← Book details Gobe Da Nisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 18

Sashe 4

Gobe Da Nisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

  A hanzarce ta juya taga Barrister Waliy tsaye a bayanta, suna haɗa ido ta ɗauke nata shi ma ya janye nashi yana barin wajen, dama wucewa yazo yi don zuwa meeting ya ga office ɗin a buɗe ya leƙa ko akwai wani a ciki.
  Mariya cikin sauri tabi bayansa don ba sanin ina za ayi tayi ba, kuma sam bata da labarin meeting ɗin sai dai idan yau da safe suka haɗa.
  Babban compress room taga ya shiga, ita ma tabi bayansa ta shiga bakinta ɗauke da sallama ƙasa ƙasa. Jama'a ta tarar a wajen har da wanda bata sansu ba a ma'aikatar, manyan baristoci da suka jima a aikinsu, alkalai har da su register, ga sabbi irinta. A cikinsu ta samu guri ta zauna cikin sauri.
  Tamkar ita ake jira ta zauna gurin ya ɗauki shuru. Barrister Hamza ne ya miƙe ya fara jawabi da musu sannu da zuwa, tare da karfafa musu guiwa akan aikinsu su jajirce sannan kar suji tsoro ko shakkar kowa. Haka ɗaya bayan ɗaya manyan suka gabatar abin da zasu yi.
Barrister Waliy shi ne a ƙarshe.   Cikin muryar nan nashi mai saka tsoronshi a zukatan jama'a ya fara nasa jawabin.
 Mariya duk yadda taso jurewa karta kalle shi kasawa tayi, a hankali ta ɗago kanta tana kai idanuwanta gare shi.
  Tamkar walkiya haka ya hango fararen idanuwanta suna kallon sa, kallonta ya yi suka haɗa ido. Mariya da sauri ta ɗauke idonta ta sunkuyar ƙasa jin yadda zuciyarta ta buga.
Barrister Waliy ma janye nashi ya yi yaci gaba da bayaninsa.
Awanni uku aka ɗauka ana abu ɗaya wanda duk su Mariya ake ƙarawa sani a fannin aikinsu a matsayinsu na sabbi. A wajen aka raba musu abin ci da abin sha aka ajiyewa kowa a gabansa, ɗaya bayan ɗaya kowa ya fara ɗauka yana sha.
  Mariya kasawa tayi ganin uban jama'ar nan ta ɗauki abu tasha, ji take ai zata kware.
Haka aka gama taron wajen ƙarfe sha biyu saura sannan aka sallame su, kowa ya miƙe ɗauke da abin da bai ci ya fita. Mariya kasa ɗauka tayi, tana miƙewa ta juya ta fice.
Duk abin da tayi idanuwan Barrister Waliy akanta, daga jiya zuwa yau ya karanceta tsaf, babu abin da yake hangowa tare da ita sai miskilanci zalla.
Miƙewa ya yi daga inda yake ya nufi inda ta zauna, hannu yasa ya ɗauki abubuwan da babu abin da ta taɓa ya fice a compress room ɗin. Office ɗinsa ya wuce kai tsaye, bayan ya shiga ya ajiye snack ɗin hannunsa saman tables sannan ya zauna. Landline na office ɗinsa ya jawo ya yi ƙira.
...

  Ƙara ne ya cika office ɗinsu na landline, dukkansu sun tsorata don ba a taɓa ƙiransu ba. Kafin ya yanke ɗaya namiji ya miƙe ya ɗauka da sauri yana kafawa a kunne, sallama ya yi a hankali kamar mai tsoro.
  Daga can ɓangaren Barrister Waliy jin muryar namiji ya amsa sallamar ya ba shi umarni.
"Ka turo min waccan mai white hijab, Barrister Waliy ne."

"Ok sir."
Ya faɗa yana zare wayar jin ya kashe. Wajen zamansa saurayin ya koma, ya dubi matan ciki yaga banda Mariya babu mai baby hijab fari, sauran gyale ne sun yi rolling, hakan yasa ya gane ita yake nufi.
"Barrister Waliy yana ƙiranki mai hijab."

Mariya da sauri ta ɗago kanta jin abin da ya faɗa sanin itace kaɗai mai hijab. Taga ya nuna mata landline yace.
"Yanzu ya ƙira kina ji."

Ɗauke kanta tayi don ba za ta musu ba don taji ta gani, miƙewa tayi ta fita bata ɗauki ko handbag ɗinta ba balle files din da ya bata. Tasan akan case din da ya bata kaɗai zai tambaya, ita kuma zata sanar dashi bata gama ba.
  A haka ta ƙarasa office ɗinsa, da bismilla ta ƙwanƙwasa ƙofar tana dakatawa. Taji ya bata umarnin shiga, a hankali ta murɗa handle ɗin ƙofa ta shiga da sallama.
A can ƙasan makoshi ya amsa mata, ba dan ta kasa kunne ba kuma babu surutu ba zata ji ba. Ƙyam ta tsaya kanta a ƙasa ita ma cikin murya ƙasa ta ce.
"Gani Sir."

Bai ɗago ba daga rubutun da yake, ya ce."Kwashe waɗannan kayanki."

Sai lokacin Mariya ta ɗago kanta takai idonta kan kayan da yake faɗa, nan ta yi tozali da abin da aka raba musu ne na ci da ta bari. Kasa motsawa ta yi balle ta ɗauka.
Jin shuru yasa Barrister Waliy barin abin da yake yi ya ɗago ya kalleta, suka haɗa ido ta yi saurin ɗauke nata. Kallon daƙiƙa ya mata ya ɗauke kansa, duk yadda ake cewa yana da miskilanci yarinyar nan ta dama sa, yana mata magana kuma yasan taji amma ta ƙi ko motsi.
'Ko dai tana da matsalar kunne.' Ya tambayi kansa a zuci, a zahiri kuma cikin ɗaga murya ya ce.
"Kar ki bari na tashi."

Jin tsawar da ya yi yasa Mariya ɗagowa a tsorace, ta kalli kayan sai lokacin ta buɗe baki cikin sanyin murya ta ce.
"Me zan yi dashi to?"

"Ki zubar."
Ya faɗa yana buga tsaki iya ƙarfin, haushin kansa ne ma ya kamasa da ya ƙirata ta ɗauka, da ya sani ya bari a wajen ko ya kyautar.
Matsawa Mariya tayi tasa hannu ta ɗauka, ta juya tana barin wajen ta fita a office ɗin. Tsaki ya buga yana cigaba da yin aikinsa.
...

  Mariya tana fita office ɗinsu ta koma, bayan ta ajiye kayan hannunta ta zauna ta zubawa kayan ido. Mamaki take ashe yana kallonta ta kasa cin komai.
'To kuma me zai damu kansa sai taci.' Wani sashe na zuciyarta ya tambayeta.
'Gudun yin asara?' Ta bawa kanta amsa, da sauri ta girgiza kanta ganin tamkar yafi ƙarfin hakan, ba shi kaɗai ba dukkan manyan gurin sunfi ƙarfin asarar abin dubu biyu.
Ƙiran sallar azahar da aka kwada ne ya shiga dodon kunnenta, a hankali tabi har aka idar, bayan an gama tayi addu'a, ta ɗauke kayan ta buɗe drawer ta ajiye ta miƙe ta fita.
  Masallaci ta nufa tayi sallah ta dawo, bata shiga cafeteria ba ta koma office. Bayan ta zauna ta buɗe drawer ta ɗauki snack ɗin ta fara ci.
  Kasancewar babu yawa yasa ta cinye tas, sai drinks ɗin da ta rage kaɗan, sai lokacin taji daɗinsa cewarta yau ta huta da zuwa siyan abinci. Bayan ta ƙoshi ta fara aikinta, sai dai duk yadda taso rubuta tambayoyi ta kasa dole tana buƙatar zuwa wajen mai ƙara.
  Barin abin da take yi tayi ta kalli agogon hannunta, uku saura ta gani. Tana da lokaci kaɗan, daga nan ma za ta wuce gida ba sai ta dawo ba, tuna haka yasa ta miƙe ta ɗauki files din tare da handbag ɗinta ta fita. Da kallo ƴan gurin suka bita dashi suna mamakin halinta na rashin son magana, wasu hakan ya burgesu yayinda wasu haushi taba su.
  Mariya bata ma san suna yi ba domin tuni ta samu ficewa a court ta tari napep, bayan ta faɗa mishi stations da zai kaita ya yarda ta shiga yaja. Har ƙofar ya kaita ta sauƙa ta biyashi sannan ta wuce ciki.
  Da sallama ta shiga wajen, suka tareta cikin girmamawa. ID card ɗinta ta nuna musu ta gabatar da kanta, tare da neman Isah Hamza wanda aka kama sati ɗaya da ya wuce bisa zargin sata, lauyansa ne ya turota za ta masa tambayoyi.
  Babu ɓata lokaci suka yarda, DPO yasa aka fito dashi aka basu guri. Bayan sun gaisa Mariya ta nemi ya faɗa mata gaskiya, tsaf ya sanar mata. Cikin hikima Mariya ta cigaba da mishi tambayoyi yana bata amsa tana rubutawa, a haka ta tsinci abin da za ta samu. Ganin lokacin yaja ta miƙe tana faɗin.
"Na gode Malam Isah. Zan iya dawowa kowanne lokaci don wasu tambayoyin."

"Ni ne da godiya, ki ƙara yiwa oga godiya bisa dawainiyar da yake dani."
Faɗin Isah don ko ahlinsa sun banzartar dashi, abokansa ne suka yi shiga da fice suka samu damƙawa Barrister Waliy case ɗin domin ya tsaya mishi bisa zargin da unguwa ake mishi yana musu sata. Duk da yana matsayin abin zargi hakan bai hana Barrister Waliy kin kula dashi ba.
Murmushi kawai Mariya tayi ta yiwa ƴan waje godiya ta fita. Napep ta tara ta shiga ya nufi gida da ita, bayan sun isa ta sauƙa ta biyashi ta shige gida.
  Yau babu motar Abba alama baya nan, numfashi ta sauƙe taji wani nutsuwa ya sauƙa mata. Cikin falo ta wuce ta samu ahlin gaba ɗaya suna zaune a falon.
  Sallama ta musu, ta durƙusa ta gaishe da Umma. Cikin fara'a tana kallonta ta ce.
"Sannu Mariya. Ya aiki?"
Chapter 4 · 0% Book details