← Book details Gobe Da Nisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 18

Sashe 12

Gobe Da Nisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu musu ta miƙe ta zuba mishi ta ajiye masa, ta zuba nata kaɗan ta fara ci a hankali, sauran ma suka zuba a dadare don sun san kuskure kaɗan zasu yi Yaya Haydar ya ci kaniyarsu. Haka suka fara ci banda Mariya da aka haɗa da shan shayi mai zafi.
Yaya Haydar ne ya fara miƙewa don kaɗan ya ci ya bari, sai Abba shi ma ya miƙe ya kalli Mariya ya ce.
"Tashi ku tafi."

Cikin hanzari ta ɗago kanta tana kallon Abba jin abin da ya faɗa. Girgiza kanta tayi idanuwanta suka cika da kwalla, ƙasa ƙasa don Yaya Haydar kar yaji ganin yayi gaba ta ce.
"Abba ya je kawai."

"Tashi Sister kar kiyi wani laifin."
Haneefa ta faɗawa Mariya hakan don tuna mata kar tayi wani laifin da zai jawo mata matsala a aikinta.
Mariya kallon Haneefa tayi, ta ga ta ɗaga mata kai alamar ta tashi taje.
Babu musu ta miƙe ta ɗauki handbag ɗinta tabi bayansa don har ya fice a falon tuni, haka Abba ma da ta rasa me zai yi yabi su.
  Yaya Haydar ta samu jikin motarsa, Abba a gefe yana mishi magana. Kallo ɗaya ta mishi ta sunkuyar kanta ƙasa ganin fuskar nan a haɗe  kamar koyaushe, tasan yau mai hanasa mata abin da yaga dama a mota sai Allah.
Ita ta rasa me yasa Abba yake son haɗata da shi, kuma ya san ba shiri suke ba, ya san halin yayan nasu ba ya haɗa hanya da su, ba shi da aiki sai cin zalinsu musamman ita.

'Ko dai daɗi yake ji idan yaga yana cin zalinta?' Ta tambayi kanta.

#vote
#comment
[06/06, 7:28 pm] Pharty BB: GOBE DA NISA
Page 9
Na Pharty BB

Mariya da ƙyar taja ƙafafuwanta zuwa gare su, yayinda zuciyarta ta ci gaba da bugawa. Abba da kansa ya buɗe mata gidan gefen Yaya Haydar.
Da murmushi a fuskarsa kamar koyaushe, yana kallon Mariya ya ce. "Shiga ku je Daughter."

  Ba ta iya musu ba haka ta shiga ta zauna a dadare, tabbas da tana da dama ko su biyu ne da Abba da tuni ta bijire mishi, amma tasan yin hakan tamkar yin gaggarumin laifi ne a gurin Yaya Haydar.
  A murfin mota ta takure kanta waje ɗaya, motar banda ƙamshin mayen turarensa da sanyin ac babu komai ko karatu balle kiɗa. Tana ji ya yi hon mai gadi ya zo ya buɗe mishi get. Cikin sauri ya fizgi motar suka fita a gida.
  Sun yi nisa a tafiya a tsakiyar hanya taga ya gangara gefen titi, ita dai bata ce komai ba don numfashi ma da ƙyar take ja balle wani motsi, tsoronta ɗaya kar ya mata maganar nema mata sallama a aiki da ya faɗa .
  Yaya Haydar juyawa ya yi ya kalli Mariya, ta haɗe cikin baƙin coat nata da ƙaramin baby hijab fari, jakarta ma fari, dole ta burge mutum kasancewarta ƙarama kuma mace cikin shigar manya.
Gare shi kam ko kusa bata burge shi ba, baki ya taɓe yana ɗauke kansa daga kallonta.
"Fice min a mota don ni ba driver naki bane." Ya faɗa mata cikin muryar nan nasa mai tsoratata.
  Kafin ya gama rufe baki Mariya ta buɗe ƙofar mota ta fice fit. Sam ba ta ji haushi ba, sai ma daɗi da nutsuwa da taji na ganin sun raba hanya.
  Figar motar yayi yabar wajenta, ba ta ko juya ta kalle shi ba ta hau tsayar da napep, bayan ya tsaya ta shiga tana faɗa masa inda zai kaita.
  Suna isa ta biya shi ta wuce ciki, can wajen fakin idanuwanta ya hango mata motar Barrister Waliy da Yaya Haydar. Ɗauke kanta tayi ta ci gaba da tafiya cikin nutsuwarta wanda yake ɗaukar hankalin mutane, wanda kamar da gayya ko yanga take tafiyar.
  Office ta nufa kai tsaye ta shiga musu da sallama, wanda suka ji suka amsa mata. Saman table nata ta nufa ta zauna da bismilla.

"Oga ya aiko ƙiranki." Faɗin ta gefenta mace.
  Mariya cikin mamakin da ya bayyana a fuskarta ta kalleta ta ce.
"Ni ko wa?"

"Ke dai, ko ba ke ce Mariya ba?"
Ta faɗa mata tana mayar kanta kan computer nata.
  Mariya jiki a sanyaye ta miƙe ta fita, ba ta tsaya ko'ina ba sai upstairs da zai sadata da office ɗinsa, haka ta zo ta gifta ta office ɗin Yaya Haydar a tsorace ce tamkar za ta gansa, inda aka yi rashin sa'a wucewarta ta yi daidai da buɗe office ɗinsa ya fito.
  Ba ta lura dashi ba, don ta basa baya a lokacin ta buɗe office ɗin Barrister Waliy ta shiga da sallama.
  Yana zaune kamar kullum yana aiki, ƙyam ta tsaya kanta a ƙasa ta ce. "Ina kwana sir"

  Sai lokacin ya ɗago kansa idonsa ya sauƙa a fuskarta. Karantar yanayin fuskarta ya yi duk da ta dukar idanuwanta ƙasa. Fuskarta kamar koyaushe babu son hayaniya sai alamun tsoro kaɗan.
  Ɗauke kansa ya yi daga kallonta, ya sauƙe numfashi da bai san daga ina ya fito ba. Murya a hankali tamkar ba nashi ba har Mariya sai da ta ɗago, a lokacin ya ce.
"Koma aikinki, anjima zamu fita tare."

  Kanta ta mayar ƙasa ganin ya sake ɗagowa sun haɗa ido, a hankali ta juya ta fita. Office ɗinsu ta koma, computer nata ta kunna don fara duba aikin ciki taji ƙarar wayarta.
Barin abin da take yi tayi ta buɗe jakarta ta ciro, sabon lamba ta gani, kamar ba zata ɗauka ba sai kuma tayi tunanin ko ƙiran yana da mahimmanci, hakan yasa ta ɗauka tare da sallama a hankali.
  Daga can ɓangaren taji muryar Nabeela cikin rawar kannan nata, ta amsa tana tambayarta aiki.
  Murmushin ƙarfin hali Mariya tayi tana faɗin.
"Allahamdulillahi. Ya karatu?"

"Lafiya lau sai wahala. Ga Ammina ku gaisa kullum ina ba ta labarinki."
Nabeela ta faɗa daga ɓangarenta, kafin Mariya tayi wani yunkurin ko magana ta ji ta zare wayar, ta ji muryar Dattijuwar mace tana mata sallama.
  A kunya ce cike da nauyinta Mariya ta amsa tana gaishe da ita. Ammi daga ɓangarenta tuni ta sake yabawa da nutsuwar Mariya, cikin farin ciki ta ce.
"Sai haƙuri da shiriritar Nabeela, kullum tana bani labarinki."

"Babu komai wallahi. Allah ya ƙara tsawon rai Ammi."
Mariya ta faɗa tamkar yadda ta ji Nabeela ta faɗa mata.
Ammi ta ji daɗin addu'arta sosai, ta amsa da amin ta bawa Nabeela wayar. Anan ta sake haɗata da Farah da Radiyya duk sai da suka gaisa sannan ta kashe, suna yabawa da hankalin Mariya don daga yanayin muryarta babu rawar kai da feleke suka ji.
...
  Mariya kam mamakin Nabeela take ganin yadda ta ɗauketa lokaci ɗaya, hakan yasa ita ma tayi saving number nata kafin ta mayar wayarta jaka ta fara aikinta, so take ta tattara shari'ar Isah Hamza ta damƙawa Barrister Waliy nan da gobe.
Sallar azahar ya ɗagata, ta fita ta yi sallah, ta siya abinci taci sannan ta dawo office. Tana zama ta ji sallama cikin muryarsa, da sauri ta ɗago tana amsawa suka haɗa ido, tayi saurin yin ƙasa da kanta.

"Biyo ni."Ya ce da ita yana juyawa ya fita.
Babu musu Mariya ta miƙe ta ɗauki handbag ɗinta tabi bayansa.
   Wajen parking ta ga ya nufa, ita ma ta ƙarasa zuwa wajen daidai ya buɗe motarsa ya shiga, zagayawa ta yi ta buɗe ta shiga don ta san yace zasu fita tare mai yiwuwa akan aiki ne, hakan yasa tabi sa.
Bayan shigar Mariya ta kulle ƙofa ta gyara zamanta, Barrister Waliy ya yi riverse yaja motarsa suka fita a ma'aikatar.

  Yaya Haydar yana cikin motarsa yana kallon su tin fitowarsu ransa a haɗe, idan ransa yayi dubu ya ɓaci.
Da safe ma ya ganta ta shiga office ɗinsa, yanzu kuma ya gansu sun fita tare. Leɓbensa ya cije kamar zai huda su, a ransa ya kudura niyar zai yi maganinta idan shi ne, sai ta gwammace tabar aikin da hukuncin da zai mata yau idan sun koma gida.
...

  Mariya da Barrister Waliy bayan fitar su wani waje ta rakasa akan wani shari'a da yake dubawa, sun ɗan ɓata lokaci sannan suka kamo hanyar office.
  Shuru cikin motar kamar yadda suka zo, sun kusa isa taji maganarsa ya ratsa dodon kunnuwanta, cikin sabuwar muryarsa da yake ba ta mamakin ashe yana da sanyin murya.

"Ya ku ka yi da Barrister Aliyu?" Ta ji ya tambayeta.
Ita ma a hankali cikin sanyin muryarta da yafi nashi ta ce.
"Bai ce komai ba."

"Ok fine." Ya faɗa yana ci gaba da tuƙi. A haka suka isa court, bayan ya yi fakin kafin Mariya ta fita ya sake tambayarta."Ya maganar case biyun da na ba ki? Ga shi har gobe Friday."

"Gobe zan kawo ɗaya." Mariya ta faɗa mishi, da sauri ta fita a motar ganin mutane suna wucewa suna kallon su.
  Shi ma fita yayi daga nan kowanne ya nufi office ɗinsa.
  Mariya tana shiga sosai ta dukufa akan case ɗin ganin yana nema, ta kammala komai ta ajiye a guri mai kyau, akan gobe za ta ba shi ya duba kafin Monday.
  Ƙarfe biyar da minti goma tabar office lokacin duk kowa ya watse a ciki sai ita, ita ma lokaci ta ƙara gudun ta fita ta haɗu da Yaya Haydar, ko ta koma gida ya ganta ya ce ta yi saurin dawowa.
  Ai kuwa babu motarsa alamar ya tafi, haka ta fice zuwa bakin hanya, napep ta tara ta shiga zuwa gida, bayan ta isa ta biyasa ta sauƙa ta shiga gidan.
  Motarsa kaɗai a filin gidan babu na Abba, addu'arta ɗaya Allah yasa ba ya falo. Da ƙyar ta shiga falon da sallama a bakinta.
  Falon tsit babu wanda ya amsa mata inda ta tabbatar yana nan, zuciyarta ce ta buga wanda ta jima da sabawa da hakan indai akan Yaya Haydar ne, tasan dalilinsa wataran zuciyarta za ta yi bugawar da ba zata sake amfanuwa ba ko yayi ajalinta.
Shi kaɗai ne zaune a falon sai ƙarar TV yana aiki, can dining Umma ce da alama wani abun take yi.
  Mariya durƙushewa tayi har ƙasa, cikin tsoron me zai biyo baya ta ce.
"Sannu da hutawa Yaah Haydar."
Chapter 12 · 0% Book details