Sashe 71
Gurbin Ido Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga annin har haj munubiyan suma sai da duka bisu da kallo,saidai kowanne da irin kallon da yake musu,ta fannin anni wani farinciki ne ya tsarga mata,zallar dacewa ta hango mai yawa tsakaninsa da maimunatu,ganinsu tare kuma ya ninka kwadayinta nason daidaituwar al'amura a tsakaninsu,ya kuma sake saka mata kwadayin son dorewar alaqarsu,sannan kuma ta hangi wani haske a tattare dasu da take fatan tabbatarsa da kuma dorewarsa.
Haj munubiya kuwa wani abu ne yayi mata tsaye a rai mai kama da kishi qyashi da hassada,tun shigowar unaisan ita kadai ta fara jin hakan,a yanzun kuma ya sake qaruwa da shigowar maimunatu da ja'afar din,yadda taga ya sake fresh ya kuma qara haske ya tabbatar msta da gaskiyan labaran da suke ji a kansa na yadda yaketa samun budi,arziqinsa kuma ke dada ninkuwa,wannan shine dai dai lokacin da ya kamata ace diyarta ta kasance daya daga cikin jerin matansa,saidai sam bata mata sha'awar zama mace ta uku kwata kwata,inda da hali so takeyi ta zama mace qwalli daua tilo ga ja'afar din,to amma hausawa sukance da babu gwanda babu dadi,ya kamata tayi wani abu akai,ta kuma gwada sa'arta,koda basu zama du uku ba ya kasance su biyu ne,wannan tunanin yasa ta sake fuskarta sosai tana gyara zamanta gami da dubansu maimunatu tare da sanya baki wajen musu marhaba,tana kuma qara kaifin hankalinta da hasashenta akan fuskar unaisa,take ta fara shinshino al'amura,ta kuma fara kuma tunanin daga inda zata dasa harsashinta.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 54
Kudin da iya su kenan cikin abinda ta mallaka?,sai ragowar dabbobin da suketa sulalewa suna qarewa daya bayan daya,sauran kuma suna bushewa kamar ana lasarsu?.
Sallamar jauro yayi dai dai da tunanin daya darsu a ranta na cewa tabbas shine ya debe mata kudin,domin kuwa taga yana ta gyaran bangare daya na cikin gidan,idan bashi ba bataga wanda zai debar mata kudi ba,tunda dai saman katifar suke kwana,kwana biyu ne ma yayi qaura yabar dakin saboda fushin da yake da ita kan abinda ke faruwa game da gajee.
Zumbur tayi ta miqe ta fito,tayi tsaye a bakin qofar dakin nata,hannuwanta a qugu tana kallonsa,sai ta zare hannuwan nata ta miqa masa tana dubansa da idanuwanta dake cike taf da rashin kunya da diban albarka,bin hannuwan nata yayi da kallo cikin mamaki,don baisan me take nufi ba
"Meye hakan ke kuma?"
"Ai kafi kowa sani,kudi na....kudi na nake so ka tafen ka bani,kuma wallahi sisi idan yayi ciwon kai sai ka fiddoshi" kallon mara cikakken hankali yake mata,don shi gaba daya kwana biyun nan kamar a zare kuma a firgice yake ganinta
"Kanki daya kuwa?" Ya soma da tambayarta,saboda yasan ta inda zai kamo maganganun dake bakinsa
"Ras nake jauro,kuma babu abinda zaka layancemin,kudina kawai nake da buqata,zaa cuceni a ha'inceni,har an tada gini ban sani ba" qare mata kallo tas yayi,yadda take girgije girgije ya tabbatar masa da gaske take maganarta,shikam a yanzun bashi da magana da ita,burinsa kawai ya gama gininsa lafiya Lau a daura masa aure da bazawararsa sadiya,ya tabbatar zatayi dai dai da furera da kuma dukka iskancin dake kanta
"Allah ya baki lafiya furera,na fuskanci tunda dabbobin marainiya suka fara kama gabansu aka soma taba naki tunanin,Allah ya kawo manzan sauqi,amma ki sani,koda zanyi sata bazan saci dukiyar haram dukiyar marayu irin taki ba,na dirkawa cikina wutar sa'ira,zan shiga dakina,kada kuma ki kuskura ki biyoni ballantana kice zakimin hauka,kije can ki nema inda dukiyarki ta salwanta" ya dire maganar tasa cikin tsananin kaushi da tsaurara harshe,sannan yayi gaba abinsa dauke da jakar buhun da ya dawo da ita daga cin kasuwar cikin wani qauye dake gaban nasu.
Binsa tayi da kallo,tafi kowa sanin jauro,kuma yadda yayi maganar ya sagar mata da gwiwa,tare da debe tunanin shi ya dauka kudin,sai ta koma bakin karan gadon ta zauna gwiwa a sanyaye tana zurfafa tunaninta kan inda kudinta suka shiga.
Zumbur ta sake miqewa tana kama sunan gaje,sai a sannan ma ta tuna yarinyar bata shigo gida ba har yanxu,mayafinta taja sannan tayo waje ba tare da neman izini ko ta tsaya gayawa jauron zata fita ba.
Tana tafe a hanya tana surutai ita kadai tare da tuna cewa dazu da safe sanda take fitowa daga bandaki taga fitowarta wuff daga dakinta,saidai bata kawo komai ba,ta dauka sauri take ta dauki kununta ne zata kada dabbobin su fice.
*GWAMBE*
Suna idar da sallar la'asar cikin masallacin dake cikin katafariyar ma'aikatar tasa ya dawo third floor,inda anan makeken office dinsa yake,direct ya isa saman freezer ya dauki agogonsa ya daura,sannan ya dauki hularsa yana gyara karinta,a hankali yana tuna abubuwan da suka faru a yau din,dukka abubuwane masu tsayawa a rai,kai qararshi zuwa ga anni sai abunda yafi komai tsaya masa a rai ba tare da yasan dalilin hakan ba.....irin kallon da yaga khalid yana jifanta dashi,kallon titsiye kallon qurilla kuma kallon haramun,lips dinsa na qasa ya cije yana jin kamar yanzun abin yake wakana,ya daga hannunsa da niyyar sanya hularsa saman kansa Jabir ya turo qofa ya shigo office din,wanda a yau wannan shine shigowarsa karo na wajen hudu,abinda kusan ba al'adarsa bace.
Duk shigowarsa ta dazun yayine don yaji wani abu daga bakinsa,saboda yana da masaniya akan kiransa da anni tace zatayi,da goyon bayansa ma ta aikata hakan,saidai ko a fuskar gogan bai nuna masa ba,duk da cewa ya karanci akwai wani abu a qasan ransa,uwa uba kuma basa boyewa junansu komai
"Fita zakayi ne?" Jabir ya fada,saboda yasan lokacin tashinsa bai qarasa ba,saura kusan one hour,shanyayyun idanunsa ya daga ya kalleshi
"Eh,i have to go,ina da uzuri"
"Munyi maka,mu masu mace daya ma muke samun kanmu cikin irin wadan nan uzurorin balle kai me biyu?" Yayi maganar ta manufa biyu ne,da kuma salon jan zance tare da neman tsokana,ya sani sarai,amma sai ya shareshi,baiko daga kai ya kalleshi ba bare ya biye masa suyi,saima yaci gaba da gyara hularsa,sannan ya qarasa gaban dan madaidaicin madubin dake manne da bango cikin office din,zaka zaci ma wani abune a wajen idan baka sani ba saboda design din da aka masa,ya kafa hular da kyau a gaban goshi,sai gashi ya fito fes da wani irin kyau me daukar hankali tare da kwarjini
"Allah ya gyaraka,yasa ka koma ja'afar dinka na asal" Jabir ya fadi a fili,a wannan karon waiwayowa ja'afar yayi ya kalleshi
"Wait.....wai me yasa yau ka takura min ne?"
"Saboda yau kake ango" ya furta yana danne dariyar dake cinsa,maganar tasa ja'afar qarasa waiwayo gaba dayansa,ya zuba masa shanyayyun idanun nan nasa
"Daina kallona haka malam,ba maimunatu ko unaisa bane"
"Duk wani zagon qasa da akemin na fuskanci dakai ake shiryashi ko?"
"Dai dai kenan,munason ka zama mutum kamar kowa,ka ajjiye wannan son bayan rai din,ka fuskanci reality,ka kuma yima shaheeda soyayya ta gaskiya ta hanyar samarwa kanka farinciki ka kuma dawwama da yi mata addu'a,da kula da abinda ta bari" kashe bakinsa gaba daya jabir yayi,ba wanda yasan abinda yakeji sai Allah,yana tsintar kansa a matuqar damuwa da qunci duk sanda ya tuna yadda ya wofantar da kulawa da soyayyarta,bai tashi fargar jaji ba sai daya rasata,wannan yafi komai damunsa da hanashi dukkan wani sukuni da walwala,akwai ciwo ya zamana kayi rashin mutumin dake maka soyayyar gaskiya,baka tashi gane hakan ba sai daka rasashi,ya tafi,yayi maka nisa,nisan da babu dawowa,koda zaka salwantar da dukka abinda ka mallaka don ganin dawowar tasa.
" Ga sauran agreement din nan,ka duba idan komai yayi ka sanya hannu,munata loosing opportunity dinmu,bansan a kwanakin nan me yasa ka kasa concentrating akan aiki ba,is there any problem?"
"Nop" ya amsa masa a taqaice,ya ciro wayarsa yana turawa driver dinsa tex kan ya fidda mota zai sauko
"Okay....i hope so" jabir din ya fada shima yana miqewa,ja'afar bai sake komai ba suka fito tare suna tattaunawa.
A parking lot suka rabu,jabir din yayi motarsa,shima ja'afar ya shiga tasa,ajiyar zuciya ya sauke sanda suke fitowa a company din,idanunsa na bisa titi yana wani tunanin na daban.
Maimunatu bata wani jima sosai ba a gidan su laila suka dawo,sai gidan ya rayu ya cika da hayaniya,don an jima ba'a hadu ba,rabonta da gidan tun kafin a koma makaranta,da aka dawo din nan kuma ta dawo da rashin lafiya,bata fito zuwa gidan ba sai yau.
Harda anty maama suka dawo ita da yaranta,duka a falon anni suka yada zango,sai maimunatun ta dinga jinta sakayau,zaman kadaici sam baiyi ba,hirar tasu ta dinga debe mata kewa,duk da ba kasafai take sanya musu baki ba
"Kiri kiri manya yaqi kawomin ke,kusan shekara daya tunda hisham ya kawoki har yau baki sake dawomin ba,shi yasa nima nayi fushi naqi zuwa gidanku" anty maama tace da maimunatu wadda ke lallabewa 'yar anty maama ta uku kanta da manyan kalba, yarinyar tana da suma,amma kuma batason kitso kwata kwata.
Murmushi tayi
"Makaranta yasa bai kawoni ba,amma zanzo anty in sha Allah"
"Ina zuba ido" ta amsa mata tana bude wata leda me dauke da wani babban tambari da kuma suna,wasu kayayyaki ne a ciki,ya fiddosu ta ware wasu,sai ta dubi maimunatu
"Allah yasa kina amfani dasu,siya nayi daga baya kuma dana duba naga sunmin yawa,kada su lalace ban shanyesu ba,kwashe wadan nan kiyi amfani dasu" kunya ce sosai ya saukarwa maimunatu sanda ta kalli kayan,ko wanda baisan na meye ba idan ya duba jiki zai gane,magunguna ne irin na ma'aurata,da bayaninsu balo balo a jiki,a kunyace ta debe tana cewa
"Na gode anty"
"Ba komai,amma akwai wani a ciki miqo in gani,ki shanyeshi,don idan yakai gobe tace zai lalace" ba zata iya cewa da ita komai ba,saboda kunya da kuma nauyinta da takeji,hakanan ta karba takai bakinta a hankali ta fara kurba.
Sosai abun yayi mata dadi a baki,tana sha gardinsa yana ratsa harshensa,shi ba gardin madara ba bana kwakwa ba,a hankali sai gashi ta gama dashi,dai dai sanda laila ke shigowa dauke da babban plate data shiga kitchen da kanta ta zubo musu abinci
"Me akasha ba'a rage mana ba,naga wani hadadden bottle haka a hannunki matar yaaya" tayi maganar tana ajjiye tray din tare da miqa wuya tana leqawa
"Matsa malama,ba irin naku bane,saiki jira sai anzo kanku"
"Don Allah a bani na dandana,da gani abun dadi ne wallahi anty maama kika sata a loko ita kadai kika bata" laila ta sake fada tana daga robar zata kai bakinta.
Buge roban anty maama tayi tana harararta