← Book details Gobe Da Nisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 18

Sashe 7

Gobe Da Nisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi da ita ɗin yaran Yaya da ƙani ne Abubakar da Talba, wanda iyayensu su kaɗai suka haifesu. Tare suka taso su biyu, Abubakar ya riga Talba aure hakan yasa Waliy ya zamto shine babba a gidan kuma ɗa namiji kaɗai.
Haka rayuwa ta tafi har Mami ta haifi nata yaran Mimi, Ihsan da Rahma sai Rumana auta, sannan lokacin Ammi ta sake haihuwar mata ita ma Sadiya da Shukrah, Radiyya, Farah da Nabeela auta, yaran kusan sa'annu suke.
Mimi da Sadiya kansu ɗaya, Ihsan da Shukrah, Rahma da Radiyya, Farah da Rumana, sai Nabeela ita ɗaya.
A gabansa aka haifi Rumana duk da lokacin shekarunsa bakwai. Tun ranar da ya kyalla ido ya ganta ta gansa ƙaunar junansu ya shiga ransu, gida ɗaya suka taso hakan yasa suka shaku. Shekararta goma ta gama primary shi kuma secondary a lokacin mahaifin Rumana ya samu aiki a ƙasar Canada.
Nan fa aka so rabasu don Talba yace zai tafi da yaransa gaba ɗaya huɗu mata har da Rumana da ita ce ƙaramar su. Tashin hankali da Rumana da Waliy suka shiga yasa mahaifinsa Abubakar cewa a tafi da Waliy ya yi karatunsa a can, kowa yayi na'am da haka.
Haka suka tafi inda ƙarfin shaƙuwa da soyayya ta ci gaba da wanzuwa tsakanin Ruman da Waliy, har takai ya kammala karatunsa na lauyanci ya dawo ƙasarsa bautar ƙasa, anan ya tarar jinyar mahaifinsa, ga ƙannensa mata bayan Sadiya da Shukrah guda uku sun taso, Radiyya, Farah da Nabeela.
Hakan yasa ko da ya kammala bai koma ba. Jinyar ajali yasa Allah ya karɓi abunsa inda ahlin sun ji mutuwarsa, dole Talba ya zo suka yi sati biyu suka koma harda yara.
Rumana da kuka ta koma don tana son zama tare da masoyinta, shi yayi ta lallashinta don makaranta da take ya kusa karewa, sai dai ya kula ta sake shagwaɓewa da sangarta ko don har yanzu ita ce auta, kuma yanayin al'adar can ba wa yaro damar yin yadda ya so.
Bayan komawar su kullum suna cikin waya da juna, a haka ya samu aiki ya fara a court, acan kuma Rumana ta kusa kammala karatun likitanci da take. Haka Waliy ya ɗauki dawainiyar kannensa da mahaifiyarsa duk da Baba Talba yana aiko musu da kuɗaɗe da wasu abubuwan buƙata.
A haka aka aurer manya biyu Sadiya da Shukrah har da yayun Rumana da Mimi, Ihsan, saura Radiyya, Farah da Nabeela da ita ce auta, sai Rahma sa'ar Farah.
Shekara ɗaya da aurensu Sadiya suka haihu, a lokacin Rumana ta kammala karatunta ta zama likita, duk yadda iyayenta suka so tayi aiki a Canada ƙi tayi, ta birkice musu ita Nigeria zata dawo wajen Waliy don yadda ta gansa a bikinsu Sadiya tsawon shekara ta kasa mance siffarsa da kyawunsa, wanda ya ƙara mata sonsa.
Ganin haka Baba Talba yayi wa Waliy maganar aurensu, tuni ya amince don burinsu kenan. Haka aka sha biki aka kawota gidansu a part nasa wanda ita da mahaifiyarta basu so ba, amma son da take mishi ya danne.
Haka suka fara rayuwa tare da juna cikin so da ƙaunar juna, duk da Waliy yana haƙuri da wasu halayyarta na sangarci da rashin girmama na gaba da ita, don sai abin da taga dama take yi. Ya sha mata magana sai tace ita fa bata ga laifin abin da tayi ba ba.
A cikin haka ya nema mata aiki ta fara fita inda lalaci yaci gaba, don aikin gida da girki mai aiki ce take komai, babu abin da take yi sai tayi wanka ta fita aiki, ta dawo ta ci tasha, hatta wajen shimfiɗa watarana sai Waliy ya nuna mata ɓacin ransa take yarda, wai tsoron ta lalacewa take, ƙasan ranta kuma tsoron samun ciki take duk da a matsayinta na likita ta yiwa kanta garkuwar hana ɗaukar ba yanzu ba.
Ammi tana lura da duk irin zaman da suke, sai dai bata taɓa nunawa Waliy ko a fuska ba, haka ta kwaɓi yaran yiwa Rumana rashin kunya don bata ba ta girma, balle shi da babu zancen raini tsakaninsa dasu. Sai dai Ammi da yaran su haɗu su yi ta tattaunawa.
Har yau da Nabeela tana basu labarin diramar Waliy da Mariya na jiya suna dariya, sai ga Waliy da Rumana sun shigo suka katse musu.
***
A haka Waliy ya ƙarasa office da takaicin Rumana, yana shiga bai nemi kowa ba yau yaci gaba da aikinsa.
Da ƙyar ya kawar da abin da Rumana ta mishi kafin ya samu sukuni, duk da hakan yasa a ransa dole zai mata magana kuma yaci gaba da kwaɓarta don hakan ba al'adar hausa ba ce rashin girmama na gaba musamman iyaye.
...

Ɓangaren Mariya ma da nata ɓacin ran ta wuni, amma haka ta danne tayi ayyukanta musamman da Barrister Waliy ya ce yana buƙatar ɗaya wani sati, hakan yasa ta dukufa da aiki babu abin da yake ɗagata sai sallah.
Ba ta bar wajen aikin ba sai la'asar lis wajen huɗu da rabi, ji take kamar kar ta je gida ta je gidan Aunti Babie, amma babu yadda ta iya dole sai ta sanar an bata izini kafin ta tafi.
Haka ta ƙarasa gida, bayan ta biya mai napep ta shiga ciki tare da sallama. Kaɗan zuciyarta ta koma cikinta ganin motarsa a fake cikin motocin gidan, jikinta rawa ya fara da ƙyar taja ƙafafunta ta nufi falon gidan bakinta ɗauke da addu'ar da duk yazo bakinta, don ba ta shirya haɗuwar su yanzu ba.
Da sallama ƙasa ƙasa ta shiga falon, tsit tamkar anyi ruwa an ɗauke ko babu rayayyu a ciki masu numfashi don yadda ya ɗauki shuru.
Idanuwanta ta ɗago taga Baba Ƙarami da Khadeeja da Ummi Aisha suna falon, amma babu wannan hira da surutun nasu.
'Tabbas yana nan.' Zuciyarta ta faɗa mata wanda tasa ta wurga idonta saman ƙofar ɗakinsa amma wayam, ta juya zuwa dining da sauri.
Cak numfashinta ya nemi tsayawa, taji ƙafafunta sun ka sa ɗaukarta, ta durƙushe daga bakin ƙofar tana sunkuyar da kanta ƙasa zuciyarta tana cigaba da bugawa
Cikin rawar muryar tsoro ta ce.
"Yaya ina wuni? Sannu da dawowa."

Tamkar Allah bai ajiye ruwan halittar a wajen ba, haka bai ɗago ba balle ya amsa mata, sai ma ci gaba da cin abincinsa ya yi hankali kwance.
Ita fa duk miskilancinta ba ta da masifa, amma shi ya haɗa dukka biyu, ga mugunta da baƙin zuciya.
Mariya tun tana sa ran zai amsa mata harta haƙura ta miƙe da ƙyar don ta gaji da durƙushen, ga fitsari take ji.
Ganin bai ko kalleta ba, bai amsa mata ba kamar kullum yasa cikin sanɗa ta nufi ɗakinsu, takunta biyar taji tsawar da kaɗan ta saki fitsari a jikinta.

"Kina ƙara taku sai na karyaki a gidan nan." Ya faɗa cikin tsawar da ya tsorata Mariya, hatta su Ummi Aisha da tsoransa ya sake shigarsu, tamkar wanda aka ƙarawa masa masifa a ƙasar da yaje ya dawo.
Tun safe da ya bayyana a gidan kowa ya shiga hankalinsa fiye da daa. Ba ya wasa ba ya ɗaukar raini.
Mariya durƙushewa ƙasa tayi a inda take, hawaye ya taru a idanuwanta sai dai ta hanasu zuba, sai matse cinya take.
Tana tsoron faɗa da duk wani tashin hankali musamman na Yaya Haydar wanda yake yiwa kowa a gidan, musamman ita da take ganin ya tsaneta ne sosai.
Yaya Haydar bai ɗago ba balle kallon inda Mariya take, haka ya gama cin abincinsa ya miƙe ya nufi ƙofar falo, har ya kama handle zai fita yaran suna murna har Mariya sai kuma suka ga ya fasa ya dawo baya.
Bai tsaya ko'ina ba sai saman kan Mariya, kallon daƙiƙa ya mata kafin ya taɓe baki ya juya yabar wajen, wai mitsitsiyar yarinyar nan har ta kai ta karanci lauya bayan shegen tsoro da miskilanci da yake cikinta, a hakan za ta fito gaban kotu a fafata da ita, asarar kuɗi dai. Haka ya fita a falon gaba ɗaya.
Kusan kowanne su sai da ya sauƙe numfashi, musamman Mariya da ta ɗauka bugunta zai yi kamar yadda ya saba lokacin da ya tsaya a kanta.
Cikin sauri ta miƙe ta faɗa ɗakin su, kayan hannunta ta ajiye a saman gado ta wuce bathroom da sauri, fitsari tayi ta ɗaura alwala ta fito jin ana ƙiraye ƙirayen sallar magriba.
Sallah ta gabatar, bayan ta idar ta sake komawa bathroom ta watsa ruwa, ta fito ta canza kayanta ta haye gado ta kwanta, tunanin abin da ya faru ya dawo mata.
Tuna haka gaba ɗaya taji jikinta yayi sanyi, har take jin anya yadda Yaya Haydar yake zai iya barinta cikar burinta. Ya tsaneta zai iya warzaga mata dukkan plans nata musamman a matsayinsa na babban lauya da ya fita sanin kan aikinsa, ya karantu sosai.
Siraran hawaye ne suka zubo mata a saman kyakkyawar fuskarta, tasa hannu ta share tare da miƙa dukkanin lamuranta ga Allah. Tasan shi ne ya bata tsawon rai da damar zama Barrister don cikar burinta, tasan Allah zai bata mafita.
Haka ta zauna a ɗaki duk yunwar da take ji, duk da tana jin hayaniyar yara da ya ba ta tabbacin Yaya Haydar baya falon amma tsoronfita take.
Ana yin sallar isha'i ta miƙe ta gabatar ta haye gado ta kwanta. Tun tana ji motsi da hayaniyarsu har bacci ya ɗauketa.

A can falo suma yaran suna gama yin abin da zasu yi suka shige ɗakunan su gudun yayan nasu ya dawo ya same su ya lallasa su. Umma da Abba kam dariya suke musu don yadda suke tsoransa ko su basa tsoro.
Chapter 7 · 0% Book details