← Book details Gobe Da Nisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 18

Sashe 9

Gobe Da Nisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kafin next week ina buƙatar ɗaya. You can go." Ya faɗa yana miƙewa, ya buɗe wani ƙofa alamar bathroom ne ya shige ya barta tsaye.
Da ƙyar Mariya taja ƙafafuwanta tabar office ɗin, da tunanin ta ya za ta saka suit haka ta ƙarasa office ɗinsu, sai taga yau duk matan ma suit suka saka da baby hijab saɓanin ita da baƙin Abaya ne a jikinta.
Tasan hakan dokar aiki ne dole ta saka, kuma sun musu uzurin sati guda suna saka Abaya.
Zama tayi tana dafe kanta, ta ɗauki sakwanni a haka kafin ta buɗe computer ta fara ganin aikin da ya bata wanda yake neman ɗaya. Dole na Isah Hamza ta cigaba da dubawa don shi ne ta fara taɓawa.
Ranar kamar kullum haka ta wuni a wajen aiki, ƙarfe huɗu suka tashi yau. Bayan ta fita ta tari napep sawa tayi ya kaita station inda Isah Hamza yake. Yau ma kamar ranar tambayoyi ta mishi, anan ta ƙara samun wasu amsashin har ya faɗa mata sunan unguwarsu da gidansu ko za taje ta musu tambayoyi.
Godiya ta mishi kafin ta fito, napep ta sake tara tasa ya kaita mall. Bayan ta sauƙa ta biya shi ta shiga ciki, wajen siyar da kaya ta shiga ta fara duba suit masu kyau na mata sai dai da tsada.
Rasa abin yi ta yi dole taja gefe ta tsaya, ta ciro wayarta a handbag ɗinta ta ƙira Umma. Ya yi ringing sosai kafin ta ji ta ɗauka.
Mariya ta gaishe da ita tana ƙarawa da faɗin. "Umma kuɗi nake so zan siya abu."

Daga ɓangaren Umma ta tambayeta."Nawa?"

Mariya jikin kayan ta duba ta ga daga na dubu goma sha sai ashirin, tasan da ƙyar ta samu. Amma ba ta karaya ba ta ce.
"Umma ko dubu hamsin haka."

"Anya akwai har dubu hamsin. Ga Abbanku." Ta ji Umma ta faɗa, kafin ta faɗi wani abu ta ji ta ba wa Abba wayar.
Muryarsa ne ya daki dodon kunnenta, ta runtse idanuwanta ta buɗe lokacin da ta ji yana faɗin.
"Ni me nayi ba za a tambaye ni ba Mamarmu."

"Babu komai." Mariya ta faɗa ƙasa ƙasa.
Tana jin sautin murmushin Abba da ya yi, sannan ya ce. "Turo min account number naki."

  Ba ta iya faɗin komai ba ta zare ta kashe, ƙin tura masa account ɗinta ta yi ta fara ƙoƙarin barin wajen, alamar shigowar saƙo yasa ta dakata ta duba wayarta, alert na kuɗi ne daga Abba na dubu ɗari.
  Sai da zuciyarta ta buga, ta fita a wajen ta laliɓo lambarsa ta fara rubutu saƙo, har ta gama zata tura sai kuma ta fasa ta goge ta fita, ta kashe wayar ta jefa a jaka.
Buƙatar kayan da take yasa za tayi amfani da kuɗinsa, idan ba haka ba.
Haka ta koma ta zaɓi kayan kala goma masu kyau, ta nufi wajen biya suka cajeta dubu ɗari har da canji. Atm ɗinta ta basu suka cire sannan suka saka mata a leda, ta karɓa ta fito ta tafi. Napep ta shiga ya sauƙeta har ƙofar gida, ta sauƙa ta biyashi ta shiga gida.
  Kamar yadda ta yi tsammani haka ta tarar motar Abba, hakan yasa ta sauƙe numfashi ta nufi falon Umma ta shiga da sallama.
Dukkan su suka amsa mata, ta ƙarasa ciki tana gaishe su, Umma ta amsa tana faɗin.
"Me ki ka siya haka?"

"Kayan sawa ne na aikinmu." Mariya ta faɗa tana wucewa ɗakin su kafin ma wani ya tsayarta ya ce zai hargitsa.
Tana shiga ta cire kayanta ta jera a wardrobe ɗinta, ta rage kayan jikinta ta wuce bathroom. Ruwa ta watsa ta ɗaura alwala ta fito, ta gabatarwa da sallar la'asar.
Anan ɗaki ta zauna har aka ƙira magriba tayi sannan ta miƙe ta fita don yunwar da take ji.
Yaran duk suna falo, banda Umma da dukkan alamu tana ɓangaren Abba, da kuma Haneefa da take wajen aiki. Dining table ta nufa ta zuba abinci ta zauna ta ci, bayan ta gama ci ta ɗauki ruwa ta miƙa ta ɗauke plate ɗin da ta ci, takai kitchen ta fito ta wuce ɗakin su.
Mariya ba ta fita ba har dare yayi ta gabatar da sallar isha'i, ta yi shirin bacci ta kwanta. Har Ummi Aisha ta shigo ta kwanta ba ta sani ba.
...

Washegari

  Cikin farin ciki Abba da Umma suka farka na murnar abin farin cikin da ya riske su daren jiya. Ga yaran kuwa wasu sunyi murna saɓanin wasu da suka ji kamar su fito fili su nuna baƙin cikin su.
Musamman Mariya da ba ta shirya hakan yanzu ba, taso sai burinta ya cika nan da shekara ɗaya kamar yadda tsara kafin nan.
Hakan yasa ko takan hirar da ake ba tabi ba ta shirya ta fice a gidan cike da tsoro da kuma taƙaici, sai dai babu wanda ya lura da yanayinta kasancewar fuskarta ba kullum take kasancewa da fara'a ba.

#vote
#comment
[06/06, 7:28 pm] Pharty BB: GOBE DA NISA
Page 7
Na Pharty BB

Manyan idanuwanta ta ɗago ta kalle shi da sauri, ta ga shi ma ita yake kallo da murmushi ɗauke saman fuskarsa, babu shiri ta kawar idanuwanta don yadda ya haddasa mata ci gaba da bugun zuciya bayan wanda take ciki.
Mariya jiki na mugun rawa ta miƙe, ta ɗauki plate ɗaya ta buɗe flask ta zubawa Abba ta ajiye a gabansa. Haka ta jawo wani ta zubawa Umma ta ajiye mata, ta ɗauki wani za ta zubawa Yaya Haydar ta ji muryarsa yana faɗin.
"Haɗa min tea."

  Bari ta yi ta ɗauki cup ta hau haɗa mishi daidai yadda yake so, bayan ta gama ta ajiye mishi a gabansa. Ita ma black tea ta zuba ta zauna, ta ɗauki teaspoon tana juyawa don ba ta da ƙarfi ko nutsuwar cin abinci a gaban mutane biyun. Haka sauran yaranma da ƙyar suka zuba suka hau tsakura.
Abba ya kalleta yana murmushi ya ce. "Na fa kula ba kya son cin abinci yarinyar nan."

  "Faɗa mata dai."
Umma ta faɗa ita ma. Kowa dai ya yi gum da bakinsa ganin dodon nasu yana nan.
  Mariya ganin suna shirin kafa chapter nata yasa ta miƙe, ta ɗauki handbag ɗinta tana faɗin.
"Sai anjimanku."

"Tsaya ku tafi da Yayanku, shi ma wajen aikinsa zai fara fita yau."
Abba ya faɗa yana mayar kallonsa kan Yaya Haydar da ya ƙara haɗa fuska sosai.
  Girgiza kai Mariya ta yi cikin tsoro, haɗa tafiya da Yaya Haydar gani take zai sumar da ita ko ya jefarta a motar. Da ƙyar ta buɗe baki za tayi magana taji maganarsa ya ce.
"Abba sai anjima."

  Daga haka ya bar wajen, cikin sanyin jiki Mariya tabi bayansa. A waje ta hangosa cikin motarsa an buɗe mishi get, tana ƙoƙarin ƙarasawa kusa da shi ta ga yaja motarsa ya fice. Ko kaɗan ba taji haushi ba sai ma farin ciki da taji na ganin ya tafi ya barta.
  Haka ta fito ta tari napep ta nufi office, bayan ta isa ba ta iya shiga office ba sai da ta shiga wajen sayar da snack ta saya da drinks, sannan ta wuce office ta zauna taci kafin ta fara aikinta.
  Sallama suka ji daga bakin ƙofar, gaba ɗayan su suka ɗago har Mariya jin tasan muryar. Da Nabeela suka haɗa ido, tana mata murmushi ta ƙaraso table ɗinta taja kujera ta zauna. "Sannunki da aiki."

  Babu yabo ba fallasa Mariya ta amsa mata, hakan ya ƙara burge Nabeela tana jinjinawa ajin yarinyar.
Cikin murmushi ta sake faɗin.
"Kin san menene? Tun da muka rabu nake tunaninki, haka kawai kike burge ni."

  Sai lokacin Mariya ta saki murmushi mai sanyi, ta kalli Nabeela da ta kura mata idonta irin na Barrister Waliy sosai.

"Na gode sosai." Ta faɗa tana sunkuyar kanta ta ci gaba da abin da take yi.
Nabeela wayarta ta ciro, ta ajiye a gaban Mariya tana faɗin.
"Saka min lambarki muna waya, na zo jin wata shari'a ce na samu an ɗaga shi ne nace bari na ƙaraso mu gaisa."

'Naga ta kaina.' Faɗin Mariya a zuciyarta, a fili ta murmusa ta ɗauki wayar Nabeela ta saka mata lambarta ta miƙa mata wayar.
  Karɓa Nabeela tayi ta ce. "Sunan kawar tawa. Ni sunana Nabeela Abubakar ƙanwa ga Barrister Waliy Abubakar. "

"Mariya Harun."
  Faɗin Mariya domin ta gano ƙanwarsa ce duba da ranar da kuma kammanin su.
  Miƙewa Nabeela ta yi tana faɗin.
"Sai mun yi waya, bara na tafi kar Yaya ya ƙira gida ya ji ban isa ba nayi laifi."

  Murmushin ƙarfin hali Mariya ta yi tana faɗin. "Allah ya tsare."

   Nabeela ta amsa da amin ta fice cikin farin ciki ganin plan nasu ya fara tafiya cikin shiri.
  Bayan fitar su Mariya ta ci gaba da yin aikinta, ba ta damu da ƴan wajen da suka fara maganganun ƙasa ƙasa ba.
  Ita damuwar da take ciki ya linka shekarunta, gaba ɗaya ta rasa mafita a abin da take son cimmawa kafin lokaci ya ƙure mata, dole ta aiwatar da komai cikin sauri kuma tana neman taimako.
Sai dai na waye? Wa zai taimaka mata? Tsawon shekaru ta rasa wa zata tunkara shi yasa ta ka sa cika burinta.
Barin abin da take yi ta yi ta dafe kanta, a hankali ta furta. "Allah ka cika min burina."
...
Chapter 9 · 0% Book details