← Book details Gurbin Ido Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 113

Sashe 55

Gurbin Ido Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanda mr Rebecca ta turo qofar take shaida mata anzo daukarta sama sama take jinta,amma cikin qarfin hali ta amsa mata da to,wani sashe na zuciyarta tana jin ya sake,ta samu sauqin tunanin wani abu me muni ne ya samu hisham din,mr rebacca ce ta dauka wasu kayan tace bari ta fitar mata dasu,ita kuma ta lallaba ta miqe a hankali,saita koma ta zauna,saboda jinta da tayi kamar tana yawo kan iska,ta dafe kanta da hannunta tana jin kamar zai fado

"Kamar yana sauri ne,zan fita miki da sauran kayan,kiyi ki fito" tafadi ba tare data lura da yanayinta ba tana daukan jakarta data rage ta fice.

Agogon gaban motar ya kalla,mintuna kusan hudu kenan yana jiranta?,me ta tsaya yi ya tambayi kansa a zafafe,baya son xaman jira ko qanqani,dabi'ar da yafi tsana kenan,sai ya daga kansa don duba hanyar da zata sadaka da dakunan kwanan nasu,dai dai sanda take fitowa,tana takawa ne a hankali cike da takatsantsan saboda yadda takejin jikinta kamar ba nata ba,iska kuma nason wasa da ita daga hagu zuwa dama,fuskarta tadan tasa kadan wala'alla zafi zazzabi ya sanya hakan,lokaci bayan lokaci tana sanya tafin hannunta tana dafe kuncinta,har yanzu baby face dinta tana nan,saidai ta fara cika,ta kuma fara sauyawa,fuskar shaheeda ce ta fado masa at her age,a irin wannan lokacin datake dalibar secondary kamar haka,a wata rana da yayi mata surprise,yazo daukarta daga makaranta ranar daya samu cikar burinsa a sannan,ranar da ya zama samu shaidar zama cikakken matuqin jirgin sama me lasisi,irin murna da d'oki da ya gani saman fuskarta a sannan

"Ban zaci ganinka ba,har kazo da kanka daukana?" Shine abinda shaheeda tace

"Saboda me?" Ya tambayeta kai tsaye,shuru ta danyi still tana murmushi,da alama tana masa kaara ne akan abinda zata fada

"Uhmmm,say it,say your mind" murmushi ta sakeyi ta girgiza kanta

"Ka barshi kawai"
"Saikin fada.....koni na ari bakinki naci miki albasa....mutum ne kai mai wahalar fahimta,me tsaurin ra'ayi,mara sakewa da mutane mara alqibla" baki ta rufe tana dariya,matsalarta dashi kenan,he can say her mind daga kallon qwayar idanunta kawai,yana da wannan baiwar sosai,shi yasa duk sanda ya dage saita kalleshi ido cikin ido ba kasafai ta fiya yadda ba,baya ga dafi da zai barwa gangar jiki da zuciyarta kuma sai ya karanto sirrinta

"Nidai ban fada ba"
"Ni kuma na fada,with all these lapses ma cancanci a bani soyayya..... I don't know what to say...mafi qarancin abinda zance shine, thank you for opening my eyes and showing me the way, thank you for loving me" kalamansa sun mata dadi sosai,kuma ta sake tabbatar da cewa lallai mahaqurci mawadaci ne.

A daddafe take qarasowa cikin wata tafiya da tayi kama da takun isa ko yanga,wanda sam babu daya daga cikin abu biyun illa ciwon da takeji a dukka gabbanta,tun daga nesa idanunta ya sauka akan rolls Royce ghost din,tana da yaqinin ba motar hisham bace,ba kuma tasan me motar ba,don bata taba ganinta ba,don haka koda ta isa sai taja ta tsaya tana dan duba gefenta ko xata hangi motar hisham,wala'alla wanna motar ba ita tazo dauka ba.

Idanununsa ya bude a hankali daga dogon tunanin da ya tafi jin shuru har yanzu ba ita ba alamarta,kai tsaye a kanta suka sauka sanda take dube duben,sai ya sanya hannunsa saman hon na motar ya danneshi ba tare daya dauke dubansa daga gareta ba.

Wani irin firgewa tayi saboda yadda qarar ya saukar mata a bazata,baqaqen gilasai ne,bata tsammaci ma kwata kwata da mutum cikin motar ba,qafafunta ne gaba daya sukayi wani irin laushin da bazasu iya daukarta ba,tilas ta sulale a wajen tana dafe da kunnuwanta,jikinta na wani irin rawa.

A hankali ya bude murfin motar ya fito,ya fara takawa zuwa inda ta sulale din,tana tsugune a wajen ta cure waje guda,yaga yadda ta tsorata din ta cikin mudubin motar

"Get up" ya fada a taqaice yana duban ginin makarantar cikin yanayi na nazari,yayin da sautin muryarsa ya sake sanya maimunatun qara dimaucewa,tsoronsa ya sake shigarta.

Idanunsa ya sauke akanta jin bata motsa ba,bata kuma ce komai ba kamar bata wajen,sai ya lura da yadda jikinta yake rawa,da gasken tsoratar tayi sosai?,kafin ya sake cewa komai miss rebacca dake goye da jakarta ta iso wajen

"What's happening?,sir...kamar bata da lafiya sosai fa,ko jikin ne?" Ta fada tana qarasa kusa da maimunatu ta kama kafadarta tana tambayarta,sannan ta fara qoqarin dagota

"Sir....jikinta da zafi sosai,clinic sun rufe suma,saidai idan kun fita ku samu wani a waje a samo mata magani" ta fada cikin girmamawa bayan ta raka maimunatu cikin mota ta zaunar da ita

"Thank you" ya fada a taqaice,sannan ya taka zuwa motar ya shiga ya tada ita,saidai can deep inside him yana jin wani ba dadi a cikin ran nasa.

Tunda suka fara tafiya qwaqwqwaran motsi batayi ba cikin motar,sai ma sake takurewa da tayi saboda yadda uwar ac din daya balbalawa motar take barazanar hallakata,mugun sanyi takeji kamar me,ga na zazzabi ga na sanyin ac,abinda ya sake galabaitar da ita kenan,sanda take shirin ta bude murfin motar tana shirin fitowa wani zazzafan amai ya kubce mata,duk yadda taso kada tayishi cikin motar amma yaci qarfinta,take ta wanke jikinta zuwa qasan motar,sai ya zare seatbelt dinsa yana fitowa daga cikin motar.

Zagayowa yayi,yayi tsaye a inda take aman yanayin fuskarsa na sauyawa

"Why J,why?" Ya samu kansa da tuhumar kansa da kansa,yadda take ta yunqurin aman ya isa gaya maka tana jin ba dadi sosai a dukka jikinta,baisan kuma yadda zai taimaka mata ba,sai ya dan tura mata murfin motar ta sake dafeshi kuwa sosai taci gaba da kelaya amanta.

Ruwan roba ya fidda a motar ya miqa mata sanda ta gama aman,a galabaice ta karba,sai data kusa minti biyu sannan ta iya kuskure bakinta ta zubar,yasa hannunsa ya rufe motar,sannan ga zagaya seat dinsa ya sake shiga ya tashi motar a hankali yana yiwa mai gadi hon ya dage masa qofar suka sake ficewa daga gidan ba tare da ko ciki sun shiga ba.

Ganin yadda take rawar sanyi sai yasa hannu ya kashe ac din,tuqi yake a hankali yana tunanin wanne asibiti zai kaita?,daga qarshe dai ya samu kansa da yiwa kansa jagora zuwa asibitin da marigayiya shaheeda ke ganin likita.

Sun dan sha fama kafin a gano file din nata,idanunsa akan sunan dake jikin file din,sai ya janyeshi gefe yana gayawa receptionist din,su maida wannan a bude sabo da wani sunan daban.

"Me sunan da za'a zaka?" Ya tambayeshi

"Maimun.....maimun ja'afar" bakinsa ya subuce kawai yaji ya furta hakan,sai ya maida kansa ga wayarsa yana juya sunan a cikin ransa.

Bayan likita ya gama ganinta dole yasa aka bata daki saboda yadda take sake galabaita,tana ta aman,yasa kuma aka jona mata ruwa bayan ya mata allurai,cikin lokaci qanqani bacci ya dauketa saman gadon.

Idanunsa yadan kai kanta,fuskarta har tadan yi fayau akan ganin da yayi mata dazun,wani abu me kama da tausayinta ya tsarga masa,yana ganin kamar hon din daya danqara mata shi yayi silar ta'azzarar ciwon,don likitan ya fada,akwai abinda kamar ya razanata,dubansa yakai ga hijabin dake wuyanta tun dazun,wanda dashi akasha gwagwarmayar aman,akwai buqatar a cire mata shi,to amma bazai iya tabata ba,agogo ya kalla,baisan yaushe zaa sallamesu ba,uwa uba ma likitan yace sai yadda yaga jikin nata,sannan shi kansa drip din kadan kadan yake diga,bazaiyiwu yayita zama ba yabar duk aikin dake gabansa,don haka ya fidda wayarsa ya soma duba number anni.

Har zai kirata ya fasa,ya duba number baba tabawa,Allah ya taimaka kuwa ya ganta,ya cilla mata kiran,ya kuma gaya mata driver ya daukota yanzu ya kawota asibitin,dai dai lokacin suna tare da anni tana hada mata kwadon zogale,sai ta dubeta

"Manya ne ya kirani,wai Doma,doma hospital" cikin mamaki anni ta kalleta

"Waye kuma ba lafiya?"

"Baice komai ba haj anni,kinsan hali dai"

"Ko shine?" Yadda annin tayi maganar cikin damuwa ma sai yadan baiwa baba tabawa dariya

"Kai haba dai,shi dinne bashi da lafiya zai kirani?,kamar ma kin manta halin mutuminki?,shi da ko sanda yana matashinsa ma saidai yayi ciwonsa a daki yagama ba wanda ya sani,saidai idan anga fuskarsa ta sauya?" Kai anni ta gyada,ta tuna mata kam abinda ta sha'afa

"Kamomin shi a wayar taki" bata musa ba ta koma kiran nass,dab da zata tsinke ya daga,kafin yace komai sallamar anni ta cika kunnansa

"Ka kira tabawa kace tazo asibiti,sannan kuma bakayi cikakken bayani ba,waye ne ba lafiya?" Shuru ya danyi kadan,yana rarraba hankalinsa kan sunan da zaya kirayeta dashi,a hankali ya furta.......
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 38

Sanda sukai jarabawar first semester ta goma sha biyar tazo cikin su arba'in,ko kadan hakan bai mata dadi ba,saboda ta saba,har ta gama rayuwar primary dinta bata wuce ta biyar,bata nunama kowa ba sai aminanta kuma roommates dinta,afra ce tace

"Naga qoqarinki ma maimoon(sunan da suka koma ce mata kenan),a wata uku kacal kin doke mutum ashirin da biyar?" Kai ya girgiza sanda take hada kayanta,don a gobe kowa zai wuce gida hutu

"Ina qoqari a nan afreen(sunan da ita dinma take kiranta dashi),bazan iya nunawa kowa result dina ba"

"Zaki iya maimoon,i trust you,duk wanda ya iya arabic,boko bazai bashi wahala ba sam sam sam,boko minor abune akan arabic"

"Next time I will try my best in sha Allah" ta amsa mata tana sakar mata murmushi,tare da jin dadin irin qwarin gwiwar da ko yaushe afra take bata.

Washegari tana ta zuba idanun ganin wanda zayazo daukarta saiga yaa hisham,ya fito suka gaisa dasu afra,ya kuma gabatar musu da kansa da kansa a matsayin yayan maimunatu,sosai abun ya mata dadi,ya girmamasu ya kuma mutuntasu a mazauninsu na aminanta,su kansu sun nuna jin dadin hakan,afra taso su gaisa da 'yan gidansu,suga kuma sabuwar aminiyarta,to amma ya hisham din ya bada uzurin yana da patient da zai gani,dole sukayi sallama suka shiga mota.

Yana qoqarin tada motar ya lura da envelope din hannunta,wadda ke dauke da tambarin makarantar,sai ya miqa hannu

"Duk da ba'ayimin tayin ganin result din ba,nayi shishshigi,a bani na gani" idanu tadan zaro,ta yima kanta alqawarin babu wanda zai gani,har sai tayi abun arziqi,amma tana jin nauyin hisham din
Chapter 55 · 0% Book details