← Book details Gurbin Ido Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 113

Sashe 31

Gurbin Ido Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aiba baiwa bace ce,'ya ce ke kamar kowa,don haka ya zama dole a nema daga wajenki cikin baki cikakken 'yancin yin zabin eh ko a'ah,kije kiyi tunani maimunatu,na baki dama,idan har kikaji baki gamsu ba,ko ba zaki iya wannan alfarmar ba,kada kiji komai,ki gayamin kanki tsaye,ni kuma nayi miki alqawari har tsakanina da ubangiji na,zamu ci gaba da riqonki ba tare da komai ya sauya ba.....tashi kije" kasa cewa komai tayi,ta miqe cikin wani irin yanayi data gaza fassarashi,kamar anbi kowacce gaba ta jikinta an zare sinadarin dake bata kuzari,komai na jikinta yayi sanyi qalau,maimakon ta wuce study room ko kitchen kamar yadda ta tsara yi,saita wuce dakinta kawai,ta tura qofa ta kuma haye gado.

Inda batasan wace anni ba da sai tace wasa take mata,ja'afar dai da takejin sunansa a bakunan al'umar gidan nan?,koda batasan fuskarsa ba amma mutum ne da kowa ke ganin girma da kimarsa,kamar ita?maimunatu?,bafullatanar ruga 'yar qauye?,ta yaya zatayi kan kan kan da mutumin da take da tabbacin a yanzu ma baya qasar nijeria?,ta yaya zata iya wanke wannan babban tabon daya nannade rayuwarsa?,kai tana ganin a rayuwar gida irin ta dr marwan,koda drivern gidansu darajane dashi,koda drivern gidan ya fita daban da sauran drebobi,koda shi aka ce ya aureta tana ganin kamar ya zarce mata,bare ace dan gida,dan gidan ma irin ja'afar dan gata ta kowacce fuska,anya kuwa zata iya?,idan ba zata iya din ba kuma zata iya kallon anni tace mata A'AH?,.....kalmar tayi nauyi da kuma muni da yawa,anni mutum ce guda har da rabi,wadda 'yantata ta kuma maidata cikakkiyar mutum.

Ire iren wadan nan tunanukan su sukaci gaba da kassara maimunatu,suka kuma cika mata kwanya taf,ta rasa yadda zata sarrafasu su dace da hange da kuma fikirarta.

Ajiyar zuciya anni ta sauke bayan fitar maimunatu,fatanta daya komai ya daidaita,komai yazo da sauqi,don muddin maimunatu ta amince,to fa babu daga qafar da zata yiwa ja'afar har sai ta tabbatar komai ya kammala,wannan shine buri da kuma fatarta.

Wannan magana da sukayi da anni sai ta zamewa maimunatu kamar wani dabaibayi,dukka kuzari karsashi da walwalarta suka yi qaura sosai,duk da dama ita din miskila ce,wadda bata damu da hira ko hayaniya ba,tafi ganewa karatu,to shima karatun a dan tsukin nema yake ya gagareta,idan ta buda littafin sai ta tafi duniyar tunani,sai ta kasa qulla komai har ta gama zamanta ta tashi.

A wani yammaci ne,tana dakin karatun dauke da qur'aninta tana tilawa,saidai can tsakiyar karatun nata tunanin da ya zame mata jiki ya kutso mata kai,sai taci gaba da riqon qur'anin kawai ba tare data iya ci gaba da karatun ba.

A wannan lokacin baba tabawa ta shigo dakin,hannunta dauke da cup data cikashi da kunun gyada fari sol sai maiqo da qamshi gyada da yakeyi,daya daga cikin cimar da maimunatun keso kenan,tayi firgigit tana amsa sallamar baaba tabawa.gami da gyara riqon alqur'aninta,sai baba tabawan ta sakar mata murmushi tana miqa mata cup din,sannan ta zauna saman kujerar dake fuskantar maimunatu

"Na lura kwana biyu kin zama wata aba,don wannan kunun qilan saidao a zubda ba tare da kinzo kin dauka ba" dan murmushi tayi tana juya spoon din dake cikin kunun,cikin ranta tana ayyana yadda mutanen birni ke kashewa ciki kudi,suci wannan suci wancan

"Shawara nazo baki muna,don banaso kiyi asara har irin wannan a rayuwarki" daga kai maimunatu tayi ta dubeta cikin rashin fahimta,idanun baba tabawa cikin nata ta gyada kai tana tabbatar mata da duk abinda zata ji

"Maimunatu,tun zuwanki gidan nan naji kin kwantain,ina kuma qaunarki,maimunatu,naji na kuma san abinda ya sanyaki kika canza gaba daya,ba zancan ja'afar ba?" Tayi zancan da sigar tambaya,saita sad dakai,wato kowa ya sani kenan?,ya kuma fahimta?.

"Duk yadda zakiyi kada ki bari ja'afar ya subuce miki,duk yadda zakiyi kada ki soma wauta ko gangancin cewa baki sonshi,ja'afar yana cikin dai daikun mazan dake da wuyar samu duk da wahalar sha'aninsu,samunsa kuma sai mace mai matuqar sa'a kuma 'yar baiwa,bawai don yana da kyau da kudi ba,a'ah.....yana da wata irin nagarta da kuma kebantattun kyawawan halayen da ba kowa bane ya sansu,ba shakka kowacce mace da tasan abinda takeyi zata yiwa wadda take so ko qauna fatan kasancewa da shi a mazaunin miji.....maimunatu,a shawarce.....ki aminta da maganar hajiya anni,ina mai baki tabbacin ja'afar gaba yake da nagartaccen miji idan ma akwai" shuru maimunatu tayi tana jujjuya maganganun tabawa cikin zuciyarta,tana ganin matsayinta baikai inda anni keson kaita ba sam

"Akwai abinda kike tsoro ne?" Tabawa ta tambayeta kai tsaye,a wannan karon batayi nauyin baki ba

"Bansan waye ubana ba,bafullatanar ruga nake,har na isa na hada kafada da zuri'ar anni?" Murmushi tabawa tayi

"Zallar karamci irin na hajiya anni babu abinda ba zaki gani ba,sa'annan ke din halastacciyar 'ya ce,babu abinda ya nuna baki da.uba ne,ke koda haka ne,ina me tabbatar miki tunda hajiya anni tayu niyyar aiwatar da hakan,babu abinda zai dakatar da ita,ba kowanne mutum ke ganin baiwar da Allah yayi masa ba,kamar ke din,kina da wasu kebantatattun halaye da siffofi dani kaina nake saka ran akwai alkhairi me yawa a tare dake" shuru maimunatu ta sakeyi,tambayar qarshe kuma wadda take ta cin ranta

"Shi ya santa ne?,yana kuma sonta" maganar data fito sarari,sai murmushi kawai taga tabawa tayi

"Muna.....ke din ta musamman ce,hakazalika kina da tarin baiwar da namiji bai isa ya kalleki yace baiso ba,saidai idan wani abun daban kuma ba wannan ba" tabawa tayi matuqar sanyata cikin nazari,tana jin kokwanto tana kuma jin qwarin gwiwa,wanne zata rinjayar?.

"Anni ta damu qwarai,kin amince a shaida mata ko zata samu nutsuwa"
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 22

Bata da wani sauran zabi,sai ta samu kanta da gyadawa tabawa kai.

Unexpected wata guda ta ratsa kunnuwa zuwa kwanyar maimunatu,ta rintse idanunta tana jin wani abu na mata yawo,wanda yake cakude da zallar fargaba da kuma kokwanto.

"Alhmdlh alhmdlh alhmdlh" shine abinda anni ta dinga maimatawa fuskarta kamar wata dam daren sha hudu,bakinta yagaza rufuwa,hakanan Allah ya sanya mata qaunar maimunatu da kuma tausayinta a ranta.

A haka maimunatu taci gaba da rayuwa,cikin kunya nauyi da kuma fargabar al'amarin dake tunkararta,saidai kuma ta sake maida hankalinta ga karatunta,wanda a yanzu ta sake maida hankalinta dari bisa dari a kai,ranta da zuciyarta na gaya mata idan tayi aure shikenan,ta rabu da karatunta,tunda abinda ta taso kenan ta gani,matan aure kowacce tana gidanta a zaune,zuwa makaranta na 'yammata ne.

Saidai a kullum tana tambayar kanta ta yaya lamarin yazo kamar mafarki?,yaya kuma zaici gaba da kasancewa?.

**********Duk yadda yaso ya taushi zuciyarsa ya taho nigeria abun ya faskara,haka kawai yakejin baison zuwa din ko kadan,akwao memories masu tarin yawa da ya binne wanda baison tunosu,ko sau daya zuciyarsa bata sassauta daga tunani da kuma kewar shaheeda ba,wanda cikin jikinsa yakejin da wannan ciwon zai qarasa rayuwarsa ya kuma mutu shima,mutuwar da inda zabi take bayarwa shi zaice ta dauka ba shaheeda ba,koda kuwa ta dauketa zai zabi ya bita shima.

Duk wata hanya da jabiru yake jin zaibi ya shawo kan ja'afar abun ya faskara,hakanan itama annin tabi duk hanyar da ya kamata ta lallashi amma abinda take son bai samu ba,ranta ya fara baci,don haka a wani dare ta nema ganin dr marwan

*_08:pm Dr marwan khalid akko residence_*

Dr marwan ne zaune gaban anni,sanye da wata jallabiyya ta matsa ruwan hanta saqar qasar oman mai budadden hannu,an qawata gabanta da adon zare ruwan madara mai turuwa kadan,fuskarsa na dauke da wani annuri na zallar nutsuwa ilimi gami da samun cikakken hutu da kwanciyar hankali,yana da cikar haiba kwarjini da kuma kamala sosai a fuskar tasa da wani bangare nata ya fara samar da furfura.

Ya miqa hankalinsa matuqa zuwa ga mahaifiyarsa

"Kaji duka irin abubuwan dake faruwa,banyi tsammanin abun na ja'afar yakai har can ba,ina ganin ya kusa fin qarfinmu dai" da hanzari dr marwan ya girgixa kai

"Kiyi haquri ki daina fadin haka,bai isa ba wallahi,koda bana raye koda aishatu bata raye,bare gaba dayanmu da ranmu.....bai isa ba don ubansa,banda wancan matsalar ma harda iya shege na fuskanta ciki lamarin nasa,ai mu muka haifeshi bashi ne ya haifemu ba,ya zubda komai da kowa nasa saboda mutuwar matarsa da diyarsa kawai?,zan nuna masa mu muka haifeshi kam tabbas,karki sake bi ta kansa anni don Allah,abinda za'ayi shine.....ki shirya ki kuma saka lokaci zuwa adamawa gurin magabatan maimunatu cikin satin nan,ni kuma zanyi magana da honorable commissioner ya tsaida randa za'a kai kudin auren tasa diyar" hakan ya yiwa anni dadi qwarai da gaske,ta dinga sanyawa dr marwan albarka,yana da tsananin biyayya,abinda yasa a kullum yake sake shiga ranta.

Shiri ta fara yi gadan gadan na tafiyarsu adamawa,sanda ta shaidawa maimunatu wani dadi taji ya tsarga mata,amma kuma wani sashe na zuciyarta sai taji tana tsoro da fargabar wacce tarba zata samu daga wajen innar laulo dama gaaje?,dama kuma bata da wata fargaba akan jauro,duk inda mutumin kirki yakai yakai nan.

Saura kwanaki biyu su wuce da wani yammaci anni ta kirata,tace taje aishatu tace a turota ta kama mata aiki,haqiqa tana matuqar jin kunya da nauyin matar,tunda tasan itace mahaifiyar ja'afar,duk da cewa wata magana data shafeshi bata taba hadasu ba.

Atamfa ce a jikinta doguwar riga,sai ta zura hijab din da bata jima da cireshi daga jikinta ba saboda sallar data idar,ta zura wasu slippers dinta ta nufi sashen amma,tana tafiya a hankali tana shaqar iskar yammacin,duk bata jin dadin gidan saboda dauke amna da dangin mamanta sukayi,sun roqi alfarmar a basu ita akwai bikin da ya taso zasuyi can dangin mahaifiyar shahidan,dr yace a basu.

Gab da zata shiga sassan ta gamu da ammi,kishiyar amma tana fitowa ita da khadim,bisa dukkan alamu unguwa zata je

Cikin girmamawa ta gaidata,tadan tsokani khadim kadan sannan tayi musu a dawo lafiya ta wuce ciki.

Masu aikinta biyu ta samu a falon suna kai kawo,kowa da abinda yakeyi,ta gaidasu kamad yadda ta saba,daya daga cikinsu tace

"Tana kitchen" saita miqe zuwa hanyar da zata sadata da kitchen din.

Kamar kowanne lokaci,a duk sanda maimunatun tayi magana ko tayi sallama sai taji kamar tasan muryar,yau ma da sauri ta juyo,sai taga maimunatun ce,ta sakar mata murmushi tana fadin
Chapter 31 · 0% Book details