Sashe 14
Gobe Da Nisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cike da tsoron me zai ce ta girgiza kanta, ruwan hawaye ya taru a idanuwanta ta kalle shi, da ƙyar ta yi ƙoƙarin kallon cikin idanuwansa ta ce."Ni ba zan iya kwana ni ɗaya ba."
"Ina Ummi Aisha da Haneefa." Ya faɗa yana juyawa ya dubi Umma da Abba, sai lokacin ya lura babu su duk hayaniyar.
Maganar Mariya yasa ya dubeta lokacin da ta ce. "Ba ta nan, Haneefa tana asibiti."
Bai ce komai ba yaja hannunta suka nufi ɗakinsa da yake daga can ƙarshe. Ai Mariya ji ta yi da ba ta sanar da shi ba, jikinta rawa ya ci gaba da yi yadda yafi na farko. Ita tun da take ma za ta ce bai fi sau biyu ta shiga ɗakinsa ba, shi ma sai ba ya nan gudun ya ce ta mishi laifi ya daketa.
Tana ji tana gani babu damar mishi musu, haka ya buɗe ɗakinsa suka shiga. Ɗakinsa mai kyau da shi komai fari da blue, tsaf da shi kamar ɗakin mace sai ƙamshi da sanyin AC. Fagen tsafta Yaya Haydar ba baya ba ne domin yana da mugun tsafta da kyankyami.
Suna shiga ya sakar mata hannu ya nufi wardrobe ɗinsa, hakan yasa ta tsaya ta ka sa ƙarasawa ciki.
Yaya Haydar duvet ya ɗauka sabo ya dawo wajenta, miƙa mata ya yi babu musu ta karɓa da sauri. Gurinta ya bari yana fadin.
"Ki kwanta a saman sofa."
Daga haka ya haye saman gado ya kwanta ya rabu da ita. Mariya ta kusan mintuna uku a tsaye, ta ka sa ko motsawa, mamakinsa take yadda yake nuna mata kulawa, abin da hakan bai taɓafaruwa tsakanin su ba.
"Za ki zo ki kwanta ko sai na ɗaukoki." Ta ji mugun tsawarsa da ya dawo da ita hankalinta, ta dube shi da sauri ta ga ya tashi zaune.
Kanta ta sunkuyar ƙasa ta ja ƙafafuwanta ta nufi sofar da yake facing ɗinsa ta zauna.
"Tashi ki fita min a ɗaki." Ya faɗa cikin tsawar da ya tsorata Mariya.
Da sauri ta kalle shi ta ga ya watsa mata wani kallo da manyan idanuwansa masu tsoratata, cikin azama ta ɗauke nata ta gyara kwanciyarta ta rufe jikinta har saman kanta, zuciyarta sai bugawa take da sauri na tsoron kasancewa da Yaya Haydar da kuma abin da ya faru.
Tasan Allah ne kaɗai ya ceceta daga afkuwar komai, da ba ta san ya za tayi ba, kuma ba ta san wa za ta tuhuma ba. Ba ta hayyacinta balle ta bambamce wanene, har ta gano ina ya shiga lokacin da ya gudu dalilin ihunta.
Tana wannan tunanin har bacci ya ɗauketa ba ta sani ba, sai dai cike da tsoro take yi don cikin baccin ma sai mafarki take.
Yaya Haydar bayan ya kwanta shi ma da ƙyar bacci ya ɗauke sa tuna abin da ya faru, yasan Allah ne kawai ya rufa asiri yau.
Ƙiran sallar asuba ya farkar dasu, shi ya fara miƙewa ya shiga bathroom ya ɗaura alwala ya fito. Wajen Mariya ya nufa ya tsaya a kanta, gaba ɗaya jikinta a rufe ta kudundune sai fuskarta da ta buɗe.
Innocent face nata fiyau, gashin kanta da yake a wargaje ya bazu a saman pillow wani a gefen fuskarta, ta ɗan turo ƙaramin bakinta alama ba ta jin daɗin baccin ko sanyi ya dameta duba da yadda ta dukunkune.
Ruwan hannunsa ya watsawa fuskarta da yasa Mariya firgita tana neman yin ihu. Ganin Yaya Haydar yasa ta nutsuwa tana yin ƙasa da kanta ganin ya watsa mata wannan kallonsa.
Gurinta ya bari bai ce mata komai ba ya fita a ɗakin. Numfashi ta sauƙe tana mamakin halinsa, duk abin da yaga dama yi yake babu ruwansa, idan mugunta ne yasan duk ta inda zai yiwa mutum.
Miƙewa ta yi ta ɗauki duvet ɗin da ta rufu da shi ta linke, ta ajiye a saman sofa ta bar gurin tana fita a ɗakinsa, sam ba za ta iya shiga mishi bathroom ba, salon ya zo ya samu na jibgarta ya ce ta mishi wani abun.
Ɗakin su ta buɗe ta shigar da ƙyar don tsoro, hakanma ganin asuba ne kuma kowa ya farka, bayan ta shiga key ta sawa ƙofa, tabi ɗakin da kallo yana nan yadda yake, sai lokacin mamakin yadda aka fitarta a ciki take. Tasan dai tana tunani da jiran ko Ummi Aisha za ta shigo har bacci ya ɗauketa, ba ta sake sanin komai ba sai lalubarta da taji ana yi tamkar a mafarkinta farka.
Kawar da tunanin tayi da sauri ta wuce bathroom, kulle ƙofa ta yi kafin ta yi fitsari ta yi tsarki ta ɗaura alwala ta buɗe ta fito. Rigar jikinta ta cire ta saka wani, ta ɗauki hijab ta saka ta nufi inda sallayarsu yake shimfiɗe ta fara gabatar da sallar.
Ko da ta idar ka sa komawa bacci ta yi, ta zauna tana azahar, ƙarshe ta miƙe ta ɗauki Alkur'ani ta fara karantawa. A haka har gari ya yi haske rana ta fito, ƙwanƙwasa ƙofa da aka yi yasa ta miƙe tana rufe Alkur'anin ta miƙe ta isa bakin ƙofa ta buɗe.
Umma ce tsaye, Mariya ta gaishe da ita cikin nutsuwa. Umma ta bita da kallo cike da tausayinta.
"Kin farka lafiya?" Ta faɗa tana amsa gaisuwarta.
Mariya kanta ta ɗaga alamar lafiya. Umma ta kamo hannunta suka shiga ɗakin, a bakin gado suka zauna tana binta da kallo ciki da waje kusan mintuna.
Murmushi Mariya ta yi ta ce. "Babu komai fa Umma."
"Kin tabbatar?" Umma ta tambaya tana miƙewa.
Mariya kai ta ɗaga tana faɗin. "Eh, shiryawa ma zan yi na tafi aiki."
Jin haka yasa Umma yarda lafiyarta ƙalau, fita ta yi ta samu Abba da ya turota duba lafiyar Mariya ta sanar mishi.
Numfashi ya sauƙe sannan ya miƙe ya ce."Shike nan zan wuce, bana son yin rana ne, zan dawo da yammacin yau ƙarfe huɗu zuwa biyar. "
Umma ta miƙe ta mishi rakiya har filin gida wajen motarsa, sannan ta dawo falo ta ci gaba da ayyukanta.
...
Da safe sanin Abba yabar gida yasa yaran babu wanda ya zauna dining don yin breakfast. Musamman da dodonsu yana zaune shi ɗaya a wajen, ai hakan yasa wasu ko gigin yin breakfast ba su yi ba suka bar gidan, ciki har da Mariya.
Ya zauna bai jima ba Mariya ta fito cikin sanɗa ta fice fit a falon kafin ya ankara da ita.
Maryam ma hakan sai dai ita ya hangota, dole yasa ta dakata ta gaishe da shi. Hannu kawai ya ɗaga mata ta miƙe ta fita.
A tunaninsa Mariya tana ciki ta fito ya hanata tafiya aiki, haka ya yi ta zama don jiranta har ƙarfe tara, leɓbensa ya cije zuciyarsa ta fara hasala.
Miƙewa ya yi cikin ɗaga murya ya kwalawa Ummi Aisha ƙira. Shuru ba ta amsa ba, sai Khadeeja ta fito jiki yana rawa ta durƙushe ƙasa.
"Ina yarinyar nan?"
Ya faɗa cikin ɓacin rai.
Khadeeja cikin mutuƙar tsorata ta ce. "In dai Maryam ce ta fita."
Cikin daka tsawa ya tareta ya ce.
"Dalla ba ita ba Kibdiyya."
Sanin shi ɗaya yake ƙiranta haka yasa ta gane da Mariya yake, cikin sauri ta ce.
"Ta fita tun ƙarfe bakwai saura."
"What!?" Ya faɗa a mutuƙar mamaki cikin tsawa, bai ƙara faɗin komai ba ya juya yabar falon.
Khadeeja numfashi ta sauƙe sai kuma cikin sauri ta miƙe ta shige ɗakinsu duk ƙira da Umma take mata a nata ɗakin.
Wayarta ta nemo ta ƙira lambar Mariya, ringing biyu ta ɗauka. Ba ta jira me zata faɗa ba ta sanar mata Yaya Haydar yana nemanta me ta mishi.
Daga ɓangaren Mariya tsoro ne ya kamata, cikin raunin murya ta ce. "Babu komai."
"To wallahi ki san nayi, don ya fita cikin ɓacin rai."
Khadeeja ta faɗa cike da tausayin Mariya, sam ta rasa me yasa Yayan nasu yafi takurawa Mariya a kansu, baza tace su ba ya musu mugunta ba ko dukansu amma na Mariya yafi nasu don ko yaya tayi abu laifi ne.
Bayan haka yau kam ko me ta mishi ya rabu da ita duba da abin da ya faru da ita jiya, wanda har yanzu babu wanda ya maimaita maganar, ƙarshe ma kowa ya kama harkar gaban shi kamar babu abin da ya faru.
Zare wayarta tayi ta ajiye jin Mariya ta kashe, ta miƙe cikin sanyin jiki don amsa ƙiran Umma.
...
Mariya tana gama waya da Khadeeja ta miƙe, ta ɗauki file ɗin case na Isah Hamza da ta gama dubawa yanzu ta fita.
Cikin sauri ta nufi offices ɗin Barrister Waliy, ƙwanƙwasa ƙofa take tayi babu kakkautawa don tana tsoron Yaya Haydar zo ya tarar da ita, ba ta san me kuma ta mishi ba.
Daga ciki ya bada izinin shiga, cikin sauri ta buɗe ta shiga. Da kallo Barrister Waliy ya bita ganin kamar a birkice take, ganin ta tsaya ta ƙi ƙarasawa ya nuna mata kujera.
"Zo ki zauna."
Babu musu Mariya ta matsa ta zauna tana sauƙe ajiyar zuciya, sai da ta nutsu ta ajiye file ɗin hannunta ta ce.
"Ga wannan na kammala, saura ɗayan."
Barrister Waliy ɗauka yayi ya ajiye a gefe, ya kalleta kanta a ƙasa, ganin ba ta motsa ba kuma ba ta da niyar tashi ya ce. "Shikenan, zan duba."
Mariya ka sa tashi ta yi, kanta a ƙasa tana murza yatsun hannunta, zuciyarta tana ta kai-kawo akan hukuncin da ta yanke mata, tana faɗa mata ta sanar da shi kudurinta ko zai taimaka mata, amma wata zuciya tana hanata.
Barrister Waliy da ya gama ƙare mata kallo ya gama karantar yanayinta ya yi gyaran murya, sannan ya ce.
"Kina da matsala ne?"
Mariya kai ta ɗaga a hankali ba ta kalle shi ba har lokacin kanta a ƙasa, cikin sanyin murya ta ce.
"Ina da babbar matsala a rayuwata tsawon shekaru, kowanne dare takan yi tsayi a idanuwana har nake ganin GOBE TA MIN NISA, da fargaba nake kwana a kowanne daren rayuwata. GOBE TA MIN NISA balle burina ya cika. Ta ina zan fara? Ta ya zan cika burina da mafarkina? Sai da taimako, amma ban san wa zan tunkara ba. Don haka ina neman taimako domin samun wanda zai tsaya min ya taya ni bani ƙarfin guiwa."