principal,yaa ja'afar ne yazo" batasan ta miqe da hanzari ba sai data ji kanta ya saara,ta dafe kanta da hannunta sannan ta dubi afra

"Muje ki rakani please" hannunta ta riqe tana murmushi,tanason tsokanarta amma kuma yanayinta yana nuna seriousness dinta kan condition din duk da take ciki,don haka shuru tayi tana taka mata zuwa office din.

A nutse tayi sallama a office din,idanuwanta na kallon qasa,don ta tabbatar indai idanunta a dage suke kuma yana cikin office din,tofa lallai idanunsa suna kanta ne,ita kuma a yanzun batajin zata iya dauke idanunsa akanta,bata jin zata iya jurema wannan kallon nasa,qamshinsa kawai ya isa ya bata tabbacin yana cikin office din,taci gaba da takawa a hankali,sai zuciyarta ta gaza jurema rashin kallon fuskarsa,ta yanke shawarar ko satar kallonsa ne tayi.

Ta kuwa aikata hakan,saidai kuma ya kamata,don caraf idanuwansu suka hadu waje daya,yana binta da wani irin mayen kallon da shi kadai yasan fassararsa,gaba daya yaga kamar an sake canza masa ita,ta sake kyau ta sake fresh,saidai tadan faada kadan

"Zaki bishi zakuje ku dawo" principal din ya fada kansa tsaye,tunda yasan waye ja'afar din a wajenta

"Okay sir" ta fada kanta a qasa,sannan ta miqe ta soma takawa a hankali tana ficewa a office din da zummar zuwa dakinsu ta gani idan akwai abinda zata dauko.

A hankali taji an riqo hannunta ta baya a tausashe tana hanyar komawa hostel,da sauri ta waiwayo,tadan razana saboda hanyace da babu masu wucewa sosai a kanta,sannan kuma batasan ana biye da ita ba.

Idanuwansu suka sarqe waje guda,kowanne ya jefi dan uwansa da wani abu mai matuqar tasiri a ruhi da gangar jiki,suka shiga jin kamar zasu narke a wajen saboda abinda ke zagaya zugata da gangar jikinsu,sukaci gaba kuma da kallon junansu kamar an manne idanuwan nasu cikin na juna ne,bata ankara ba ba zato taji ya fusgeta zuwa cikin jikinsa da wani irin zafi,har takalmin qafarta yana zamewa daga qafartata.
Chapter 98 · 0% Book details