← Book details Gargada So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 98

Sashe 78

Gargada So Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Dudda Baba baiga sakon ba but ayanda yaga Khaleel yasan Ni’ima tayi wani abu ranshi inyayi dubu yabaci tsabagen bacin rai yace “muje ka shiga gidan kacimata mutunci ba anan waje zan kiramaka itaba, ai gidana nakane ban maka iyaka da ko’ina acikin gidannan ba, muje” Baba yayi gaba Khaleel yabishi abaya suka shiga cikin gidan ko’ina a gyare ta buga sallama gaban dakin Hawwa, Ammi ta amsa yace “da mijin Hawwa nazo Zainabu” Hawwa dake zaune daga ita sai dan rigan bacci tana danna wayanta dasauri tadauki hijabi tasaka dark blue har kasa, ita dama Ammi da hijabi ajikinta Ramla kuma na kitchen tana aiki dasauri Ammi ta tashi da fara’a tace “bismillah bismillah kushigo” shigowa Baba yayi Khaleel biyeda shi abaya, kan Khaleel na kasa yace “ina kwana Mom” “muntashi lpy Khaleel” ahankali Baba yace “biyoni Ammi” binshi Ammi tayi suka fice daga dakin tareda maido musu da kofan suka rufe, Khaleel yazuba hannu a pocket nashi yana kallon Hawwa dako dagokai batayi ta kalli inda yakeba, kaman ma batasan da mutum awajen ba, Babu wasa kan fuskanshi rai abace yace “wacece ke tareda ke jiya a office?” Batare da Hawwa ta kalleshi ba tace “da wanda nake tare, ko wanda nai magana, ko wanda nagani a office is none of your damn business” ran Khaleel abace ya daka mata tsawa da saida dakin ya amsa. “Nace dawa kike tare jiya an office!”? Dagokai Hawwa tayi adan tsorace sabida yanda yayi mata tsawa ta tabbata anji a tsakar gidan, tashi tayi daga gadon ta taho inda yake dasauri dan bataso su Ammi suji tanamai ihu suhau mata fada akanshi, hakan yasa tace “who do you think you are kanamin ihu aka?” Ran Khaleel abace yanunata da hannu yace “dawa kike tare an office jiya?” “My friend!” Hawwa ta amsa kai tsaye ganin yadameta da tambayan, cikeda jin haushi tace “I was with Ni’ima me akayi? Sabida an auramin kai saina tambayeka kafin naga kawata konai magana da kawata”? Wani irin fizgota Khaleel yayi yakai hannunshi zuwa wuyanta ranshi abace yace “what is so special about that witch of a woman da kin kasa hakura da ita? Are you a lesbian!? Are you really into girls?”

Ja idanun Hawwa suka soma yi tafara dukan hannunshi hakan yasa yasaki wuyanta tadanyi tari kadan sannan ta kalleshi tace “da aurenka gwara zama da Ni’ima! At least ita bata living wayward life irin naka!”Radadi zuciyan Khaleel yafara sai kawai yakara fizgo Hawwa yakama kafadunta ya matse yana kallon cikin idanunta zuciya yakaimai wuya da kishi kai da komi ma ganin yanda Hawwa ke son Ni’ima yace “idan nakara ganin ki da yarinyar nan i will killl her! I will ruin her life! I will make her life a living hell you know me so well to know duk abinda nakeso nayi sainayi, stay away from that witch evil vile woman inba hakaba saina kasheta!”
[10/6, 10:39 AM] +234 706 565 5343: EPISODE 5️⃣7️⃣

Ayanda yau taga idanun Khaleel saida Hawwa ta tsorata wlh, bata taba ganinshi haka ba, yanda ranshi yakai ga baci yasa kawai ya turata yajuya yabude kofa yafito Baba da Ammi na tsakar gidan sunyi charko charko a tsaye, yama kasa kallonsu sabida baison suga kwayan idanunshi yawuce zaure da sauri Ammi tabiyoshi daidai ya shiga zaure tace “Ibrahim!” Chak Khaleel ya tsaya batare daya juyoba, dasauri Ammi ta taho tazagayo ta gabanshi sai kawai Ammi tasa hannu takamashi ta zaunar dashi kan bench dake zauren ahankali yazauna sai kawai yakai hannayensa biyu yarufe fuskansa yafuzar da iska masu zafi kaman zai kama da wuta sakonnin nan nacimai rai, ahankali Ammi tace “it’s okay ya isa Khaleel ya isa” sauke hannunshi yayi ya gyadamata kai ahankali yace “thank you Mom” anatse Ammi cikin hikima tace “can you show me sakonnin da aka turamaka game da Hawwa”? Araunane ya girgiza kai yace “Mom banso kowa yagani, sirrin matana ne I can’t show you banso kumata wani kallo” kirji Ammi tanuna tace “nine mahaifiyar Hawwa, show me Ibrahim idan akwai abinda yakamata namaka bayani zan maka, banso ku fara aure da zargi ko kokonto aranka, ayanda abin ke tafiya nan gaba hala za’a iya maka sakonnin dayafi wayan nan daci ma da tada hankali ma, so show me” Allah yasani sabida nauyin Ammi dayakeji ne yasa gently yamikama Ammi wayanshi daya bude mata message yace “5 numbers suka turo sakkonni, nasa anmin tracking akace lambobin wasu beggars ne, jiya danai magana da ita suna tare a office dinta, I believe somehow she took my number from wayan Matana batare datasan anyi ba” duka sakon nin Ammi tabi takaranta ran Ammi yama Ammi badadi sai kuma takaraji ta natsu da Khaleel tama aminta dashi gabaki daya, dawani ne da yasaketa yace yafasa aure but shi yazo kawai yayi warning nata kan zama da Ni’ima ne, ahankali tace “Khaleel wlh karyane kazafi akeso ama Hawwa! Babu wani abu na Hawwa daban sani ba, Ni’ima so take takashe auren ku, wlh Hawwa bata taba soyayya da Oganta ba, Hawwa maza tsofaffi ma basa burgeta, sheri ne diyata ba haka takeba, sai kuma abokin aikinta Abraham tabbas ta sanar dani yaron na bibiyanta shima bawai ya iya yafurta da bakinsa yana sonta ba, ai bata bashi fuska, yana mugun shakkanta, Hawwa bazata taba iya soyayya da wanda ta girma ba Khaleel kuma wanda yake ba addininta ba, saikuma na karshe sauran samarinta“ anatse Ammi tace “Ibrahim Hawwa na can be everything, stubborn, mafadaciya da sauransu amman Hawwa na ba mazinaciya bace! Dudda ta dade batai aure ba bata taba kallon zina as solution na matsalolinta ba, duk ina maka bayanin nan sabida ni uwa ce bazanga ana so akashe auren y’ata naja baki nai shiru ba, duka sakon nin nan karya ne Khaleel koda bakai trusting Hawwa ba trust me ni mahaifiyarta, I will never lie to you kaji”.
Chapter 78 · 0% Book details