← Book details Gurbin Ido Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 113

Sashe 103

Gurbin Ido Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Banason kukan nan Angel,badon kiyi kuka ba na tsaya na nemo abbunki,don kiyi farinciki ne,ki kuma rayu cikin farinciki,kukanki ko......bakisan yadda yakemin ciwo a zuciyata ba" sassauta sautin kukan tayi,duk da bata bar zubar hawayen ba.

Shi ya da kansa ya kuskure mata baki yayi mata alwala,sannan ya hada mata tea tasha sannan ya zauna gefanta yana kallonta

"Zanje gida yanzu na dawo,but da sauri sauri,me dame zan dauko miki?,baxan bari su sallameki ba saikin warke sosai" kai ta langabe a shagwabe tana jin tea din daya bata yana damunta a qirji

"Abbu na"
"Don't worry,barci yake,ance kuma kada a tasheshi,yana farkawa zan kaiki wajensa in sha Allah" kai ta gyada masa, sukayi sallama yana kissing goshinta,sannan ya fita.
[11/25, 7:22 AM] Safiyyatulkiram: 81

Tare da anni da baba tabawa suka tafi,akabar ammi a nan,saboda baba tabawan zataje tayo girki sai ta dawo sannan ammi ta tafi,shima abbi acan suka barshi.

Suna hanya suna tattauna yadda abubuwan suka kasance,anni ta saki ajiyar zuciya

"Kaidai manya Allah ubangiji yayi maka albarka,ka gama min komai,abinda yake kullum cikin nuri da mafarkina yau gashi ga cikamin shi,na sake tabbatarwa na kuma samu nutsuwa kan zamantakewarka da maimunatu,Allah yayi maka albarka" murmushi kawai ya saki baice komai ba,yau anni ke magana dashi a haka,tabbas ba qaramin dadi abubuwan sukayi mata ba.

A reception ammi ta zauna ta bawa hajja da maimunatu waje,hajjan na zaune gaban maimunatu,hannunta cikin na maimunatun tana kallonta,tana jin kamar ta maidata cikinta,kota ina ka kalleta zaka san jininta ce ita,ta dauko wasu abubuwa nasu sosai,duk da kamanninta sunfi.rinjaye dana mahaifiyarta,wadda hajja bata taba gani ba sai a hoto.

Itama maimunatun kallon fuskar dattijuwar take,tana jin wani farinciki mara misaltuwa yana saukar mata,wai yau itace take da kaaka?,yau itace zaune gata ga mahaifiyar mahaifinta?,abun sai take jinsa kamar a mafarki,amma kuma tana mata yanayi da wata fuska data sani

"Sannu diyam,sannunki,ina mahaifiyarki?,ina fata batayi fushi da abubakar ba?,bata masa kuma mummunan fahimta ba?, jarrabawa ce ta samu abubukar,qaddarar rayuwa da kowanne bawa baya iya tsallake mata" hajjan ta fada tana share qwalla

"Daadata ta rasu" maimunatu ta fada muryarta a karye tana rawa,cikin kaduwa hajja ta kalleta

"Aishatu ta rasu?,wayyo abubukar,bansan yadda zaka dauki wannan qaddarar ba,ina dan uwa ko 'yar uwarki da mahaifinku ya tafi ya bari da cikinsa?"

"Ta rasu wajen haihuwarsa" ta fada tana rushewa da kuka,sai hajja ta jata zuwa cikin jikinta tana tayata kukan,sosai maimunatu ta dinga jin wata nutsuwa da sukuni sanda take jikin hajjan,sai taji kamar wani sashe na mahaifiyarta ne ya dawo.

Sautin kuka suka fara ji daga bakin qofar dakin sannan kuma aka turo qofar,afra ce sanye da hijab har qasa,amma idanuwanta shabe shabe da hawaye.

Tashi maimunatu tayi daga jikin hajjan tana duban afra cikin mamakin yadda akayi tasan bata da lafiya tazo gurinta,yayin da afrah ke kallon hajja da maimunatun gaba daya,tana shiga zurfin tunani,sai hajja ta sauqaqe mata ta hanyar daga mata hannu

"Zo nan,qaraso ciki fannah(asalin sunan afrah,sunan mahaifiyar hajja), shigo kiga 'yaruwarki da mahaifinku ya baro a gembu" idanu afrah ta waro gaba daya tana duban hajjan ta gani wai ko tsakanarta take?,waiko tasan maimunatu ido da ido,ta kuma san irin aminci da shaquwar dake tsakaninsu shine takeson tsokanarta?,to amma kuma ko daya bata ga alamun wasa a tattare da ita ba,take zuciyarta ta gaya mata babu ko shakka dai daine abinda hajja ta gaya mata,yayin da maimunatu ita kuma ta zubawa hajja ido cike da mamaki da son fahimtar zancanta,afreen dinta 'yar uwarta ce ta jini?,kafin ta lalubo amsa afran ta sheqo a guje,tana isowa kuma ta rungume maimunatu a jikinta

"Da gaske kike hajja don Allah, maimoon dita ashe 'yar uwata ce?" Kacamewa sukayi da kuka gaba dayansu,har sautin kukan nasu yaja hankalin alhaji mansur qani ga abubakar din.

Shi ya tsaya kansu yana musu fadan kukan kafin kowacce ta sassauta kukan,ya fice yana gaya musu kada ya sakeji.

"Nifa ji nake kamar mafarki,dama abbana abbanki ne?" Murmushi maimunatu tayi,ita daya daga ita sai ubangijinta ne kadai a yau suka san irin farincikin da take ciki,ta qagu abbanta ya farka akwai.maganganu masu yawa tasan da zasuyi

"Abbanki shine abbuu na da ya bata tun ina qarama,saidai bazan taba iya manta fuskarsa ba" hajja ce ta bata labarin yadda komai ya wakana,anan maimunatu taji cewar ja'afar ne yabi diddigi tsahon wata kusan biyu yana neman dangin mahaifin nata,ya baza cigiya daga gembu ya dinga bibiya har ya fahimci yana da nasaba da gombe,don haka binciken yazo masa da sauqi,har Allah yasa ya gano sunansa da komai nasa harda address,sanda yazo ma hajja da zancan batayi musu ba,don dama sunata neman suma su samu wanda yasan wani abu da zai zame musu haske zuwa ga gembu don binciko shatu da diyoyinta,da ja'afar ya samu goyon baya,don su tabbatar da zarginsu sai ya kawo maimunatu gidan wajen abbun,cikin hikimar Allah kuma hasashensa ya zama gaskiya,tunda gashi har abbun ya kirayi sunanta,sunan da hajja ke jinsa a bakin abbun kafin ya gamu da hatsarin motar da yasa yayi loosing memory dinsa,ya manta dukka wani abu daya faru a baya cikin rayuwarsa

"Afra ita kadai ce diyar abubukar har kwanan gobe,sai kuma dan uwanta musaddiq,kece cikon ta ukun" hajjan ta fada farinciki na sake kamata na bayyanar jikarta.

Su biyu suka zauna cikin dakin sunata hirarraki da suka shafi rayuwar,hajja na gaya mata tarin dangin da take dasu cikin gombe da maiduguri asalin mahaifar hajjan,da kuma 'ya'yan qanne na mahaifin nata da rayuwarsa ta baya,abu guda ta gaza tambayar ta,yadda akayi abbun nata ya auri daadarta ba tare da kowa yasan garin ba har ya samu wannan matsalar data zama silar rabuwarsu dashi tsahon shekaru.

"alhamdulillah" abbu alhaji ateeq abubakar ya fada yana shafa addu'a,bayan ya idar da sallolin da suka kubce masa,jin kansa yake a yau sakayau,kamar yayi dogon bacci ya farka ne,kamar dukka abinda ya faru a sanda bai cikin hayyacinsa sun faru ne cikin mafarki

"Kaini wajen diyam"ya fadawa musaddiq dake zaune daura da mahaifin nasa,sai musaddiq din ya miqe

"Zauna abinka bari muje" alhj mansur ya fada yana miqewa tsaye

"Abba nima inason zuwa na ganta don Allah" musaddiq ya fada cikin kalar tausayi

"Bismillah muje" ya fada kana ya waiwaya ga abbuu

"Zan iya takawa da kaina,bana jin komai a jikina" alhj ateeq ya fada yana miqewa da karsashinsa.

Da sallama ya shigo dakin,hajja ta miqe cikin farinciki

"Ma sha Allah,Allah mun gode maka,Allah mun gode maka" ta fada tana qwallar farinciki,gaban gadon maimunatu ya nufa kai tsaye ya zauna yana dubanta,cikin qauna kunya da jin nauyi ta gaidashi bayan ta gaida yan uwansa da suke a matsayin kawunanta a yanxu

"Diyam ina shatu?" Itace tambayar farko daya fara mata,kamar ba zatace komai ba,saidai cikin raunin murya tace

"Allah yayi mata rasuwa ita da abinda yake cikinta"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya fada sannan yayi qas da kansa,hajja da alhj mansur ke bashi baki,har zuwa sanda ya dago kansa

"Ina fata bata mutu tana fushi dani ba tare da tunanin guduwa nayi?" Kai ta girgiza tana hawaye

"Ko kadan abbuu,har ta mutu tana gayamin kai din mutumin kirki ne,ko guda bata taba ji a jikinta guduwa kayi ba,akwai gagrumin abinda ya faru dakai,ya kuma haneka dawowa zuwa garemu, kullum abinda take fada kenan" saita rushe da kuka,hakanan abbun shima ya kasa tsaida hawayensa

"Allahu akhbar,qaddara ta riga fata" alhj mansur ya fada,afra ma kukan take,yayin da musaddiq yaketa kallon yar uwar tasa,tausayinta yana kamashi,hajja ta jima tana gaya musu suna da 'yar uwa,amma ba'asan inda take ba,yau gasu gata.

Wani zama akayi na gayawa juna abubuwan da suka shude,har zuwa sanda akayi kiran sallar magariba su abbu suka fita sallah,ita kuma ta yunqura zata bandaki saboda yadda cikinta keta juya mata,batakai ga toilet din ba wani irin amai mai zafi ya yanke mata ta dinga sharara shi hajja na mata sannu,afra kuwa gaba daya ta rude,sai data gama suka kira cleaners suka gyara wajen ita kuma suka maidata gado tana maida numfashi,dr noor suka kira,sai data idar da sallah sannna tazo ta sake dubata,tace babu komai,idan ta sake zuwa anjima su gaya mata

"Karki gayama j don Allah" maimunatu ta fadawa afra qasa qasa,saboda tasan idan ta gaya masan hankalinsa zai tasa.

Kwana biyu rak sukayi a asibitin aka sallamesu gaba daya,duka suka dunguma suka wuce gidan alhaj abubukar,duk yadda ja'afar yaso ya dauke matarsa saboda yadda yayi kewarta amma anni tace dole yayi dagin qafa,dole dangi suna buqatar ganin diyar tasu,haka tana buqatar lokaci ita da mahaifin nata suga juna sosai,hakanan ba don yana so ba ya barta,amma kwana uku rak yace ya bata.

To ita dinma kewarsa sosai ta dinga yi,batasan cewa soyayyarsa tayi mata mummunar illa ba sai a sannan,komai takeyi yana maqale a cikin ranta,duk da tarin dandaxon 'yan uwa da kuma dangi daketa cika gidan kulli yaumin wajen ganinta,kuka ta dinga yi sosai,inama ace daadarta tana raye taga wannan ranar,kullum burinta shine ta sada maimunatu da mahaifinta,yau gata ga danginta tako ina,harda wadanda suke diban kamanni duka ta gani.

Kwananta biyu rak hajja ta hada gagarumar walima,dangi na kusa dana nesa kowa yazo,tace mata
Chapter 103 · 0% Book details