← Book details Gobe Da Nisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 18

Sashe 11

Gobe Da Nisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mariya kai ta girgiza alamar a'a, ta miƙe ta rage kayan jikinta ta wuce bathroom. Ruwa ta watsa ta ɗaura alwala ta fito, ta samu Haneefa ta fita a ɗakin. Wardrobe ta nufa ta buɗe gefen nata ta ɗauki simple doguwar riga ta saka, ko bra da pant ba ta saka ba ta ɗauki hijab ta saka, ta nufi wajen da sallayarsu yake a shimfiɗe.
  Sallar la'asar ta gabatar, tana cikin tahiya Haneefa ta shigo ta ƙarasa kusa da ita ta zauna a ƙasa tana ajiye plate da ruwan hannunta.
  Bayan Mariya ta idar ta juya tana kallonta, Haneefa ta tura plate ɗin da yake cike da abinci na semo da miyar zogale gabanta.
"Ki cinye tas kar ki rage, na san rabonki da abincin kirki kin manta balle naji labari wajen Ummi Aisha ko breakfast ba ki yi ba ki ka fita."

Mariya ba ta ce komai ba ta jawo plate ta fara ci cikin nutsuwa, sosai ta ci don ba ƙarya tana jin yunwa.
Ganin ta ci sosai yasa Haneefa gyara zama tace.
"Shi da Yaya Haydar waye oga a wajen aiki?"

Mariya barin cin abinci ta yi ta kalli Haneefa.
"Duk matsayinsu ɗaya, sai dai Yaah Haydar da ya ƙara karatun watanni takwas ɗin nan. Kuma a ƙarƙashinsa nake aiki."

Numfashi Haneefa ta sauƙe, sannan ta ce.
"Mafita biyu ne na samo, na farko ki ci gaba da zuwa aikinki kamar yadda ya faɗa miki tun da a ƙarƙashinsa kike aiki, idan kuma ba za ki iya ba sai mu faɗawa Abba ya yiwa Yaya Haydar magana ko zai bar ki."

Mariya kaɗan ta kware, ta ɗauki ruwa ta sha ra ture abin da ya tsaya mata sannan ta kalli Haneefa tana girgiza kai.
"Wallahi ba zamu faɗawa Abba ba, gwara naje kawai idan yaso ya min duk hukuncin da yaga dama."

"Hakan ya yi, sai ki tafi akan lokaci ki tashi akan lokaci, kar ki karya doka ko ɗaya."
Haneefa ta faɗa mata. Kai ta jinjina ta ce.
"In sha Allah. Ina Ummi Aisha na jita shuru?"

Haneefa miƙewa tayi tana faɗin.
"Maruka tasha a wajen Yaya Haydar, tana bacci a ɗakin Umma. Ya shigo falon tana ta zuba surutun nan nata, shi ko ya mammareta wai tana mace ba ta da kamun kai."

Shuru Mariya tayi tana mamakin halin yayan sun, ita da take shuru shuru ma yake cin zalinta yanzu kuma ya ce Ummi Aisha ta cika surutu. To shi wane irin mutum ne yake burge shi.
Tunani ya hanata ƙarasa cin abinci ta miƙe ta ɗauki plate ɗin, sai da ta leƙa ta tabbatar babu Yaya Haydar a falo sannan ta fitar plate zuwa kitchen ta dawo ɗaki.
Suna zaune su biyun har dare, bayan sun idar da sallar isha'i Haneefa ta dubi Mariya da ta idar tana lazumi.
"Wai sister period naki bai dawo ba?"

Kai Mariya ta ɗaga a hankali, cikin wani yanayi sannan ta ce.
"Shuru fa tsawon wata biyu."

"To idan ya wuce watan nan bai dawo ba sai ki je asibiti. Amma akwai discharge?"
Haneefa ta tambayeta.
Mariya kai ta ɗaga ta ce."Eh fa kowanne month ina gani."

Haneefa zama ta gyara tana fuskantar Mariya don so take ta fahimci zancenta, cikin nutsuwa ta fara mata bayani.
"Kin san shi discharge akwai na lafiya akwai na rashin lafiya, kuma kala kala ne. Vaginal discharge wani ruwa ne da yake fitowa daga tiny glands a bakin mahaifa da vagina, ruwan yana zubowa kullum ya wanko kwoyayin cuta da dead cells(matattun kwoyaye), don vagina ɗin ta zama clean and healthy(a wanke da lafiya) mai kyau.
Yawan ruwan da zai fita kullum ba ɗaya ba ne ga kowacce mace. Kalar shi da kaurin shi yana canzawa wanda yake depending on menstrual cycle.
Days 1-5 (kwana na ɗaya zuwa biyar) wannan ranakun menses(al'ada) ne ko fiye da haka a wasu matan.
Days 6-14 (kwana na shida zuwa goma sha huɗu) wannan lokacin na bayan al'ada mace za ta ga babu wannan discharge ɗin, in akwai ma kaɗan ne. A cikin waɗannan kwanakin ne kwan haihuwa zai fara girma.
Days 14-24 (kwana na goma sha huɗu zuwa ashirin da huɗu) sai discharge ɗin ya canza ya zama marar kauri, mai yauƙi ko santsi kamar ruwan kwai (not york). To da kwan haihuwa ya samu sai discharge ɗin ya canza, ya fara kauri yana zama fari ko yellow da ɗan ɗanko-ɗanko.
  Days 25-28 (kwana na ashirin da biyar zuwa ashirin da takwas) discharge ɗin zai rage fitowa daga nan kuma sai menses ɗin sabon wata yazo.
Wanan discharge ɗin da nayi bayani a sama haka ya kamata ko wace mace ta rinka gani kowanne wata, daga farkon zuwan al'adarta har ranar zagoyowar shi."

Mariya numfashi ta sauƙe bayan gama bayanin Haneefa, tana mamaki lallai komai sai da ilimi, murmushi ta mata sannan ta ce.
"Ina ganin hakan amma kin san a rikice nake ba lallai na gane ba tun da babu period."

Haneefa ma murmushi ta yi.
"Kar ki damu, ki je asibiti kawai."
Faɗin Haneefa cike da jimamin sabon al'amari na al'adar ƙanwarta da ya fara damunta.
***

Cikin sallama ya shiga falon nasu, falon tsaf dashi kamar kullum sai sanyi da ƙamshi yake, babu kowa kamar koyaushe. Saman kujera ya zauna cike da gajiya, hutun mintuna biyar ya yi sannan ya sunkuya ya fara zare sanar ƙafarsa.
Tsaf ya gama kafin ya miƙe ya nufi fridge, ya buɗe ya ɗauki goran ruwa ya buɗe yasha kusan rabi ya mayar sauran ya rufe ya mayar fridge yabar wajen.
Bedroom ɗinsa ya nufa bai tsaya ko'ina ba ya shiga bathroom ya watsa ruwa ya fito, ya buɗe wardrobe ɗinsa ya ɗauki jallabiya ya saka sannan yabar ɗakin.
Dining ya nufa ya zauna tare da fara ƙoƙarin zuba abinci, yana mamakin me ya tsayar da Rumana har ƙarfe biyar saura ba ta dawo a aiki ba.
Bai gama tambayar kansa ba ya ji buɗe ƙofar ɗakinta, da sauri ya juya suka haɗa ido. Tare suka sakarwa juna murmushi, ya mayar kansa kan abin da yake zubawa yana faɗin.
"Kina ciki da ma?"

"Eh, bacci nake motsinka ya farkar dani na ɗauka ma Ramlat ce."
Faɗin Rumana cikin kwababbiyar hausarta, a lokacin ta iso tana zama ta ɗauki spoon ta saka cikin abincin da ya zuba ta fara ci.
Waliy ma spoon ya ɗauka ya fara ci sannan ya ce.
"Ina ta tunanin ina kike."

"Allah My B."
Ta faɗa tana narke murya cikin shaukin son mijintan kuma yayanta.
Murmushi ya mata suka ci gaba da cin abinci cikin nutsuwa, haka suka kammala Waliy ya miƙe ya ɗauki wayarsa ya bar waje.

"Zan leƙa Ammi." Ya faɗa yana fita bai jira me za ta faɗa ba.
Ita ma ba ta damu ba ta kwalawa ƴar aikinta ƙira ta fito ta hau tattare wajen. Ita kuma ta koma cikin falo don jiran dawowarsa.

Waliy a falo ya samu Ammi da Nabeela sai shagwaɓa take zuba mata, gefenta Farah babu Radiyya.
Kujera ya samu ya zauna bayan sun amsa sallamarsa, ya hararo Nabeela yana faɗin.
"Bar nan ko na ɓata miki rai, kin girma ba ki san kin girma ba."

Baki ta tunzura gaba ta miƙe ta shiga ɗakinsu, Farah ta gaishe da shi ya amsa yana tambayarta.
"Ina Radiyya?"

"Tana kitchen."
Farah ta faɗa tana miƙewa ta bar wajen don su gaisa da Ammi da kyau.
Bayan wucewarta Waliy ya kalli Ammi yana tambayarta.
"Ammi ya gida? Fatan babu wani matsala?"

"Babu komai. Ya naka wajen aikin?"
Ammi ta tambaye shi cikin kulawa.
Kansa ya shafa ya ce.
"Allahamdulillahi sai godiya."

Hira suka hau taɓawa har magriba sannan ya mata sallama ya fita, ita ma ta miƙe ta shige ciki don aikatarwa.
Waliy daga nan masallaci ya wuce, bayan an gabatar da sallah ya koma ɓangaren su ya samu Rumana tana jiransa, kusa da ita ya zauna yana binta da kallo. Ita ma kallonsa tayi ta gyara zamanta tana ɗaura kanta saman cinyarsa.
A haka suka gama hiran su wajen ƙarfe goma sannan suka kashe komai suka wuce ɗaki don bacci. Bayan sun yi shiri suka bi lafiyar gado.
Rumana bacci ne ya kwasheta yayin da Waliy tunanin Mariya ya faɗo mishi. Yanayinta ya fara karantowa, farkon haɗuwar su da yanayin yadda take da saurin shiga tsoro, ga kuma ɗazu da abin da ya faru. Tabbas ba shuru shuru kaɗai bane ya sakata zama miskila duk da yanayinta ba mai son surutu ba ce, akwai wani abun a rayuwarta da yake damunta.
Numfashi ya furzar ya sake rumgume Rumana, baccinta take hankali kwance kamar babu wani abu da yake damunta. Yau tsawon sati bai nemeta ba, ko da zasu shekara haka yasan ba za ta nemesa ba wanda ya rasa dalili. A haka bacci ɓarawo ya sace sa.
***

Da safe Abba yasa aka sake zaman cin abinci a tebur, nashi tunanin haka zai sake haɗa kan yaransa. Yaran kamar su yi kuka, har da masu karyar ciwo irinsu Ummi Aisha don ba ta manta marin jiya da ya saka mata ciwon kai ba, sanin bata da lafiya yasa Umma barinta.
Gaba ɗaya suka haɗu a dining ɗin, Abba ya kalli Mariya wacce gaba ɗaya a takure take yasa ta miƙe ta zuba musu abinci shi da Umma da Yaya Haydar.
Kamar ta fasa ihu haka ta miƙe ta zuba musu, sai dai Yaya Haydar ta ka sa zuba masa abinci ta haɗa masa tea ta ajiye kamar yadda jiya ya bata umarni. Tana ƙoƙarin zama ya buga mata tsawa.
"Ɗauke ki shanye tas, uban wa zai sha miki."

Mariya jiki na rawa ta ɗauka ta fara sha duk zafinsa, Abba ya kalle shi ya ce.
"Kai kuma ai ba haka ake ba, ka faɗa mata tun kafin ta haɗa."

"Abba ai ba ta tambaye ni ba."
Ya faɗa yana kallon Haneefa da yake mata kallon ita kaɗai ce mai ɗan hankalin cikinsu ya ce.
"Ke tashi ki zuba min abinci."
Chapter 11 · 0% Book details