Sashe 2
Gobe Da Nisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Murmushi Mariya ta yi har dimple ɗinta suka lotsa, wanda ko ya ya tayi da fuskarta sai sun lotsa tsabar yadda suke da saurin shigewa. Ta duka tana faɗin.
"Ina wuni Umma?" Ta juya gefen Abba da shima sanyayyar murmushi yake binta da shi ta ce.
"Abba ina wuni."
Gaba ɗayansu suka amsa mata cikin kulawa da tambayarta aiki.
Cikin sanyinta ta ce
"Allahamdulillahi." Sannan ta miƙe ta wuce ɗakinsu.
Kwance ta samu Ummi Aisha, kasancewar ta yi sallar la'asar saman gadon ta zube ƙafafunta suna reto a ƙasa, cikin makoshi ta furta.
"Wash! Na gaji."
Ummi Aisha ta gyara kwanciyarta tana kallonta ta ce.
"Manya Barrister, sannu da ƙoƙari."
Da ƙyar Mariya ta ce. "Yawwa."
Ta miƙe tana cire baby hijab ɗinta ta ce."Aiki ko wahala."
"Ke kika sa kanki aikin maza. Bar ni da baking ɗina hankali kwance."
Faɗin Ummi Aisha tana dariya ta sauƙa a kan gadon.
Mariya leɓbenta ta cije ba ta mata magana, bayan ta rage kayan jikinta ta miƙe ta shiga bathroom. Ruwa ta watsa ta fito ta saka doguwar riga na shan iska, ta saka ƙaramin hijab iya guiwarta sannan ta fita.
Yadda ta barsu haka ta dawo ta samesu sai ma ƙarin Ummi Aisha da ta hango a dining, can ta nufa ta ja kujera ta zauna, ta buɗe warmers din saman dining ta ga akwai ragowar abinci. Plate ta ɗauka ta zuba sannan ta zauna ta hau ci ganin Ummi Aisha tana tare da ita.
Sosai ta ci ta kwara da ruwa kafin ta miƙe, ta kai plate din kitchen ta fita, bata tsaya a falon ba ta wuce ɗakin su ta ɗauki wayarta ta kwanta. Haneefa ta ƙira ta sanar mata ta dawo, ita ma ta sanar mata tana da night duty sai safiyar gobe zata dawo.
Daga haka suka kashe wayar, Mariya ta miƙe ta shiga bathroom ta ɗaura alwala ta fito ta samu Ummi Aisha ta shigo ɗakin. Sallah ta fara ita ma Ummi Aisha ta shiga bathroom ta yi alwala ta fito ta fara sallar.
Bayan Mariya ta idar ta haye saman gado ta sake ɗaukar wayarta ta kunna data don ganin sakwanni da ba ta samu gani ba tun safe, ashe nutsuwa shi yake kawo mutum ya wuni yana chat.
Babu wani dogon hira tsakinta da Ummi Aisha don Mariya ba ta son surutu sam, idan ana hira maganarta a kirge yake ko da cikin ƴan uwanta ne balle bare.
Daga murmushinta mai kyau sai umm da a'a, hakan yasa mutane suke mata kallo ta cika jan aji da miskilanci, ita kuwa har ranta ba haka bane, tayi ta zuba surutu ne ba ta so balle tsiwa da bata sanshi ba sam, abin gabanta shi ne kawai a gabanta.
Bayan ƙiran sallar isha'i Mariya ta miƙe ta gabatar, da ta idar ta ɗauki kayan baccinta na riga da wando ta saka ta haye gado. Addu'o'i ta yi ta shafa ta kwanta tana cewa Ummi Aisha."Sai da safe."
"Aiki ya nukurkusa wata."
Faɗin Ummi Aisha tana dariya. Ita dai Mariya murmushi kawai ta yi ta rufe idanuwanta, don so take bacci ya ɗauketa ko don ta samu ta farka da wuri don tafiya aiki akan lokaci.
#newbook
#vote
#comment
GOBE DA NISA
Page 2
Na Pharty BB
Mariya Abaya baƙi ta saka wanda ba shi da wani kwalliya, sai farin hijab ƙarami da ya rufe mata kirji, takalminta baƙi mai tsini da handbag ɗinta ƙarami fari, ta yi kyau sosai duk da ba wani kwalliya ta yi a fuskarta ba, sai ɗaddaďan ƙamshin turare take mai saukar da nutsuwa a ruhi da gangar jiki.
Tana gaishe da Umma ta fita a gida, bata tsaya gaishe da Abba ba. Napep ta tara sai court. Tana isa office ta wuce, ta samu maza ukun sun zo da mace ɗaya ita ma cikin Abaya kamar yadda take, alamu dai ita ma ba ta son suit ko ba ta saya ba.
Da sallama ta shiga musu suka amsa, daga haka ta nufi table ɗinta ta zauna. File ɗin jiya ta ɗauka ta fara dubawa, yana nan tsaf yanda ta bari, abu kaɗan ya rage ta gama haɗa tambayoyi da za a gabatar a court, amma kafin nan sai ta yiwa wanda suka kawo ƙarar tambayoyi.
Dafe kanta ta yi don dole sai taje, kuma dole ta sanar da wanda ya bata duba shari'ar cewa za taje. Ƙaramin tsaki tayi ƙasa ƙasa sannan ta miƙe, ta ɗauki file ɗin tare da handbag ɗinta ta fita.
Zagaye wajen ta fara tare da duba office-office ko za ta samo office ɗinsa, sai dai kaf gurin irinta ne ƙananan ma'aikata. Har ta haƙura sai kuma tayi tunanin duba saman bene, hakan yasa ta nufi can.
Tun daga harabar wajen yake da kyau da tsari, sosai gurin ya haɗu, ga office a jere reras. A hankali take tafiya tana duba kowane office da taga sunan mai shi a rubuce a sama cikin style na calligraphy, cak ta tsaya ganin sunan da ba tayi tsammanin gani ba, ta kurawa jikin ƙofar ido tamkar wacce za ta hango shi tsaye, abubuwa dayawa suka fara kai kawo a zuciyarta da ƙwaƙwalwarta da ya haddasa mata bugun zuciya.
Takun mutane da taji ya dumfarota yasa ta yi azamar ɗauke idonta, ta cije lips ɗinta jin yadda zuciyarta ta juya. Kafafuwanta taja tabar gurin cikin wani irin yanayi da ta tsinci kanta.
Office ɗaya ta tsallake sannan ta samu wanda take nema, bakin ƙofa ta ƙarasa ta ƙwanƙwasa da ƙyar saboda tsoron da taji ya maye gurbin abin da taji yanzu. Tsawon mintuna ba'a amsa ba, hakan yasa ta sake ƙwanƙwasa. Da ƙyar ta iya jiyo muryar na ciki ya bata umarni ta shiga.
Tura ƙofar ta yi a hankali tana shiga, bakinta ɗauke da sallama yayinda bugun zuciyarta ta ƙara ƙarfi. Tsaye ta yi ƙyam bayan ta daidaita nutsuwarta, ta ɗago a hankali ta kalli wajen da yake zaune, kansa a ƙasa yana danna computer tamkar bai san da shigowarta ba.
Tsawon daƙiƙa ita ta kasa magana shi bai ɗago ba ya tambayeta dalilin zuwanta ba, sai shakar ƙamshin turaren juna suke kowanne a zuci yana mitar na juna ya dame sa.
Mariya har cikin ranta jira take ya nemi dalilin zuwanta a matsayinsa na oganta, ya bata dama ta faɗi abin da take tafe da shi. Shi kuma mamakin rainin hankalinta yake da tazo ta sa shi a gaba ta kasa faɗin komai.
Fuska ya sake tamkewa ya ɗago ya mata kallo ɗaya ya mayar kansa kan abin da yake, tamkar ba zai furta komai ba da ƙyar ya buɗe baki ya ce.
"Idan ba ki da abin faɗa ki bar kaina."
Jin muryarsa yasa Mariya ɗagowa ta kalle shi, taga tamkar ba shi ya yi maganar ba. Matsawa ta yi ta ajiye file ɗin hannunta a saman table ɗinsa.
"Da ma nace zan je na musu wasu tambayoyi ne."
"Wani case ne?"
Ya tambaya yana barin abin da yake ya ɗago ya kalleta.
Kanta ta ƙara rissinarwa ta ce.
"Na yarinya da tsoho da suke gidan haya tare."
Kafin ta gama bayanin ya jawo ya buɗe, ya fara karanta abin da ta rubuta ganin yadda take fitar da harafi ɗaiɗaiya cikin sanyin murya. Bayan ya gama ya rufe ya ce.
"Babu buƙatar wannan, amma idan ta kama za kiyi hakan. Tambayoyin da kika tanada su kaɗai zasu yi aiki a court, don haka kin gama naki."
Mariya jin abin da ya faɗa yasa ta ɗago ta kalle shi, ta ga ya miƙe. Numfashi ta sauƙe a hankali, sannan ta ce.
"Ok sir."
Ta juya ta fara ƙoƙarin barin office ɗin, har ta kama handle taji ya ce."Na sallameki?"
Dakatawa ta yi ta dawo baya ta tsaya, kanta a ƙasa tana mamakin wannan isa da mulki, sai wani muzurai yake mata.
Barrister Waliy ajiye file ɗin da ya dauko ya yi saman table ya tura gabanta.
"Ki je ki duba wannan. Sabbin case ne ba kamar wanda kika gama ba, duk da shi ma sai na zauna na duba."
Mariya hannu tasa ta ɗauka tana faɗin. "Ok sir."
Daga haka ta juya ta fita cikin sauri, fitarta yasa Barrister Waliy ɗago kai, ya kalli inda ta tsaya kafin ya mayar kansa kan file ɗin da ta kawo mishi. Daki-daki yabi duk tambayoyin da ta rubuta, tabbas ta yi ƙoƙari ganin ita ce ta biyu da aka bawa aiki suka fara kawowa, kuma ko shine irin tambayoyin da zai yi kenan.
Bayan ya gama gani ya miƙe dauke da file din, ya adana a cikin files ɗin da gobe za a yi zaman shari'ar su.
...