Sashe 18
Gobe Da Nisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Sai lokacin ta ji nutsuwa ta rumgume Zakiyyah tsam tana sauƙe numfashi kamar wacce tayi gudu, ita kanta Zakiyyah ta tsorata da yanayi Mariya, ta san ba ƙaramin mafarki ba ne yake farkar da mutum a bacci har yana surutu haka ba.
Mariya a jikin Zakiyyah wani bacci ya ɗauketa, jin haka Zakiyyah ta gyara mata kwanciya ita ma ta kwanta, da ƙyar wani baccin ya ɗauketa.
Ƙarfe biyar na asuba suka farka shi ma ƙarar wayar Mariya ne ya farkar dasu. Da ƙyar ta jawo ta ɗauka ta gani, ba ta san numbern ba ga ƙiran asuba, har zai yanke ta tuna da maganar da suka yi da Barrister Waliy, hakan yasa ta ɗauka da sauri tana kafawa a kunne.
Tana ji daga ɓangaren sa ya yi mata sallama yana faɗin. "Kin yi sallah ma? Ko you're off."
"Um um. Yanzu zan yi." Ta faɗa bayan ta amsa sallamarsa, cike da jin nauyin faɗa mishi ba ta yi sallah ba duk da har yanzu akwai masallatai da suke.
Maganarsa taji yana faɗin. "Na ba ki 10mins ki kammala. Kafin nan turo min address na gidan da kike."
"To sir." Faɗin Mariya tana cire wayarta ta kashe, da sauri ta shiga bathroom ta ɗaura alwala ta fito. Zakiyyah kuma ta koma bacci don ba ta sallah.
Mariya kafin ta fara gabatar da sallah sai da ta ɗauki wayarta ta tura mishi address ɗinta kamar yadda ya buƙata, sannan ta fara sallah.
Tana idarwa ta miƙe ta ɗauki wayarta ta fice a ɗaki, tararwa tayi falo babu kowa, cikin sanɗa ta buɗe ƙofar ta fice fit. Haka get ma ta samu a buɗe don daga dawowa sallah mai gadi bai rufe ba dama ba ya rufewa, hakan ya ba ta damar fita.
Tafe take garin har yanzu da ɗan duhu, sauri take zabgawa tare da addu'ar Allah yasa ta samu napep masu fitowar asuba.
Haskata aka yi ta gaban hanya, tasa hannu ta kare fuskarta tana matsawa gefe. Motar a hankali ta taho har ta tsaya gaban Mariya, kallon mai motar tayi mamaki ya bayyana a fuskarta ganin Barrister Waliy, wanda hasken alfijir ya ba ta damar kallo. Sam ba ta yi tunanin zai zo bane yasa ta tura mishi address ɗinta.
Barrister Waliy ɗauke kansa ya yi daga kallon da Mariya take mishi yau na kurilla, manyan idanuwanta da basa kallonsa sosai yaji sun hanashi kallonta da kyau.
"Zagayo ki shigo rana tana yi." Ya faɗa a hankali.
Sai lokacin Mariya ta ankara, ta ɗauke idanuwanta tana sauƙe numfashi. A hankali ta zagaya ta buɗe ta shiga, shi ko ya yi riverse suka bar unguwar.
Tafe suke shuru har lokacin ba a fara fitowa ba, sai matafiya nesa da ɗaiɗaikun napep, a haka har suka isa gidansu Mariya, yayi fakin a gefe kaɗan.
Kallonta ya yi wacce ta zubawa ƙofar gidansu ido, yasan akwai zafi da ciwo iyayenka su koreka a gida, amma ya ta iya? Nata ƙaddarar kenan.
Numfawa ya yi a hankali sannan ya ce."Ki yi sauri ki shiga ki fito."
Mariya ba ta iya magana ba a hankali ta buɗe motarsa ta fita, ta nufi gidan zuciyarta cike da addu'o'i. Tana isa get ɗin a hankali ta tura ƙofar ya buɗe, tasan mai gadi yana bari a buɗe. Hakan ya ba ta damar shiga ta shige cikin gidan, babu motar Abba sai na Yaya Haydar.
Cikin sanɗa ta nufi falon gidan, a bakin ƙofa ta tsaya ta kama handle ɗin ƙofa ta tura a hankali tana saka kanta. Falon shuru babu kowa alamar duk suna ɗaki, ajiyar zuciya ta sauƙe ta ƙarasa shiga ciki, ba ta tsaya dube-dube ba ta nufi ɗakinsu da sauri.
Ummi Aisha ta samu tana ta bacci, a hankali ta taka har zuwa inda bedside drower yake, ta jawo ta buɗe tare da tura hannunta ciki sosai ta ƙasa don ba irin mai cirewa ba ne. Nan taci karo da folder da take ajiyewa shekara da shekaru, ta jawo ta ɗauka tana mayar drawer.
Miƙewa tayi a hankali ta fice a ɗakin zuwa falo, har lokacin babu kowa sai dai wutar falon a kunne, motsi ta ji a kitchen. Jin haka ya haddasa mata tsoro, cikin sauri ta fice har da ɗan ƙarawa da gudu, haka ta fice a gidan tare da ƙarasawa wajen motar Waliy ta shiga. Motar a kunne hakan yasa yaja suna barin wajen cikin sauri.
Yaya Haydar jin motsi a falo da ƙarar buɗe ƙofa yasa ya fito a kitchen, sai dai wayam babu kowa. Har zai koma ya ka sa zuciyarsa ta ka sa aminta cewa wani bai shigo ba, haka ya juya ya fita har zuwa get ya buɗe, amma sam babu alamar kowa, hasalima layin shuru. Haka ya koma cikin gidan, bai shiga kitchen ba ya fasa ya wuce ɗakinsa.
...
Sun yi nisa Barrister Waliy ya kalla Mariya wacce take damƙe da foldern, ya mayar kansa kan titi sannan ya ce.
"Fatan babu wanda ya ganki?"
Kai ta ɗaga masa tana faɗin."Babu."
Tafiya suka ci gaba da yi babu wanda ya ƙara magana, har ƙofar gidan su Mariya ya faka.
Mariya foldern ta miƙa masa, ya karɓa ya ajiye a gefe sannan ta ce. "Sai anjima."
Kai ya ɗaga mata ta fice a motar tana shigewa gida. Sai da yaga shigarta yaja motarsa yabar harabar gidan.
Gidansa ya koma ya samu Rumana ta farka tana shirin aiki, shi ma wanka ya yi yai shirin ganin takwas saura. Suka yi breakfast sannan suka nufi wajen Ammi.
Cikin girmamawa Waliy ya gaishe da ita ta amsa, haka Rumana ma ta gaishe da ita kamar yadda take yi kullum.
Ammi ta amsa mata kamar babu komai. Daga nan suka mata sallama suka fito, bayan sun yiwa juna sallama kowanne ya shiga motarsa suka fita suka nufi wajen aikin su.
...
Mariya lokacin da ta shiga gida Zakiyyah ta farka tana bathroom, jiranta ta yi ta fito sannan ita ma ta shiga. Fitowa tayi ta hau shiri cikin coat ɗinta, tayi kyau kamar kullum sai ƙamshi take.
Bayan ta kammala ta fita falo, ta samu Aunti Babie ta farka tana shirya yara makaranta. Gaishe da ita ta yi sannan ta wuce kitchen, tea ta haɗa tasha a tsaitsaye ta fita, ta yiwa Aunti Babie sallama ta fita.
Napep ta tara ya kaita office, kai tsaye office ɗinsu ta wuce bayan ta sauƙa. Bayan ta musu sallama ta zauna a desk nata, ta ɗauki ɗayan case din da ya rage mata ta fara dubawa.
Ranar haka ta wuni babu wanda ta haɗu dashi daga Barrister Waliy har Yaya Haydar. Ƙarfe huɗu da rabi ta bar office ta wuce gida.
Kwanakin da suka wuce kafin sati biyu ranar zaman shari'a
...
To fa ana wata ga wata?
Tambayoyi nasan da yawa a cikin ranku dangane da kowa a cikin littafin da komai da yake faruwa.
Ku biyo ni don samun amsoshinku har da wanda ban lissafa ba. Akwai ƙaddara, sadaukarwa, kauna da zazzafan soyayya(hot love) da ba ku taɓa karantawa a littafaina ba, sai kun karanta kawai. Kun san littafaina but wannan daban ne.
Mai buƙatar Books 2 completed akwai a ArewaBook a farashi mai sauƙi.
#vote
#comments