← Book details Gobe Da Nisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 18

Sashe 10

Gobe Da Nisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Barrister Waliy bai nemi Mariya ba yau ma don yasan aikin da ya bata yana neman nutsuwa, duk da ya ce mata wani sati yake so, yasan kwazon yarinyar zai sa ta yi ko guda ɗaya ne a ciki.
Daren jiya bayan ya koma gida shi da Rumana suka shirya don basa dogon fushi da juna, sai dai yau da safe ma kamar yadda take gaishe Ammi haka ta sake yi duk da ta zauna a kan kujera.
  Waliy ya rasa ya zai mata, ya yi fushin ya yi magana ta kasa canza halinta. Duk da yasan Ammi bata nunawa yasan abin zai sosa ranta, musamman yadda su Radiyya suke nuna abin da Rumana take yiwa Ammi basa jin daɗi, basa mata rashin kunya don Ammi ta hana su ta nuna musu matsayin yayarsu take bayan haka matar yayansu ce, kawai daga gaisuwa sai gaisuwa yake haɗasu kamar yadda ita ma bata sake musu ba.
  Da safe haka suka fice kowanne ya nufi wajen aikinsa. Fitarsu ya ba Nabeela damar fita ita ma don fara gudanar da nasu shirin da suke addu'ar samun nasara.
...

  Barrister Aliyu Haydar a yau ya dawo bakin aiki bayan tafiya karatu da yayi na tsawon watanni takwas.
  Da dama sun shigo sun masa murnar dawowa da addu'ar samun nasara, ya amsa musu a sake duk da fuskar babu murmushi ko kaɗan.
  Samun raguwar mutane yasa ya fara duba ayyukan da ya tarar, ayyuka ne manya manya na shari'a.
***

   Ƙarfe uku da rabi Mariya tabar office ɗinsu don gujewa haɗuwa da Yaya Haydar. Cikin rashin sa'a tana fitowa da motarsa ta fara cin karo, ji ta yi tamkar ta koma don ta tabbatar yana ciki, amma haka ta daure ta ci gaba da tafiyarta.
  Har ta gifta motarsa ta nufa get ta ji wani mahaukacin horn, da sauri cikin bugun zuciya ta juya, ta ga babu kowa da yake yiwa illa ita.
  Wani bugu zuciyarta ta yi jikinta ya hau rawa, da ƙyar taja ƙafafunta ta nufi wajensa cikin addu'ar da yazo bakinta don kaucewa muguntarsa.
  Ta gefensa ta tsaya kanta a ƙasa, shi bai buɗe ba shi bai kashe motar ya fito ba, gudun ta yi laifi ya samu na mazgarta yasa ta ci gaba da tsayuwa har tsawon mintuna da take ganin sun kusa talatin.
Gaba ɗaya ta galabaita da tsayuwar, ta ji tafiyar ma ta kasa sai ta huta. Yaya Haydar salon mugunta ya iya kala-kala musamman idan ita zai yiwa.
  Sauƙe gilashin motar aka yi, hakan yasa Mariya ta sake yin ƙasa da kanta, don tana tsoron waɗannan manyan idanuwansa, tsoratata suke su fitarta a hayyaci.
  Maganarsa ce cikin muryarsa mai tsoratarwa ya shiga kunnuwanta.
"Tsabar rashin sanin kan aikinki ƙarfe uku da rabi za ki bar office? Da ma shirme ne ya kawoki nasan wannan ƙwaƙwalwar naki babu abin da ta iya. Don haka zan faɗawa Abba zan nema miki sallama."

  Babu shiri Mariya ta ɗago manyan idanuwanta ta kalle shi, suka haɗa ido ta ɗauke nata ganin uban harara da ya aika mata.
Hawayen da take ɓoyewa ne suka zuba, ba ta share su ba ta hau girgiza masa kai.
"Don Allah Yaah Haydar kayi haƙuri, yau ne kaɗai nayi saurin tafiya, wallahi ba zan sake ba."

  Bai kulata ba ya zuge gilashin motarsa yaja motar yabar wajen yana buleta da kura.
Mariya durƙushewa tayi a gurin, ta haɗa kai da gwuiwa tana fashewa da kuka. Da ma tasan idan Yaya Haydar yana ƙasar nan ba zai taɓa barinta ta yi wannan aikin ba balle har ta samu cikar burinta, tamkar wanda yasan tana da wata manufa na yin aikin ya dawo da wuri.
Kullum cikin kusheta da faɗin ba ta da ilimin yin wannan aikin yake, amma hakan bai saka ta sare ba sai ma ƙoƙari da ta ƙara don ta nuna masa za ta iya, amma yanzu akan ɗan abin da bai kai ya kawo ba yana neman rabata da aikinta da ta ci buri.
Tsayuwar mutum taji saman kanta, ba ta dago ba sai dai ta tsagaita da kukan, ƙamshin turarensa ne ya dameta wanda ya saka zuciyar kokonton ko shi ne. Hakan yasa ta ɗago da sauri suka haɗa ido, fuskar nan kamar kullum babu fara'a.
  Kanta ta mayar ƙasa ta share hawayenta, ta miƙe tana karkaɗe jikinta ta fara shirin barin wajen ba ta ce komai ba.
  Cak ta tsaya da ƙoƙarin barin wajen inda ta ji ya ce. "Biyo ni."

  Kamar ta fasa ihu take ji, shi ba ya duba halin da take ciki ne zai ƙara mata wani takurar, ya barta a yadda ya ganta.
  Amma ya ta iya? Haka tabi bayansa ta ga ya nufi wajen motarsa, ƙarasawa tayi ta tsaya ganin ya shiga ya kunna.
  Barrister Waliy ganin Mariya ba ta da niyar shiga yasa cikin tsawa ya ce. "Ni zan shigarki?"

  Da mugun mamaki ta kalle shi ya aika mata harara yana ɗauke idonsa cikin nata. Mariya cikin rawar jiki ta zagaya ta buɗe ta shiga, da ƙamshi da sanyi ta fara cin karo, ta lumshe lumshashshun idanuwanta ta buɗe.
Wani mugun fizga Waliy ya yiwa motar yana barin harabar wajen, sai da suka hau titi taji a dakile ya ce.
"Unguwarku fa."

  A hankali ta faɗa masa ya karkata kan motar. Sun yi nisa a tafiyar ta sake jin wata tambayar.
"Me ya saka ki kuka? An miki wani abun ne."

Girgiza kai tayi a hankali, sannan cikin sanyin murya tuna abin da ya faru tace. "Babu komai."

"Daɗin kukan kike ji ko sha'awar yi kika yi?"
Ya watsa mata tambaya.
Shuru tayi kamar ba zata ce komai ba, a hankali tace.
"Yayana ne zai saka a bani sallama a aiki."

"Waye shi?"
Ya faɗa da sauri yana katseta.
Wani yawu ta haɗiye na kuka da ya tare mata maƙoshi, sannan ta ce.
"Barrister Aliyu Haydar."

  Bai ce komai ba ya ci gaba da tuƙi, har zuwa unguwar su Mariya ta nuna mishi layinsu ya shiga ya kaisu har ƙofar gida.
Bayan ya yi fakin ta kai hannu za ta buɗe ƙofa ta ji a rufe, ta juya ta kalle shi taga ba ita yake kallo ba. Kafin ta buɗe baki ta yi magana ta ji ya fara faɗin.

#vote
#comment
[06/06, 7:28 pm] Pharty BB: GOBE DA NISA
Page 8
Na Pharty BB

    "Kar ki damu, ki fito aikinki." Barrister Waliy ya faɗawa Mariya, yakai hannu ya cire lock ɗin motar sannan ya juya ya kallonta.
   Mariya ta buɗe murfin motar za ta fita ta dakata, cikin sanyin muryarta ta ce."To na gode."
   Daga haka ta fita a motar, ba ta ko juya ba ta nufi cikin gida. Shi ma motarsa yaja yabar ƙofar gidansu.
...
  Kamar kullum da sallama ta shiga cikin gidan, sai dai ji tayi da komawa tayi don hango Yaya Haydar zaune a bakin balcony saman farin kujera, saman cinyarsa laptop yana dannawa.
  Ta san komawarta yin wani laifi ne, hakan yasa cikin tsoro da ya shigeta ta nufi falon. Tana isa wajensa ta durƙusa ƙasa saman gwuiwarta.
"Sannu da aiki Yaya." Ta faɗa kanta a ƙasa, ba ta saka ran zai amsa mata ba amma dolenta ta gaishesa.
Yaya Haydar da ya ji tamkar ya maketa yadda tazo ta sashi a gaba ta katse mishi aikinsa, ya ɗago ya wurga mata wani kallo ya mayar kansa kan laptop ɗinsa, tsaki ya buga cikin faɗa ya ce.
"Za ki bar kaina ko sai na canza miki kamanni."

Bai ƙarasa faɗa ba Mariya ta miƙe cikin sauri ta faɗa cikin falo. Nan ma da Abba ta ci karo zaune da yara babu Umma, ɗauke kanta tayi ta wuce ɗakinsu da sauri.
Abba da sauran yaran duk da kallo suka bita ganinta kamar a birkice, duk dawowar Yaya Haydar ya sake mayar da ita wata iri, ya sake canzata, kowa yana tsoransa amma na Mariya yafi nasu tsanani.
Mariya tana shiga da Haneefa taci karo zaune a gado, cikin sauri ta ƙarasa kusa da ita ta zauna tare da ɗaura kanta saman cinyarta. A hankali ta fara fitar da hawayen da take ɓoyewa cike da rauni.
  Haneefa wayarta ta ajiye a bedside drower, ta ɗaura hannunta saman kanta ta zare mata baby hijab ɗinta tare da fara shafa mata gashin kanta da yake ɗaure a parke babu kitso mai tsantsi da tsayi, tausayin ƴar uwartan yana ratsata don tasan ba abu kaɗan bane ya sakata kuka haka ba, duba da yadda take da haƙuri da kawar kanta a komai.
  Mariya sai da tayi kuka mai isarta ta fara sauƙe numfashi, ko ba komai ta ji zuciyarta tayi sanyi. Ta ɗago kanta tana kai hannu ta share guntun hawayenta.
  Haneefa ta bita da kallo har ta gama sannan ta ce.
"Me ya faru ne? Wani ya miki wani abu a wajen aiki ne?"

Mariya girgiza kanta ta yi, ta kalli Haneefa cikin muryarta da take neman yin wani kukan ta ce.
"Yaah Haydar ne zai nema min sallama a wajen aiki. Ni kuma kin san yadda nake son aikin nan, shi ne burina da mafarkina."

"Kin masa wani abun ne?"
Haneefa ta tambayeta don ita kanta shaidata ce yadda Mariya take son wannan aikin nata, dalilinsa ya canza mata rayuwa da burinta na zama likita zuwa barrister.
Girgiza kai Mariya tayi tana kallon Haneefa.
"Wallahi babu abin da na masa, kawai don saura minti talatin a tashi na tashi, kuma ni duk gudun haɗuwa dashi ne."
Anan ta faɗa mata har yadda suka yi da Barrister Waliy, ta ƙarashe maganar tana share hawayenta ta ce.
"Ina tsoron Yaah Haydar sosai, zai iya dukana idan na fita."

Shuru Haneefa tayi ita kanta ta rasa mafita, gaba ɗaya ɗakin ya ɗauki shuru sai ajiyar zuciyar Mariya da take sauƙewa. Haneefa ta kalleta ta ce.
"Kin yi sallah?"
Chapter 10 · 0% Book details