← Book details Gurbin Ido Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 113

Sashe 104

Gurbin Ido Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Naso ace ba'ayi taron bikinki ba diyam,taron aure nakeson muku na gani na fada,ku biyu kacal Allah ya bani mata a cikin jikokina,dukka maza ne,bugu da qari abubukar na musamman ne,yasha wuya ya gamu da jarrabawa,gashi a yau Allah ya yanke masa komai,aurensa da mahaifiyarki qaddara ce mai qarfi,ya boyemin batun auren saboda yana ganin kamar bazan amince ba,don a sannan matarsa nada tsohon cikin afra,bayan kuma an haife cikin sai ya kasa gayamin din,saboda ni da matarsa baisan wai yadda zamu dauki batun ba,a haka shekaru suka fara turawa har zuwa sanda Allah yayi nufinsa ya gayan,nayi masa fada sosai naji kuma.babu dadi,sannan na gaya masa a sannan ne matarsa zatafi ji ciwon abun,za kuma tace ya munafunceta,har gwara farko farkon abun,na masa umarni da yaje yazomin da ku,ya tafi zai taho daku sai kuma aka kirashi hauwa'u matarsa mahaifiyar afra ba lafiya,sai ya yanke ya taho shi kadai idan ta samu sauqi ya dawo ya daukeku ayi mai gaba daya,ashe ba rabon abun zai ritsa daku,ya samu mummunan hadarin daya kawo masa wannan matsalar,yana cikin jinyar kuma itama hauwa'u ta rasu,duk da na shaida mata komai,tace kuma ta yafe masa,ta shaidi halinsa,ba haka yake ba,ta tabbata qaddararsu ce tazo a haka,sannan idan ta dawo Allah yayi zamanmu tare ta riqe mata afrah da musaddiq,to ashe itama Allah bai nufi ganawarmu ba" shuru maimunatu tayi tana share qwalla,tun faruwar abun kawo yau ba ranar da bazataji wani abu daya motsa ranta ba.

A daren abbuu ma ya kirata,sun jima suna hira,bayan sun gama ne ya dauko wasu files da takardu a ciki ya miqa mata

"Akwai haqqoqinki a wuyana masu tarin yawa da ban samu damar sauke miki su ba,hakanan akwai alqawura da na yiwa mahaifiyarki saboda kyautatawarta gareni da haqurin zama dani da tayi,wannan takardun wani estate dina ne dake new GRA road,na mallaka miki su halak malak,sauran 'yan uwanki dukkansu suna da kadara kwantankwacin taki" kamar a mafarki takejin abun,estate guda.abbun nata ya bata?,koda ta duqa zata masa godiya dagata yayi

"Ban biya shatu da komai ba akan soyayyar data nuna min,fatana kawai Allah ya hadamu a aljanna,ya sake tabbatar dani da ita a matsayin miji da mata"

Cikon kwana na uku ja'afar yazo da niyyar daukarta,amma saita mararaice masa,tana son binsa amma kuma tana buqatar lokaci sosai ita da abbunta,ga umma sa'adah ma tanata qorafin har yau basu zauna ba.

Da farko yaqi,amma da hajja ta saka bakin kan ya qara mata ko kwana uku ne sai ya tafi ba tare da yace komai ba,saidai ita maimunatun ta cikin idanunsa ta karanci bawai ya haqura din bane.

Cikin dare ta dinga jin zazzabi ta cikin qashinta,ta dinga juyi saman gadon,tana jin wata azababbiyar kewarsa,ta saba duk sanda take zazzabi irin haka cikin jikinsa yake boyeta,ba zata dauki dogon lokaci ba zazzabin yake rabuwa da ita,to amma yau din saboda babu shi a kusa da ita,sai takejinta kamar tsirara babu tufafi a jikinta.

Tun goma na dare da suka gama hira da abbu da hajja harda afra da musaddiq take kwance amma sha biyu saura idanunta a soye suke,hakan ce ta faru ga ja'afar,ya shiga ya fita tsakanin bedroom dinsa zuwa parlor ya kusa sau uku,ana hudun sai yayi zaune saman kujerar falon nasa,ya miqe qafarsa saman glass center table dinsa,ya dauki wayarsa ya fara laluben number dinta.

Cikin jikinsa yakejin idanuwanta biyu itama batayi barci ba,hasahensa ya tabbata kuwa,don ringing biyu tayi ta daga,nannauyar ajiyar zuciya ya sauke wadda ta ratsa har cikin kunnuwanta,saita damqe filon da take kwance akai da kyau saboda yadda tsigar jikinta ta zuba,shuru ya ratsa tsakani,dukkaninsu aka rasa wanda zai fara yin magana

"Lafiyar ki qalau kuwa?" Narke fuska tayi kamar yana gabanta sai tace

"Ummmmm" cikin shakku ya sake magana da wata murya mai taushi da dadin sauraro

"Me kikeyi har yanzu bakiyi bacci ba?" Kamar jira take ya tambaya kawai sai taji kuka ya tsinke mata da 'yar sheshsheqa har ta cikin wayar

"Ya salam" ya fada yana sauke qafafuwansa qasa gami zama sosai

"Please my angel,please" ya furta a hankali yana rufe idanunsan

"Zuciyata na qara yawan gudunta,stop it please,ki gayamin menene?" Maimakon tayi magana sai wani kukan ya kuma qaruwa,haka kawai batajin dadin dukka jikinta,kuma ranta tana jinsa aquntace.

Shuru yayi tsahon minti guda yana sauraron kukanta,sai kuma a hankali yace

"Ok,am on my way" ya kashe wayar,yana miqewa cikin kuzari yayi bedroom dinsa.

Wayar ta zare daga kunnenta tana son tuna abinda yace

"Am on my way fa?,yana nufin gidan zai taho a wannan tsohon daren?,ta sani indai ja'afar ne zai aikata,don haka saita shiga kiransa da sauri don ta dakatar dashi kada ya biyo hanya a wannan tsohon daren.
[11/25, 12:59 PM] Safiyyatulkiram: 82

Yana gaban closet dinsa yana sauya kaya yaga shigowar kiran nata a jejjere,da kamar bazai dauka ba saboda saurin da yakeyi,amma sai ya daga ya sanyata a hands free yana saurarenta,da narkakkiyar muryarta cike da sautin kuka tace

"Don Allah kada ka biyo hanya yanzu"

"Why?"ya tambayeta kai tsaye yana fesa turare a jikinsa

"Dare"

"Bana tsoronsa,nafi tsoron nisantarki akan dukkan wani abun tsoro,so get ready,i will call you idan na iso,ki zauna kusa da wayarki" daga haka ya katse kiran,ya dauki key din qaramar motarsa cikin motocinsa ya sanyama kansa wata hula ya fito.

Samun kanta tayi da zama daram tsakiyar gadon, idanunta nakan afrah dake bacci can nesa kadan da ita,da yake gadon yana da girma sosai,kamar wata me dakon jiran nasa haka ta dinga duba agogo,wasa.....gaske saiga kiransa bayan minti talatin,ta tsorata sosai da taji wai har ya iso,wanne irin gudu ya sharara haka?,saita miqe a hankali tana yaye window din dakin nata

"Ki fito ko na shigo" taji ya fada a tausashe,tadan tsorata kadan amma sai ya zura hannu ta window din ya riqe mata hannu yana kallon qwayar idanunta ta cikin hasken daya gauraye harabar gidan gami da zare hular kansa,mamaki ya kusa kasheta,duk security din gidan amma ta ina ya iya shigowa da daren nan?,kallon da yayi mata kadai yasa taji duk duniya bata buqatar kowa sai shi,sai ta zame hannunta sannan ta juya a hankali ta bude dakin ta fice,bata ko sauya kayan baccin jikinta ba,duk da akwai baby hijab a jikinta.

Tana riqe a hannunsa kamar zata bace har suka isa qofar gidan,sai a sannan ta lura da guard daya ne ya taso ya bude masa gidan,to ya akayi yasan da zuwansa?,wannan kuma bata sani ba,har ya bude mata motar ta shige ya shigo ya tayar suka bar layin tana kallonsa cikin mamaki

"Yanzu inda wani abu ya cutarmin da kai fa?" Ta fada da wata irin murya data sanyashi waiwayo wa ya kalleta,wani irin kallo take jifarsa dashi mai tsuma zuciya data sanyashi dan dukan sitiyarin motar softly

"Ba abinda zai cutar dani in sha Allah,bana jin komai inda zan kasance dake,ko meye zai biyo baya mai sauqi ne" sai ya miqa mata hannunsa ta sanya nata a ciki,ya hada ya matse gam

"Don Allah karki sake yarda kije ko ina ki barni....kiyimin alqawari" a tausashe ta gyada masa kai

"Nayi maka" cikin jikinsa ya dauketa tun daga harabar gidan zuwa cikin gidan,yana kallon fuskarta kamar ya riqo jaririya

"Jikinki babu qwari moon,banjin kina da cikakkiyar lafiya" ta bude bakinta zata amsa mishi wani amai me zafi ya taso mata,saita zille daga jikinsa da sauri ta dire ta sheqa zuwa toilet dinsa,baiyi qasa a gwiwa ba yabi bayanta,saidai garin rufewa ta kulle bandakin gaba daya,haka yayi tsaye gaban toilet din yana kiran sunanta.

Dukka abincin da taci sai daya dawo mata,sai data gama ta kuskure bakinta sannan ta fito tana takawa da qyar,riqeta yayi sosai ya samu waje nan qasan carfet ya zaunar da ita

"Na fada baki da lafiya daman,me yake damunki angel,menene?" Kamar tambayarsa na zuwa da amai,sake yunqurin tashi tayi don kada ta bata kyakkyawar farar jallabiyyar jikinsa amma sai ya riqeta gam,bata sa sauran zabi illa kwararar dashi a nan,ta dinga sheqashi kuwa,sai data wankesu tas ita dashi.

Sosai hankalinsa ya tashi,don a daren tayi amai ya kusa sau hudu,kafin gari ya qara haske ta galabaita sosai,qarfe shida na safiya ba tare daya damu da lokaci ba ya dannawa dr noor kira.

A sannan tanata shiri da sauri sauri akwai emergency C.S da zatayi,already tasan waye ke kiran,don haka ta daga kiran,yayi mata bayani gami da neman tazo ta dubata

"Karka damu,zan iso yanzu in sha Allah".

Cikin mamakin yadda captain ja'afar ya koma gaba daya kalan tausayi take duba maimunatu,PT test tayi mata,saita daga kai da murmushi tana kallonsa,tunda ta shigo yake tsaye ya kasa zama,ya kafe maimunatu da ido kawai kamar zata bace,J mai tsauri da kaushi marason wasa amma gaba daya yayi laushi saboda ciwon matarsa,wacce irin soyayya ce wannan mai ban mamaki?,wadda sun fidda rai zai sake ma wata mace irinta

"Congratulations captain,zaka sake zama uba again in sha Allah" idanu ya zubewa dr noor,gani yake kaman tana masa wasa ne ko kunnuwansa basuji da kyau ba

"Really?" Kai ta jinjina masa tana tattare jakarta

"Da gaske nake,abu daya ya rage ka kawota nayi mata scanning don na tabbatar da lafiyar komai,watanninsa da kuma expected date of delivery dinta"

"Allahumma salli ala sayyadina muhammadin wasallim" ya fada da wani irin amo mai qarfi yana rufe idanunsan,sannan ya dora

"Alhamdulillah alhamdulillah" har kamar bazai daina fada ba sannan ya dubi dr noor

"Ki duba parking lot na gidan nan,duk motar data yi miki ki turo gobe a daukar miki ita,wannan shine tukuicinki".

Sosai farinciki ya kama dr noor,dama qarshen satin nan take sanya ran sauya mota,sai kuma ga dama ta samu,godiya tayi masa sosai sannan ta juya ta fita.

Zamewa yayi a hankali zuwa qasa yayi sujudush shukur,sannan ya rarrafa zuwa gaban gadon maimunatu dake kwance,wadda tuni bacci yayi awon gaba da ita,hannu yasa yana shafar gefan fuskarta a hankali,wasu qwalla suna tarar masa a ido,ashe ita din ba gurbin ido bace,ashe ido ce guda,sai yanzu idanun suka samu gareshi,ita alkhairi ne masu tarin yawa tattare da ita,rasa me zaiyi mata yayi,kawai sai ya fara kissing duk inda bakinsa yakai very softly yadda bazai tasheta ba yana fadin alhmdlh.
Chapter 104 · 0% Book details