← Book details Gurbin Ido Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 113

Sashe 21

Gurbin Ido Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ameen,ameen ya hayyu ya qayyumu"anni ta fada tana jin dadin yadda tabawa ta fuskanceta

"Amma kuma wani hanzari ba gudu ba.….."

"Uhmmm,ina jinki tabawa"

"Kinsan akwai matuqar banbanci da tazara me yawa tsakanin manya(sunan da takan kira ja'afar dashi,saboda sunan babban malamin da yaci,kuma wasu sukan kirashi da sunan) da ita yarinyar?,kinsan kuma hali da dabi'ar yaran zamani,musamman shi daya keta qasashe da dama,yaga kuma mata iri iri,inajin kamar idan akace za'a bashi yarinyar nan a haka zai zama da matsala" murmushi anni tayi

"A hakan zaa bashi ita ba kuma a hakan za'a bashi ba" cikin rashin fahimta tabawa ta kalli anni don bata gane hausar ba

"Abinda nake nufi shine,inaso ki kulamin da duk abinda zata ci ta kuma sha,nasan ba lallai a yanzu ta farat daya ta dauki cimarmu ta iya sakin jiki taci yadda ya kamata ba,sannan ki kulamin da tsaftarta ki jata a jiki a kiyi mata duk abinda ya kamata,sauran abubuwan zanyi magana da salamatu,abinda ya samu zuwa sanda zai zo gida shikenan,zan bashi ita a haka,shi nakeso ya qarasa rainonta,kinsan hikimar yin hakan?" Kai tabawa ta girgiza tana duban anni

"Inaso ne yasan ciwonta,yasan dadi da kuma wuyarta,yadda bazai riqeta sakwa sakwa ba,sa'annan inason ya ginata kan tsari da dabi'ar da yakeso,ya dabi'anceta a yadda yakeson matarsa ta kasance,hakan shi zai bada damar da zata shiga zuciyarsa fiye da marigaiya shahida,don shahida tazo da tarbiyyar ta da kuma dabi'unta ne daga gida,ita kuma wannan shi zai saitata a yadda yakeso,zata kasance ne kan tsarin da duk yaso" sosai tunani da hangen anni ya yiwa tabawa dai dai,kuma hikimarta tayi mata,ta sha alwashin lallai zata yiwa annin duk abinda ta buqata,don tana cikin mutane na gaba gaba da takejin ciwo da zafin yadda har yanzu suka kasa shawo kan matsalar manya,tana jinsa kamar danta,don tun yana qarami take a gidan,da ita akayi rainonsa.

"Dubamin ita tabawa,ki duba ma'ajiyar kayan nan da aka dinka wancan watan ki ciccire mata wadanda zasu yi mata dai dai,inason ta fito muci abinci da ita anjima kadan"

"To an gama haj anni" tabawa ta fada tana miqewa.

Tana shirin fita a dakin sallamarsa cikin muryar dake cike da tarin nutsuwa da kuma haske na ilimi da dattako ta ratsa falon,dr marwan ne,sanye yake da lafiyayyar shadda ruwan qasa dinkin babbar riga 'yar ciki da wandonta,kansa kuwa hula ce da ba'a iya hangota saboda fari qal din rawanin dake nade a kansa,idanunsa sanye yake da farin gilashi dake qara masa qarfin gani,akwai cikakken gemu a fuskarsa wanda furfura ta fara yiwa ado ta gauraya da baqin dake jiki.

A girmame tayi maaa sannu da shigowa sannan ta juya ta fita a dakin,shi kuma ya sanya kai dakin mahaifiyar tasa,bakinsa dauke da sallama.

Fuska a sake ta amsa sallamar tata,sannan ta janye qafafunta don ya samu wajen zama saman lallausan carpet din da take kai,don qasa ne wajen zamansa duk sanda yazo gaidata.

"Kun sha hanya anni" ya furta bayan sun gama gaisawa da tambayar mutanen data baro.

"Wlh marwanu,amma alhmdlh,gamu a gida"

"Mun godewa Allah" ya fada yana murmushi

"inata zuba idanu na zaci baku qaraso ba,har ina shirin kiran jibril"

"Mun iso marwanu,kana tare da baqi lokacin.....na iso da baquwar yarinya ma"

"Eh tabbas,muna tare da ministern ilimi ne,batun da nakeso mu tattauna kenan dake akai" kai ta jinjina

"Nima akwai batun da xamu tattauna din,amma kamar lokaci bazai bamu dama ba,naga an kusa sallar magariba,inaga idan aka idar da sallar isha'i sai mu zauna"

"Eh hakan yayi anni,Allah ya nuna mana"

"Ameen.....amma kunyi waya da jabiru ne?" Dan dubanta yayi

"Sai da ya sanar miki kenan?"

"Kana da wadda ta fini ne marwanu?" Qas yayi da kansa

"Babu anni,amma banason tashin hankalinki ne ko kadan"

"Ja'afaru rayuwata ne,Allah ne ya doramin qaunarsa cikin dukka jikokina,idan har an aka fara boyen matsalar ja'afar saboda kada na shiga damuwa to kuwa ba'a kyautamin ba,zanyi dukkanin me yiwuwa ne don naga rayuwar jaafar ta daidaita kamar yadda take a baya"

"In sha Allah ba zata sake faruwa ba,kuma maganar da nakeso muyi din tana da alaqa da jaafar din"

"Allah yasa alkhairi"

"Khairan in sha Allah" ya amsa mata
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 14

Sanda aka gama musabaqar suna tsaye a jikin motar dr marwan(abbi) suna jiransa yayi kiransu,ya hadasu da mahaifin shaheeda da ita kanta shahidar suka gaisa,irin dadin da shaheeda taji ba qarami bane ganin cewa akwai sanayya tsakanin mahaifinta da nashi,ko meye zai dan zo mata da sauqi,ba kamar ace babu komai tsakaninsu ba,kwata kwata bata nuna wannan farincikin a fili ba saboda kamun kai da kuma tsira da mutunci.

Babu jimawa shaheeda ta ziyarci gidan dr marwan,nan da nan ta saba da mafi yawa na jama'ar gidan,tayi amfani da hikima da kuma hankalinta da wayo ta shiga jikin anni da amma mahaifiyar ja'afar sosai,a lokacin jaafar tuni sun koma hutunsu,bata damu ba tasan tana da target a kansa komai dadewa,baka isa kace son ja'afar take ba,don ko zancansa bata taba yi ba bare ka kawo hakan cikin ranka,saidai a hikimace ta gama karantar dabi'unsa daga hirarsa dake bakin 'yan uwansa,da kuma yawan ambatonsa da anni takeyi,ta gama gane abinda yakeso da wanda bayaso,ta haddacesu tsaf bisa kanta.

Sanda suka dawo hutu sun samu shaheeda a gidan,don tuni ta maida gidan wajen zuwanta,sun kuma saba sosai ta zama kamar 'yar gida,da yawa suna cewa saboda gidansu duka maza ne shi yasa tafison gidan baba dr kamar yadda take kiransa,don nata 'yan uwan duka maza ne,ita daya ce mace.

Eh tabbas,zamanta a gidan na mata dadi,saboda tana da abokan hira sosai ba kamar gidansu ba,saidai nata plan din ja'afar ne,boyayyen sirrinta da babu wanda ya sani,tayi qoqari matuqa wajen ganin ta janyo hankalinsa kanta cikin hikima da basira,ba tare da shi kansa ta bari ya fahimci komai ba,komai na ja'afar din dabanne,ita ke kula da wasu abubuwa nasa.

Da farko bai farga ba,saboda sam hankalinsa bashi a wajen,mma daga bisani ya soma fahimtarta,ya kira qanwarsa nadiya,ita yake nema idan yana buqatar wani abu da anni ko su amma basu iya ba ko ba zasu iya ba,wadda tasu tafi zuwa daya saboda kamanceceniyar da kuma nutsuwarta,ya yanka mata warning akan ta cire shaheeda akan duka sabgarsa sai idan shine ya buqata.

Farko nadiya ta kasa gayawa shaheeda,sai ita da kanta ta fahimta,ta kuma yiwa nadiya maganar,bata boye mata ba ta gaya mata,tun daga ranar shaheeda ta fita a sabgarsa gaba daya,duk wani abu da ya shafeshi ta fita a ciki,koda zaune take a wajen yazo zata tattara tabar wajen,hakanan abu idan ya dangaceshi komai yadda ta iya babu ita a ciki,abun yana cinta a rai,tana jin ciwo amma ta danne zuciyar tata,mutum ce mai yawan addu'a,maimakon damuwa ta rinjayeta,saita rinjayar da addu'a,takan hana idanunta barci ta tashi cikin dare ta gayawa Allah damuwarta.

Sannu a hankali shima ya fara noticing canzawarta,sai ya fara jin damuwa a kanta cikin zuciyarsa,shi da kansa ya dinga mamakin kansa,damuwa for what?,akan wata mace?,sannu sannu Allah ya fara matsa zuciyarsa,sai ga ja'afar da kansa ya fara nema shaheeda tayi masa wasu abubuwan,kamar kalolin girke girken da take masa a baya,amma fur sai ta murje idonta taqiyi,duk da yadda zuciyarta kan buga,taji babu dadi amma haka take mazewa.

Rana ta uku daya aika tace ace bata da lpy taqiyi zuciya tazo masa iya wuya,yana zaune a sannan yana duba saqonnin da yake samu daga companies na jiragen sama dakeson yin aiki tare dashi,zare laptop din yayi daga saman qafarsa ya ajjiyeta gefe ya miqe ya fice.

A dakinsu nadeeya ya samesu zaune an kafa majalisar hira,tana ta dariya tana dariya harda riqe ciki,Har kowa yayi shuru bata ankara ba,sai da taga hankalin kowa ya karkata ga qofa,sun kuma saka nutsuwa a jikinsu sannan ta ankara,tayi hanzarin jawo dankwalinta ta rufe lallausar sumarta ta fulani,gabanta na wani irin faduwa saboda zallar kwarjinin da yayi mata,tana jin kamar zaman ma ba zata iya ba.

Bata ji yace musu komai ba amma sai taga kowace ta fara miqewa tana fita a dakin,ganin sunata ficewa ba tare da tasan dalili ba sai itama ta miqe tayi joining dinsu.

Nadeeya ce qarshe sai ita,nadiya na fita ya matsa yayi blocking qofar gaba daya da jikinsa yana kallonta da idanunsa da suke fasa mata zuciya,tayi baya kadan ta kuma sauke kanta qas,don ba zata iya jurewa kallonsa ba,ta fara lanqwasa yatsunta,tana son tace ya matsa mata itama ta fita amma kuma tasan cewa tayi kadan ta iya fadin hakan.

"Baki da kunya ko?" Ya fada a taqaice kamar me ciwon baki,abinda yasa babu shiri ta daga kanta ta kalleshi,sai kuma ta sake saukarwa saboda idonsa yana kanta

"Ni sa'anki ne da zan dinga aikowa kiyimin abu kina rejecting,bakisan ba kowa nake sawa yayi mun abu ba?" Sosai maganar tasa tayi mata dadi,wani abu ya tsarga mata,gefe daya kuma rauni ya kama zuciyarta har ya sanya qwalla silalowa daga idanun nata tare da kalmar

"Kayi haquri" shuru na sakanni yayi kafin ya sauke hannayensa ya juya ya fara ficewa daga dakin,sai ta bishi da kallo har yabar wajen.

Kwata kwata ji tayi bataji dadi ba,cikin ranta kuma tana tsoron kada fa ta barar da damarta,a sukwane tayi kitchen ta fara hada masa abinda ya buqata a daxun,tana tsaka da aikin su safina suka shigo

"Me yayi miki?,me ya faru?" Tambayar da suka dinga mata kenan

"Ba abinda yayimin" ta amsa musu hankalinta na ga girkinta

"To wannan abincin fa?,naga bamu jima da gama cin abinci ba" safina ta fada tana bude tukunyar

"Na yaa ja'afar ne" amsar daya sanyasu kallon kallo a junansu,suka fara kuma tsegumin anya kuwa?,bata bi ta kansu ba,itadai burinta ta gama ta kai masa.

Sanda khadim yakai masa dawowa dashi akayi,yace bayaso,abinda yasa hankalinta ya tashi sosai,ta kuma boye ta dinga kuka,washegari ta hada kayanta tace zataje,duk da kwanakin da takeyi basu cika ba.

Kwana biyu rak a tsakani ya karanci bata gidan,yayi kaman ya share amma sai yaji ya kasa,ya kira nadeeya ta tambayeta,bata boye masa ba ta gaya masa duk abinda ta sani,ya sallameta,sannan yayi shuru shi daya yana tunani,rashin cin abinda ta aiko masa ne ya kawo faruwar hakan?,washegari sai ya tsinci kansa da shiryawa ya tafi gidan daukota,babu ko rakiyar jabir.
Chapter 21 · 0% Book details