← Book details Gurbin Ido Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 113

Sashe 68

Gurbin Ido Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai daya gama shiryawa sannan ya tuna bashi da abinda zaici,ya sani yau baba tabawa ta koma gida,it means zaici gaba da bulayin neman abinci?,anya ba cook zai dauko ba kuwa ya aje cikin gidan?,sam ba girmansa bane a dinga ganinsa a eatery da sunan siyan abinci,bayan yana da komai,Allah ya mishi komai,yana da arziqin da idan abincin wata qasar yakeso yaci kullum to fa zai sameshi,sai ya miqe yana fita zuwa ga fridge din falonsa ko zai zamu wani abu da zai iya ci,gefe daya yana tunanin yadda zai gaya musu su shirya goben zasu wajen annin.

**********Karfe goma na safiyar washegari,wata safiya da aka tashi da haduwar gajimare wanda me dan duhu,cikin abubuwan dake alamta fara saukar damuna kowanne lokaci daga yanzu.

Tsaye a gaban daya daga cikin motocin dake fake a harabar gidan yake,sanye da wata shadda sky blue me matuqar kyau da daukan hankali,anyi mata dinkin zamani wanda ya dace da yanayin qirar jikinsa,ya kuma tafi da structure na jikinsa a matsayin cikakken namiji da ya amsa sunansa,mai haiba cikar kamala da kuma zati.

Qarasowarsa wajen kenan,cikin hanxari drivernsa ya fito yana karbar jakar hannunsa,gami da qoqarin bude masa seat din baya kamar yadda suka saba duk sanda xasu fita.

Hannu ya daga masa ya qarasa cikin coolness dinsa ya sanya hannu zaya bude gidan gaba,a dai dai lokacin ta qaraso cikin shigar wata irin gown da aka mata wani dinki,kanta yane da qaramin mayafi,yayin da fuskarta ke dauke da wani makeken sun glasses da yayi shigen kala da kayan jikinta,wani babban bangul ne a hannunta ke zobe guda daya,sai hig hill shoes data sanya a qafarta,mahadin figigiyar hand bag dinta,ta fito a unaisarta sak,unaisar shekarun baya,diyar gidan minister,shigarta gaba daya batayi kama da shigar wadda zata gidan surukanta ba,ga mutumin da ya fara ganinta yanzu,zaiyi zaton wani taro daya shafi siyasa ko kuma jiga jigan 'yan boko zata je.

"Good morning" ta fada cikin salo,idanuwanta na kan ja'afar,wanda tuni ya bude gaban motar yana yunqurin shigewa

"Morning" ya amsa mata a taqaice,sannan ya zura jikinsa a hankali kafin ya dauke qafafunsa dake saye cikin wani lafiyayyen half cover shoe na kamfanin louise vuitton,hannunsa dake daure da wani lafiyayyen gogon kamfanin Blancpain ya zura da niyyar rufe murfin motar,unaisa tabi hannun da kallo bayan ta gama qarewa takalminsa kallo,take ta sake sallamawa,da gasken gaske dan gayu ne shi din na qarshe,wanda yasan sirrin kwalliya tare da ta'ammali da designers kayayyaki,bata sake cewa komai ba itama,saiya bude back seat amma ta saitinsa ta shige,tana dora idanuwanta kan fuskarta da take iya hange ta madubin gaba,wanda tuni ya bude news paper ta safiyar ranar da drivern sa ya miqo masa,yawanci dukka safiya yakan dudduba jaridan data fito a safiyar,musamman page din da suke wallafa al'amuran da suka shafi kasuwanci.

Tana so ta tambayi wanda suke jira amma wani irin kwarjininsa daya cika motar ya hanata cewa komai,sai ta fidda wayarta ta bude watsapp dinta,ta hau turawa anty talatu saqo,abinda ya dan janye hankalinta kenan,saboda maganar da suke da anty talatun nada matuqar muhimmanci.

Karo na uku kenan ya daga kansa yana duban hanya da niyyar idan bata fito ba zasu wuce kawai,ta biyosu daga baya,har yadan fafa hasala,saidai bai nuna ba kamar yadda ko sau daya baiyi qorafi ba,kasancewarsa mutum ba mai yawan magana ba,saidai a cikin sa'a ya hangeta tana tahowa.

Glass din fuskarsa da yakanyi amfani dashi lokaci lokaci ya zare a hankali tare da qoqarin kau da idanunsa daga sashen da take tahowan,bawai don yana tunanin tana ganinsa ba,a'ah......daya daga cikin dressing na shaheeda tayi,dressing din da kusan zai iya cewa ita daya ce macen da yasan tana yinsa,kuma har yau shi dai bai sake ganin wata da irin shigar ba sai ita....bai sani ba,ko don idanun gaske dana zucin ma gaba daya tare da hankalinsa kacokam basa tare da kowacce mace?.

Shigar lafaya tayi blue black me adon gold a jiki,ko ba'a fadi ba kalar tana daya daga cikin kalolin dake haska farar fata ainun,rashin sabo da yanayin shigar ya sanyata take jin kamar zata harde,wannan ya sabbaba mata taku cikin nutsuwa da takatsantsan,abinda ya zame mata kamar ado,kamar wadda ke yin tafiyar da gayya da kuma wata manufa ta daban.

Dukka cikin sakannin da basu haura goma ba ya gama kallonta kafin ya zare idanunsa ya maida kan news paper din nasa,dai dai lokacin da ita kuma unaisa ta daga kanta da xummar gyara zamanta,idanuwanta sukayi kyakkyawan ganin da ya sanya tunaninta qwacewa na wasu daqiqu

"Damn it" ta fada can qasa,tana jin wani abu me qarfi yana fusgarta,kishinta ya soma huda zuciyarta yana ratsata da gasken gaske,bata iya dauke idanuwanta ba,har zuwa sanda ta iso dab da motar.

Batasan waye da waye a ciki ba,don haka tadanyi knocking kadan,drivern ya motsa da niyyar fita ya bude mata kamar yadda ya yiwa unaisa,sai ya cira kansa a hankali daga cikin news paper din

"Ummm ummm", ya fadi a taqaice,sai ya waiwayo ya kalleshi,yayi masa alama da ya zauna,a ladance ya amsa masa,ya ajjiye news paper din,sannan ya kama handle na motar ya bude,ya zuro qafarsa waje guda daya.

Kusan a tare suka hada idanu ita dashi,dukkansu cikin gaggawa kowa ya killace ganinsa,cikin dakakkiyar muryarsa ya magantu

"Bana iya zaman jiran kowa....wannan ya zama shine lokaci na qarshe da zaki aikata hakan" ya qarashe fada da muryar warning gamida da kausasa maganar tasa.

Sauka idanuwanta sukayi kan unaisa,wadda tadan rage glass din xuwa qasa kadan saboda ta samu damar jin a inda zasu fada,ita unaisar ke kallo,sai da suka hada idanu kuma sai ta tabe baki ta kuma janye idanun nata daga kansu ta mayar ga wayarta,a hankali maimunayu ta dauke idanunta daga wajen itama,tana jin yadda idanun nata suka cika da qwalla,cikin muryar nan tata dake cike da rauni....wadda ga wanda bai snata ba zai kira hakan da zallar shagwaba tace

"Kayi haquri" lafazin suka fita da sanyi da kuma zaqun muryarta,bashi ba,hatta da unaisa sai da salon da tayi maganar yaja hankalinta,ta sake maida idanunta kanta ba tare data shirya ba,tana jin kamar ta samu abu ta boye maimunatun,idanu su daina kaiwa zuwa gareta.

Sai daya lumshe idanunsa kana ya bude duka kusan lokaci guda,ya sake zube dubansa akan fuskarta,yana kallon yadda idaninta keta qyalli saboda ruwan hawauen da sukayi guzuri,yana mamakin saurin kukanta....me yasa ita din bata da tsayayyar zuciya,saurin bada haquri saurin kuka da kuma shagwaba kamar wata yayayya.

Qaramin tsakin da ita daya ta iya jinsa yaja yana maida jikinsa cikin motar

"Shiga mu tafi" ya fadi s gajarce,sai tasa hannu ta buda murfin motar ta kuma shiga bakinta dauke da sallama,driver ya amsa,yayin da da bakin J din yadan motss kadan alamun amsawa,ta fannin unaisa kowa ko uffan bata ce,can qasan ranta a mugun quntace.

Kaf maganganunta na jiya bata ga inda ta sanyo maimunatun a ciki ba,don me xa'a tafi da ita,ta maslahar aurenta ita daya kawai takeyi,bata qaunar ganin kowacce mace ta giftawa wannan buri da muradin nata.

Sosai qamshinta ya cika motar,har yaso yayi gogayya da nashi turaren,ya rufe news paper din a hankali ya ninketa gida biyu yana jan numfashi sosai wanda ya cika da qamshin nata,yana fesarwa kiran anni na shigowa wayarsa,ya dubi fuskan wayan bayan yayi kamar bazai dauka ba

"Am on my way" ya fada a taqaice,ya zame wayar daga kunnensa ya maidata inda ya dauko ya ajjiye,gefe daya na zuciyarsa yana cike da mamakin kiran meye haka anni ke masa da har ta qagu su iso,tabe bakinsa yayi,baisan da wacce rigimar zata zo masa yau ba,don bata rabo da rikici,amma koma dai meye...... he's ready akan duk wata rigima da takeji da ita,don yayi mata iya abinda zai iya,duk da ransa da zuciyarsa basa so.

[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 52

Fuskar anni kadaran kadaham sanda yake gaidata,duk da ba wani kallonta yayi can can ba,amma kuma jiki da zuciyarsa sun gaya masa lallai akwai wata a qasa,maida idanunsa yayi ga haj munubiya,matar da tun da can ba wani yi masa tayi ba,dama babu wani jituwa sosai a tsakaninsu,duk da ba wani abu bane yake shiga tsakaninsu ba,amma jininsu bai hadu ba.

Tata gaisuwar mai guda daya ya miqa mata,ta amshe da sauri tana cewa

"Lafiya qalau manya,ya ayyuka ya iyali?"

"Alhamdulillah" ya amsa mata a taqaice idanunsa akan qafafun anni dmda aka shafawa magani,ta kuma miqesu,da alama ciwonsu ya motsa

"To Allah ya taimaka,ya kuma dafa mana" bai maida hankali kan amsa addu'arta ta qarshe ba,cikin muryarsa me taushi da wani lokaci kan fito da wani amo da nauyi yace

"Anni,har yanzun duka tarin magungunan da kike amfani dasu basa aiki?" Dan duban qafar tayi kafin ta maida dubanta gareshi

"Abunne kasan dacewa ne,anata yi dai,sai sanda Allah ya dauke"

"Bare ciwo,kasan idan ya hadu da girma sai haquri" haj munubiya ta tsoma musu baki,ba tare da yabi ta maganarta ba ya zaro wayarsa,ya budeta,yayi kiran waya sannan ya sanya ta a kunne.

A hankali ya fara magana cikin yaren da maimunatu taji yana magana dazun,sai kuma yadan miqe a nutse yayi gaba dasu kadan can wajen dining din annin yana ci gaba da yin wayar,dai dai lokacin da khalid yayi sallama cikin falon.

Kan maimunatu idanunsa suka fara sauka,zuciyarsa tadan motsa,ya dan kafeta da idanu yana qarasowa cikin falon,sanye da qananun kaya,ya cusa hannunsa guda daya a aljihun jeans dinsa,daya hannun kuma riqe da key din motarsa yana dan kadawa

"Har ka dawo?" Haj munubiya ta fada,don ba haka taso ba,bataso dawowarsa a yanxun ba,saboda tana son fara aiwatar da shirinta,maganarta tasa ya dauke dubansa ga maimunatun zuwa kanta

"Eh,naji kince sauri kike ko?"

"Eh.....bawai wani sosai ba,dama abinda yasa nace kayi saurin kazo mu wuce,hafsat tacemin zata shiga makaranta,to kuma yanzun naga tex dinta ta fasa fitar,kuma na dan kwana biyu ai banzo gidan ba,ya kamata nadan zauna kadan mu gaisa sosai,don ko wajen yaaya marwan din ban shiga mun gaisa ba" anni dake sauraronta baki ta tabe tana kauda kanta gefe,a dan zuwan da take jifa jifa bata taba ganinta ta shiga sashen marwanun haka siddan ba,saida dalili,saboda haka kawai ta dorawa aishatu amma tsangwamar da babu dalili,face zallar faccalanci,amma yau abun mamaki wai ita ke zancan bata shiga sun gaisa ba,kafada ya daga yana maida kallonsa kan maimunatu kamar da ita suke maganar
Chapter 68 · 0% Book details