← Book details Gobe Da Nisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 18

Sashe 13

Gobe Da Nisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bar kaina." Ya faɗa mata a tsawa ce.
Babu shiri Mariya ta miƙe tana wucewa ɗakinsu. Ita kam ta rasa me ta tsarewa Yaya Haydar, ba ya ko amsa gaisuwarta daga hantara sai faɗa.
  Numfashi ta sauƙe ta cire baby hijab ɗinta, ta cire coat na sama ta rage daga ita sai rigar sama da dogon wando. Botilar rigarta ta fara cirewa har ta yi rabi daidai na kirjinta ta balla.
Buɗe ƙofar ɗakinsu ta ji anyi, tsammaninta Ummi Aisha ce don ba ta ga alamar Haneefa ta dawo ba, ba ta juyowa ba ta ci gaba da cire botilan, ta ce.
"Akku ina kika shiga?"

  Damƙar gashin kanta da yake parke mai cika da tsayi ta ji anyi ta baya, cikin mutuƙar jin zafi ta bar cire rigarta ta riƙo hannun wanda ya damƙa, da ƙyar ta juya suka haɗa ido da Yaya Haydar fuskarsa a mutuƙar ɗaure.
  Kirjinta kaɗan ya faso ya fito, tuni ta nemi jin zafin da take ji ta rasa, sai neman jin me ta aikata mishi don ba ta hango tausayinta a idanuwansa ba.
  Idanuwanta cike da hawaye tana girgiza kanta da ƙyar don azabar zafi, ta fara faɗin.
"Don Allah Yaah Haydar kar ka dake ni, don Allah ka sakar min gashina zafi yake min."

  Sake damƙa yayi don so yake ta ji zafin da yake ji shi ma a zuciyarsa. Mariya babu shiri ta saka mishi kuka, tana sake riƙe hannunsa ta ma ka sa magana.
  Yin shurunta yasa cikin muryarsa mai firgitata ya fara faɗin.
"Uban me tsakaninki da shi? Da ma maza kika fara bi ba aiki kike zuwa ba?"

  Da sauri Mariya ta dakatar da kukanta ta kalle shi, wani birkitaccen kallo ya watsa mata, ta ɗauke idanuwanta tana runtsewa cikin jin zafin maganganunsa hawayen ciki suka zubo.
  Sauƙar zazzafar mari taji saman fuskarta, babu shiri ta buɗe idanuwanta tana fashewa da kuka mai ban tausayi.

"Ba tambayarki nake ba?" Ya sake faɗa yana riƙe gashinta da ƙarfi.
Cikin kuka Mariya ta buɗe baki da ƙyar ta ce. "Aiki muka fita tare, amma babu komai tsakaninmu na rantse da Allah."

  Sakin gashinta ya yi ya turata ta yi baya, da sauri kuma ya fizgota ta faɗo jikinsa ya riƙeta gam ganin za ta buge kanta da gado, kuma za ta ji mummunar ciwo.
  Mariya gaba ɗayanta ta faɗa kirjinsa cikin tsoro tana riƙe shi, hannayenta ya sauƙa a wuyansa ta riƙosa da kyau don ita kanta ta tsorata da faɗuwar da za ta yi.
  Yaya Haydar yana jin yadda take fitar da numfashin tsoro yana sauƙa mishi, ga tudun kirjinta ya tokare shi, hakan yasa ya janyeta jikinsa cikin sauri.
  Babu shiri Mariya ta durƙushe ƙasa tana ci gaba da kuka. Yaya Haydar rankwashi ya sake sakar matar a tsakiyar kanta da ya sake sata sakin wani ƙaramin ƙara don zafi.
  Daga haka ya juya ya fice cike da jin haushinta, yaso ya mata dukan da yafi haka da Umma bata nan, amma yanzu yasan yana farawa kukanta zai jawo hankalin Umma, kuma yanzu ta gama mishi maganar marin da ya yiwa Ummi Aisha ranar.
  Mariya sai da tasha kukanta sosai sannan ta miƙe, ribbon ɗin kanta ta cire ta baza gashinta don yadda kan yake mata zafi sosai. Kayan jikinta ta cire ta wuce bathroom, shower ta sakarwa kanta ruwa ya fara jikata sosai musamman kanta da har ya fara ciwo.
  Tsawon mintuna kafin ta yi wanka ta ɗaura alwala ta fita, ta saka riga marar nauyi ta gabatar da magriba jin ana ta ƙira.
  Bayan ta idar ta cire hijab ɗinta don kanta a jike yake, ta baza gashin yasha iska. Kanta ta jinginar da gado ta lumshe idanuwanta da suka ɗan kumbura don kuka.
  Yanzun ma zuciyarta tayi rauni, kuka take son yi. Komai ya fita a kanta a rayuwarta, lokaci yayi da za ta cika burinta da mafarkinta ko zata samu salama da kwanciyar hankali a rayuwarta.
'Sai dai ta ya? Ta tambayi kanta.
"Dole sai da taimako wani ko wata don ita ɗin har yanzu ba ta zama cikakkiyar lauyar da zata tsayawa kanta ba."
  Ta faɗawa kanta tare da tsunduma tunani har lokacin idanuwanta rufe. Da sauri ta buɗe idanuwanta jin wanda zuciyarta ta ambo mata takai kokon bararta wajensa.
  Haka har dare ya shiga tana tunani a ɗaki ta ƙi fita, duk yunwar da yake cinta ta kasa fita gudun gamuwa da Yaya Haydar, sai dai ta sha ruwan tap na bathroom ta fito.
  Ƙarfe tara ta gabatar da sallar isha'i ta haye gado ta kwanta, tana mamakin ina Ummi Aisha ta shiga, ba ta ji ko surutunta ba balle motsinta, ta san da Haneefa tana nan sai ta kawo mata abinci har ɗaki, amma ita ma ba ta nan.
  Nan ta ji tsoro ya kamata ganin ita ɗaya a ɗakin za ta kwana, abin da tun da ta yi wayo ba ta taɓa bari Ummi Aisha ko Haneefa su barta ita ɗaya ta kwana ba.
  Ji take kamar ta fita ta nemo Ummi Aisha ko ta tafi ɗakin Umma ta kwana ko nasu Maryam, amma ta ka sa hakan don ba ta saba kwana a ɗakin Umma ba, hasalima basa kwana ko da wasa dukkansu yaran, gwara ma Ummi Aisha tana kwanciya wani lokaci.
  Tun tana zuba ido don jiran zuwan Ummi Aisha har bacci ya ɗauketa. Ga yunwa ga tsoro, amma da yake a gajiya take ga kukan da tasha tuni wani bacci mai nauyi ya kwasheta.

  A hankali ta ji ana shafa mata kirjinta cikin wani irin salo, motsi ta yi ta juya tana gyara kwanciyarta sai dai ji tayi tamkar ba a saman gado take ba. Hakan yasa ta sake juyi za ta yi magana ta ji bakinta a rufe gum.
  A tunaninta cikin mafarkinta ne da ta saba, hakan yasa ta fara shure-shure don ta farka amma sai ji ta yi an rirriketa da ƙarfi ana ci gaba da shafarta musamman kirjinta, hakan ya tabbatar mata da a gaske ne a zahiri yau komai yake faruwa.
  Cikin mugun tsoro da ya ziyarci zuciyarta da ilahirin jikinta ta ci gaba da turjewa, tana shure-shure da neman kwatar kanta, ta ka sa ihu don bakinta a rufe sai nishi take. Hakan da take tamkar ƙara ingizawa take, ba zato take ta ji an ɗaga doguwar rigarta sama.
Cinyoyinta ne suka bayyana duk da a duhu ne, Allah ya taimaka mata da pant a jikinta, hakan yasa aka sakar mata jiki aka fara ƙoƙarin jan panta nata ƙasa.
  Wannan damar yasa ta kai hannunta ta zare abin da aka toshe bakinta da shi, ba ta yi ƙoƙarin hana janye pant ɗinta ba ta daddage ta fasa gigitacciyar ƙara da ya saka mai cire mata pant dakatawa.
  Hasken wuta da aka fara kunnawa a gidan tare da tahowar takun mutane wajen yasa aka ɗagata tare da barin gurin da sauri. Mariya kuka ta sanya da ƙarfi ta janye pant ɗinta ta mayar.
   Yaya Haydar da Abba kusan tare suka iso wajen jin inda ihun ya fito, bayan su Umma sai Maryam da Khadeeja da sauran maza da suka ji suka fito su ma cikin tsoro.
  Mariya ganinsu yasa ta sakin wani ƙara ta sume a kwancen da take. Abba da Yaya Haydar har rige rige suke na isa wajenta cikin tsantsar mamakin me ya kawota nan, ga ta kuma birkice ga ta sume.
  Abba yana shirin ɗagata cikin tsorata Yaya Haydar ya hanasa ya ɗagata cikin jarumtar da ya sakawa kansa, cak ya ɗauketa ya nufi falon Umma da ita, a saman kujera ya ajiyeta ya ɗaura kanta saman cinyarsa. Hannunsa saman fuskarta yana ɗan bugawa alama ta farka.
  Umma da sauri ta ƙarasa dining ta ɗauki goran ruwa ta dawo, Abba ya karɓa ya buɗe ya yayyafa mata. Ko motsawa ba ta yi ba, hakan yasa Yaya Haydar karɓar goran ya tultula mata ruwan a fuskarta.
  Mariya numfashi ta ja a gigice tana neman miƙewa, Yaya Haydar ya riƙota jikinsa yana faɗin.
"Ke ki nutsu."

  Jin muryarsa yasa ta ɗan nutsu tare da kankameshi iya ƙarfinta. Bai hanata ba don yasan tana cikin tsoro ne amma da tuni ya janyeta. Luf ta yi tana sauƙe numfashi cike da tsoro.
  Ya kalleta yaga rigar jikinta duk ya manne a jikinta ya fito mata da jiki, kuma babu hijab gashin kanta duk ya hargitse. Idanuwansa ya ɗauke da sauri ya kalli ƙannensa ya ce.
"Ku je ku kwanta."

  Don tsoronsa yasa suka bar wajen. Yaya Haydar ya kalla Abba da Umma ya ce. "Abba kuma ku kwanta dare ya yi sosai."

  "Amma Aliyu me yake faruwa da ita? Dubeta ka ga? Me ya fito da ita cikin wannan dare? Ganta gaba ɗaya a hargitse take."
  Abba ya faɗa yana kallon Mariya cike da tausayinta. Shi kam ya so ayi maganar yanzu don jin me ya sameta a wannan dare.
  Umma ita ma ta ƙara da faɗin. "Gaskiya kam? Mariya me ya sameki?" Ta tambayeta cikin tashin hankali, ta rasa wani irin tunani za ta yi akan fitowar Mariya zuwa bayan ɗakunan su cikin wannan dare, abu kamar aljanu.
'Ko dai su ne.' Ta tambayi kanta tana ƙara kallonta.

  Mariya shuru ta yi ta ka sa magana, hakan yasa Yaya Haydar ɗagota yana kallon fuskarta yaga idanuwanta a runtse. Kallon su Abba ya yi ya ce. "Zuwa safe ku yi maganar."
     Daga haka ya miƙe yana miƙar da ita suka bar wajen, ita kam da ƙyar take tafiya don jikinta ciwo kamar wacce ta yi mugun dambe.
  Gefe ɗaya kuma mamakin Yaya Haydar ne ya cika ranta ganin ya ƙi maganar gaba ɗaya, uwa uba yadda ya yi wani bake-bake ya hana kowa ko tambayarta, sai ma kulawar da ya nuna mata.

#vote
#comment
[06/06, 7:28 pm] Pharty BB: GOBE DA NISA
Page 10
Na Pharty BB

Mariya gani ta yi Yaya Haydar ya nufi ɗakinsu da ita, da sauri ta tsaya turus cike da tsoro, ba za ta iya kwana a ɗakin nan ita ɗaya ba, gani take za a sake zuwa mata.
  Yaya Haydar kallonta ya yi ganin ta tsaya yaga kanta a ƙasa, murya a cunkushe ya ce. "Mene ne kuma?"
Chapter 13 · 0% Book details