← Book details Gargada So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 98

Sashe 29

Gargada So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wuraren 7 yashigo gidan a tsakar gida yaga Ammi tareda Ramla datake gwadama yanda ake buga kosai sun hada gawayi dan basu soya kosai a gas, ganinshi yasa Ramla tace “ina kwana Baban Yaseer” murmushi yamata yace “lpy lau” yace “ina kwana Ammi” murmushi tamai tace “an tashi lpy sannu da kokari fa Aliyu, Allah ya maka albarka, bari yanzun nan zan kawoma kosai nariga an dama kamu saina kawoma kayi karo kafin kashiga hanya” girgixakai yayi yace “no Ammi bazanyi kari ba bana kari da wuri yan sanda na barma motana chan hanyan kaduna dole nafita yanzu Ammi” yayi maganan yana ciro kudi daga aljihunsa daya samo a ATM fitan nan nasa a kujeran tsakar gida dake gefen Ammi ya ijiye kudin yace “aba Hawwa idan ta tashi, wannan kuma aba su mai girki” cus baisan sunan Ramla ba, hade fuska Ammi tayi tace “kaga dauki kudaden nan karna saba maka Baban Yaseer” dasauri yajuya yayi gate yace “Ammi nagode” yafice dasauri dudda har ranshi yaso yaga Hawwa kuma sarai ta tashi tun dazu har salla ma tayi kawai bataso ta ganshi ne kawai yasa bata fitoba, tanajin fitanshi tafito falo Amina dake gyaran falo na ganinta tai ihu sosai “Ramla Ya Hawwa ta tashi” tawani zo dagudu tai tsalle tafada jikinta Hawwa tai dariya sosai Ramla tasaki kosan datake ta rugo dakin aguje itama tai tsalle kawai Hawwa tai kasa suna kanta, Ammi ta shigo dakin ta kwadamusu duka abaya tace “Oya ku dagamin ita bance ku karyamin diya ba” kankamesu Hawwa tayi tace “Ammi I missed my babies” hararansu Ammi tayi tawucewarta tafito tashiga soya kosan da kanta tunda taga shirme suke Hawwa tafito tareda su tana Ammi wai ina su Hamza da Ahmadu? “Hamza na school, Ahmadu yace anjima zaizo da matarsa su gaidake, Baffan ku na dayan gidan sai gobe zai dawo nan amman hala anjima ki gansa” murmushi tayi ta karbi kosan tana soyawa su Ramla nabata labari she looks so happy Ammi tayi murmushi ganin ayanda idanunta sukadan kumbura jiya sabida kuka sun sauka sosai yanzu kaman batayiba.

Wuraren 12 Ni’ima taji ana bude gate, tunda tasan Hawwa bata taba taga miss call na Hawwa taki kiranta back ba sai yau, nor tai replying message nata, jiya tamata message shiru, da safen nan takirata sau biyu ba amsa sai tamata magana tace “call me idan kin dawo daga hospital Best, su Ramla nata tambayanki”.

Jin ana bude gate yasa ta tashi dagakan kujeran tawuce da sauri tashiga kitchen, ita kadaine agidan su Yaseer na school sai though 1 suke tashi on Friday, sallama taji yayo yashigo abu kawai taji yatokare mata zuciya tama kasa amsa sallaman, kofan bedroom nasu taji yabude ya shiga sannan tasauke ijiyan zuciya tashiga fito da flasks da plates tana ijiyewa a dinning tazauna a dinning din saikuma chan tamike tawuce bedroom din nasu ta zauna bakin gado tanajin karan zubam ruwa ba’a wani jimaba yafito daure da towel a waist yadan kalleta hada idanu sukayi tana kallonshi kaman yau tafara ganinshi dauke kai yayi da sauri yawuce wajen wardrobe nasu yace “wife ya gida? Su Yaseer basu dawo daga school ba”? Tana kallonshi kaman gunki tace “basu dawo ba tukunna” gyadamata kai yayi ya tsaya gaban mirror yadau mai yana shafawa yakasa wani maganan, kalulu ta hadiye a wuya tadan bude bakinta kadan saikuma tarufe sai chan kuma tace “ka kuwa sanar da Hawwa kana sonta?!” Dum! Haka maganan yadaki kunnenshi man daya diba zaikai jikinshi yashafa kasa shafawa yayi yajuyo yakalleta suka hada ido yace “wace irin magana haka kikeyi Ni’ima”? Mikewa tayi a fusace ta nunashi da hannu tace “don’t you dare lie to me, nasan son Hawwa kawata kake why are you hiding it? Eh maisa kake boyewa bayan ka kamu da mugun sonta” hade giran sama dana kasa yayi yadan dafe kanshi yace “kinsan mene? I don’t want your drama this afternoon I had a long journey I just want to sleep peacefully, dan Allah ki kyaleni I don’t know wat you are talking about” yajuya zai wuce yanda abu kecin zuciyan Ni’ima batasan sanda tai ihu ba tace “Namiji munafuki, namiji mara amana, namiji butulu! Aliyu I know everything! I know about hotunan Hawwa dake wayana da duk ka sace suna wayanka, I know kana stalking friend dina kana biye biyenta kana mata hotuna without her knowledge, how dare you kana karyata cewa sonta kake don’t be a coward, kaji be a man for once mayaudari kawai” “Ni’eematullah!” Baban Yaseer yakirata azafafe idanunshi sun kada sunyi ja, yace “yes yes yes I love Hawwa! Yes inason kawarki! Yes I love your best friend Ni’ima and so what!?” Hannu Ni’ima takai tadaura kan bakinta tana kallonshi completely heart broken hawaye masu jarababben zafi na saukowa daga idanunta, yace “do you think I’m happy with the fact that I’ve fallen in love with your friend? Kin dauka choice dina ne? Kokin dauka son Hawwa ya tambayi izinina? Why are you insulting me calling me names mena miki? Tayaya na yaudareki? Kinga na sanar da ita ina sonta ne? Ko kinga nayi wani abu ne? I love Hawwa yes and I also love you! Sabida I don’t wanna hurt you saisa all this years ban auri Hawwa ba, I can’t bring kaina into to hurting u that much, nasan yanda zakiji, I know wat kishi is! Yes I love Hawwa, and I also love Ni’ima, nima I don’t know mesa Allah zai dauramin soyayyan kawaye biyu kuma best friends, I know this same reaction kikeyi maybe na gayama Hawwa ina sonta zatamin more than yours, so just let me be, ban miki komiba ban yaudareki ba, and bance zan auri Hawwa ba cus nasan bazata yardaba, but all I know is harna mutu bazan taba daina son Hawwa ba, son danake mata yawuce tunani na, when it comes to Hawwa banmasan me nakeyi ba, I just want her to always be happy, I want to protect her, and always be there for her and make her happy, that’s just it” yayi maganan yana komawa wardrobe yadauki kayan dazaisa yafice daga dakin, Ni’ima tafashe da kuka bana wasaba gwanin ban tausayi tana zubewa akasan dakin…….

TOH JAMA’A IMAGINE MIJINKI NA SON BEST FRIEND DINKI, YAYA ZAKIJI???

HOW WOULD YOU HANDLE THE SITUATION???

KAI YAYA ZAKIYI NE????

IDAN KECE NI’IMA MEZAKAYI KO YAYA ZAKIYI DA HAWWA???

THINK AND TELL ME🥰
[9/18, 5:03 PM] M Shakur: 💫GARGADAN SO💫

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣5️⃣

FOLLOW MY WATTPAD ACCOUNT AKWAI FREE COMPLETE NOVELS DAYAWA AWAJEN KUSHA KARATU💃

https://www.wattpad.com/user/MSHAKURworld?utm_source=ios&utm_medium=link&utm_content=share_profile&utm_campaign=invitefriends&wp_page=home&wp_uname=MSHAKURworld

Ni’ima kuka kawai take bana wasaba, tana ganin tunda aka haifeta bata taba feeling wannan kalan zafin da zuciyanta kemata yauba, for years sunyi aure itada Baban Yaseer basu taba having issues ba like babban issue haka, batada wani complain akanshi but yau yayi hurting nata kwarai, kalan soyayyan datagani a idanun Aliyu ko ita baitaba mata shi ba, duk soyayyan dazaisa kafara stalking mace kana bibiyan hotunanta harda na kusan tsiraici ma dan kayan bacci ne ba karaman soyayya bane, soyayya ce ma dakana bukatan kaga therapist, he is sickly in love with Hawwa that’s idan akwai word din, ciwon son Hawwa yake, yanzu Hawwan ta Baban Yaseer zaiso? They’ve been through so much together with Hawwa, Hawwa is her biggest support bazata taba manta sanda Hawwa tasayo mata form na school of Nursing takawo mata ba, sabida lokacin Babanta baida lpy basuda kudin daza’a saimata form agida haka Hawwa tadinga dinki tahada kudin tasayo mata form 5k takawo mata that day was the happiest day of her life, Hawwa tarakata taje tai entrance exam na shiga school of nursing din, dataci Hawwa was happier than her ma datai jarabawan, bayan 2days aka kirata zuwa interview still Hawwa tabita sukaje tajirata awajen tayi tafito suka tafi gida dagabaya aka saki admission taci an bata admission, babu kudin registration Hawwa tadinga dinki day and night, tasaida babban wayanta alokacin tasa sim nata akaramin waya takawo mata 30k itama Maman Ni’ima tasaida sarkanta da dankunne aka hada 20k daga wajenta aka hada mata taje tai registration da 50k, the first ever book da pen datai rubutu dashi a school of nursing Hawwa ta siyamata su, hawaye ta share tana tuna rayuwansu da Hawwa duk yanda mutum zaiyi tunanin friendship, kawancenta dana Hawwa yawuce haka, sabida kawance ne mai asalin amana, Hawwa harda Maman Ni’ima take fada akanta just like yanda take fada da Baba akan Hawwa tanajin haushinsa kan Hawwa haka sukema junansu wajen iyayensu, they supported each other like better half, kawance su babu ha’inci, babu kyashi ko rowa, babu bakinciki, they’re always happy for each other, dudda tayi aure Hawwa bata taba mata bakincikin wani abuba, datana da ciki wlh wlh ko Baban Yaseer mai cikin baikai Hawwa kula da ita ba, idan tana craving wani abu Hawwa zata iya barin aiki taje ta nemo takawo mata, yanzu haka yaranta su Yaseer sun fison Hawwa kan mahaifiyarta grandmother su sabida aminci da kaunan dake tsakaninsu, she’s just crying bitterly bamatasan ina zata saka kanta ba, kawai taji ta bama kanta tausayi bamatasan inda zatasa kanta ba wannan wani irin intertwine situation ne haka? Wani irin kaddara ne wannan? Ita da Hawwa started friendship ana maganan tun suna around 6yrs old cus primary one suka hadu, yanzu suna 30yrs, 20yrs plus friendship kifa kanta tayi akafanta tana shesheka tajiyoshi an budemai gate yafita tasan mosque zashi yau juma’a.
Chapter 29 · 0% Book details