← Book details Gobe Da Nisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 18

Sashe 15

Gobe Da Nisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

  "Mene ne matsalarki." Ya tambayeta zuciyarsa tana son fassara kalamanta daki-daki. Abin mamaki hawaye ya gani zar sun zubo saman kyakkyawar fuskarta, ba tasa hannu ta share ba ya ji ta fara faɗin.
"Ban kai matsayin da zan tsayawa kaina ba, bani da kowa da zai taimaka mini daga cikin ahlina."

  Shuru office ɗin ya ɗauka sai ajiyar zuciya da Mariya take sauƙewa yake tashi, zuciyarta tayi rauni kuka take son yi sosai ko za ta samu salama. Tsawon shekaru ta samu ta fitar da abin da yake ranta, wanda take ɓoyewa yana damunta kullum.
  Barrister Waliy ya ka sa faɗin komai, yayi shuru tsawon sakanni biyar yana tattara bayanan Mariya cikin ƙwaƙwalwarsa guri ɗaya.
Numfashi ya furzar ya kalleta yadda take share hawaye mugun tausayinta ya rufe shi, ashe gaskiyarsa da yace akwai wani abun a rayuwarta. Yana ci gaba da kallonta murya a hankali ya ce.
"Zan tsaya miki zan taimaka miki, zan yi dukkan ƙoƙarina naga kin samu nasara. Mene ne matsalarki? Wace shari'a kike son shigarwa."

  Wani sanyi Mariya taji ya ratsa kahon zuciyarta, wasu hawaye masu zafi suka taru a idanuwanta. A hankali cikin rawar murya ta sanar mishi mafarkinta, burinta da kudurinta don samun cika alƙawarin da ta ɗaukarwa kanta tun ba ta kai haka ba, a ƙarshe ta fashe da kuka.
Barrister Waliy jikinsa har tsuma yake jin abin da Mariya ta faɗa, ga kukanta yana ƙara baƙanta ransa, zuciyarsa tana bugawa da ƙarfi  gaske, gani yake tamkar yanzu komai yake faruwa a gabansa.
  Cikin ɓacin rai a mugun fusace ya miƙe, ya zagaya ta wajen Mariya ya tsaya saman kanta yana dubanta yadda take kuka sosai. Cikin muryarsa mai tsorata mai sauraro ya ce. "Tashi muje."

  Daga haka ya juya ya nufi ƙofa, Mariya miƙewa tayi da ƙyar don yadda yanayin jikinta ya canza, ji take da ba ta faɗa masa ba, da ba ta fallasa ba ta ci gaba da ɓoyewa a ranta kamar yadda take yi.
Sai yanzu take tunanin me zai je ya dawo ya zo mata amma bakin alƙalami ya bushe.
Haka tabi bayansa bayan ta share hawayenta, sai dai kallo ɗaya za ka mata ka gane ba a nutse take ba, gaba ɗaya tamkar ba ita ba.
Barrister Waliy yana gaba tana binsa a baya har office ɗin register inda ake rubuta ƙara, a kujera ya zauna ya kalli Mariya ya mata nuni da ta zauna bai ce komai ba. Babu musu ta ja ta zauna suna facing ɗin juna.
Ya juya ya kalla register da duk ya tsure ganin Barrister Waliy da kansa.
"Cika takardar tuhuma."  Ya faɗawa register ya juya ya kalli Mariya da ta tsura idanuwanta a takardar da register yake rubutu, ya ci gaba da faɗin."Ki sanar mishi."

  Mariya da sauri ta kalli Barrister Waliy, ya haɗa rai yana mata wani kallo don ya hango tsoro a tare da ita wanda yake karyar da ita, har ta ka sa aikata komai tun farko.
Sunkuyar kanta ƙasa tayi ganin irin kallon da yake mata, cikin rawar murya cike da fargaba ta faɗa mishi, tana gama faɗa wasu hawaye masu zafi da suka taru a idanuwanta suka zubo, zuciyarta ta cunkushe wani yawu mai tauri ya maƙale mata a maƙoshi.
  Barrister Waliy duk yana lura da ita sai dai bai hanata kukan ba, yasan dole ta yi, irin wannan babbar masifar na bibiyar rayuwarka.
  Register dai yana ta rubutu, bayan ya gama ya sanarwa Barrister Waliy. Bai karɓa ba ya miƙe sannan ya dube shi, muryarsa har yanzu a cunkushe ya ce.
"Yanzu-yanzu ka aika. And da ni za ayi wasan."

  Register kai ya jinjina, duk da yasan barrister Waliy da ba wa aikinsa mahimmanci da kwazo akai ya lura na yau dabanne. Hakan yasa ya miƙe ya fita don bada saƙo.
  Barrister Waliy kallon Mariya yayi, cikin taushin murya kamar ba shi ba ya ce. "Tashi muje."

  Miƙewa tayi babu musu suka fita, office ɗinsa ta ga sun nufa, ta dakata da tafiya ta tsaya, ganin zai yi nisa bai lura da ita ba tabi bayansa a hankali.
  Ya rigata shiga, ita ma ta shiga sai dai bata zauna ba ta tsaya. Shi kam wajen fridge ya yi ya buɗe, ya ɗauki goran ruwa ya buɗe ya hau sha ko zuciyarsa za tayi sanyi, kusan shanyewa ya yi sannan ya dakata, ya ajiye ya ɗauki wani ya nufi wajen Mariya.
  A gabanta ya tsaya daf har sai da ta ɗago ta kalle shi, idanuwansa da suka ɗan canza kala cikin nata, da sauri ta mayar ƙasa. Shi ma ya janye nashi yana miƙa mata goran ruwan.
"Karɓi kisha."

  Hannu tasa hannu ta karɓa a hankali, cikin muryarta da ya fara dashewa ta ce. "Zan koma office."

Bai amsa mata ba yabar wajenta, ya zagaya ya zauna a kujeran sa yana jawo files ɗin da ta kawo mishi, ya buɗe sannan ya ce.
"Shiga ki wanke fuskarki sannan."

  Ɗago kanta tayi taga hankalinsa ba ya kanta, jiki a sanyaye ta nufi bathroom ɗinsa, kafin ta shiga ta ajiye goran ruwan a saman wani desk ƙarami sannan ta wuce.
Fuskarta ta wanke ta yagi tissue ta goge, tayi fiyau da ɗan ja abinka da farar fata musamnan saman hancinta, sai cikin idanuwanta da suka ƙanƙance don kuka har fatar ya kumburo kaɗan.
  Bayan ta gama ta fita, ta ɗauki ruwan ta buɗe tasha ta riƙe sauran tabar wajen, zagayawa tayi don fita ta ji ya ƙirata. Dawowa tayi ta tsaya kanta a ƙasa tana amsawa.
  Barrister Waliy yana ci gaba da duba abin da yake yi ya ce.
"Duk abin da za ki ji ki gani karki ki tanka. And maganar shaidun da za ki bani sai har mai laifi ya shigo hannu, kotu ta bamu lokacin zama. Zan karɓa sannan zan yi iya ƙoƙarina don sama mana nasara."

"Na gode, in sha Allah zan yi duk yadda ka faɗa." Mariya ta faɗa wani hawayen yana taruwa a idanuwanta.
  Kai ya jinjina mata sannan ya ce.
"Shikenan, ki je sai na nemeki."

  Mariya juyawa ta yi ta fita. Barrister Waliy rufe files ɗin ya yi ya jinjina kansa a kujera tare da lumshe idanuwansa.
Mugun tausayin Mariya ya rufe shi, yarinyar ƙarama da faɗawa wannan iftila'in, masifa tana bibiyar rayuwarta da karancin shekarunta. Duk daren Allah ba ta da kwanciyar hankali. Shi ya ga ƙoƙarinta ma da take ɓoyewa.

'Me mutane me suke nema a rayuwar su?' Ya tambayi kansa ya rasa me ba shi amsa, sosai yaga ƙoƙarinta na iya kawar da komai take rayuwa, duk da mai kula ire-irensa idan ya zauna da ita zai karanci yanayinta.
...

   Mariya tana fita office ɗinsu ta wuce, table nata ta wuce ta zauna tana sauƙe tagwayen ajiyar zuciya.
  Kamar an jefosa ta ga ya tsaya a saman kanta, cikin mugun tsoro ta miƙe ta mishi kallo ɗaya, ta ɗauke kanta ganin wannan mayun idanuwansa masu cike da bala'i waɗannan bata iya juran kallo suna kallonta.
Jikinta mugun rawa ya fara, cikin tsarkewar harshe ta ce."Yaah...Haydar me nayi."

  Zai yi magana wayarsa ta ɗauki ƙara, leɓbensa ya cije ya zaro wayar da niyar kashewa ya fasa ganin ƙiran mai muhimmanci ne.
Ɗauka ya yi ya kafa a kunne bai ce komai ba, da hanzari kuma ya ce.
"What? Ina zuwa."

  Daga faɗin haka ya juya ya fita bai kalla Mariya ba. Ita kam komawa ta yi ta zauna tana addu'ar Allah ne ya kuɓutar da ita daga muguntar sa, sai dai zuciyarta ta ka sa daidaituwa akan ƙiran da ya samu.
  Sai lokacin tsoron me za ta tarar a gida ya faɗo mata, tasan da wuya su yarda har su bata haɗin kai, abun zai zo musu a ba zata kamar yadda ita ma ta faɗa a gabar da bai dace ba, domin ba yanzu ta so ba sai nan da lokacin da ta ɗauka, amma komai ya canza.
  Haka ta wuni a wajen aikin ba ta tabuka komai ba, gaba ɗaya jikinta ya mutu, ga kukan da tasha ya saka mata ciwon kai. Ana yin sallar la'asar ta tattara ta bar office zuwa gida, tare da fargabar me zata tarar.
...

  Haka ɓangaren Barrister Waliy ma da tunanin halin da Mariya take ya wuni, da ƙyar ya daure ya yi wasu aikin don samun sauƙi nan da litinin, ƙarfe huɗu yabar office ya tafi gida.
Ba Rumana ba hatta Ammi ta lura yaron nata baya cikin walwala, sai dai babu wanda ya tambaye sa suka bar abun akan aiki ne.

   Finally Mariya ta faɗawa Barrister Waliy burinta, saura muma mu ji a gaba.
  Ko Abba da Umma zasu yarda su ba ta haɗin kai ta cika burinta idan suka ji?
Yaya Haydar fa? Wanda ya takura mata?
...

Free pages ya kusa ƙarewa Book 2 akan #300 First Bank, Fatima Bello Bukar. Evidence of payment 07037487278

#vote
#comment
GOBE DA NISA
Page 11
Na Pharty BB
Chapter 15 · 0% Book details