← Book details Gargada So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 98

Sashe 56

Gargada So Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Gidan Mama
Jin parking mota a kofar gida yasa Mama dake kokarin shanya zani a igiya tace “waye yazo duka duka ko awa daya cikakke Ni’ima batayi da fita ba yo ko Aliyu ne”? Tana fadin haka tacire hannunta daga kan zanin datake kokarin shanyawa daga igiya tai wajen gate din nasu tana kokarin bude kofan aka turo Ni’ima ke shigowa ga fararen uniform nata ajikinta sai abaya asama dayake abude, ga wani katon envelope a hannunta sai jaka da wayanta da car key a hannunta idanunta sunyi jajir ga ruwa ruwa ma kaman tai kuka, faduwa gaban Mama yayi rass dasauri tace “lafiya naganki gida? Bayanzunan kika tafi aiki ba sai dare zaki dawo? Yanaga kaman kinyi kuka Meya faru”? Envelope din hannunta tadaura akan hannun Mama tawuce tazauna gaban dakalin dakinsu kawai tafashe da kuka mai ciwo da zafi, Mama ta kalleta saikuma hannunta yashiga rawa sosai ta bude envelope din da sauri ta zaro paper ciki ta yarda envelope din akasa ta iya karatu tadanyi makaranta bakinta har rawa yake tace “lICENCE REVOKED LETTER FRON NMCN” takasa karanta surutun data gani sai kawai ta taho wajen Ni’ima tace “ke meke faruwa fadamin bazan iya karatun nan ba tell me” da kyar harshenta har karyewa yake tace “NMCN shine Nurses and midwifery council of Nigeria, sune suka aikomin da letter nan ta asibitin mu wai Leadway hospital sun turamusu video evidence of ni Nurse Ni’ima nazo hospital ina threatening patient nasu da murder, they saw everything a video, and I’ve caused lot of unrest among other patients, some even had panic attack due to tantrums dina, so according to code of conduct Nurses represent life, hope, not threat and fear, plus attempt murder danayi dan haka sunyi revoking licence dina” bakin Mama bari yashiga yi sosai tace “m….me….menene revoking license Ni’ima? Yimin bayani dalla dalla ke” fashewa da kuka sosai Ni’ima tayi mai ciwo, cikin kukan tace “Mama revoking license yana nufin bazan kara iya practicing nursing a any government hospital ko any accredited private hospital ba, Mama infact any registered hospital bazan taba ita aiki dasu ba saidai irin banzayen local quack hospital wanda gwamnati batasan dasu ba ko da zamansu, kuma till further notice sukace babuma ranan dawomin da licence dina, asibitin mu kuma they fire me wai zan bata musu suna” hannu Mama tadaura aka tana kallon Ni’ima data fashe da kuka sosai cus she love her job tanason nursing, it has always been her dream to become a nurse, so taking her license jitayi kaman batada wani purpose kuma, kaman part of her is gone” share hawaye tayi tana huci tace “Mama kuma duk sabida Hawwa ne, nasan ita tasa asibitin suka bata footage din ta tura ma NMCN intentionally Mama, Leadway hospital have no idea ni nurse ce, sannan basusan dawani asibiti nake aiki ba, Mama aikin Hawwa ne wlh, tanada connection din, she did all of this to get back to me” takalli Mama tana huci tace “Mama I will make Hawwa pay for everything datamin wlh tundaga kan rabani da mijina, Mama sainaga bayan Hawwa! Yanda narasa Aliyu narasa soyayyan sa yadinga gayamin ya tsaneni, sannan yanzu narasa aikina, I will make Hawwa loose everything also! Mama na tsani Hawwa! She’s a curse arayuwana Mama! Nima saina zama curse arayuwanta” Mama na kallonta tace “to yanzu yazakiyi eh Ni’ima? Bakida aiki dawani kudi zaki dinga ci ga Aliyu yaki kulamu?” Murmushi tama Mama tace “inada yan kudi kuma kudi bazai taba gagarana ba saidai in ba Hawwa aduniya, don’t worry Mama” ijiyan zuciya Mama tasauke but ranta babu dadi Ni’ima ta tashi tashiga daki ta chanza kaya zuwa abaya tafito Mama tace “ina zaki?” Murmushi tayi tace “gidansu Hawwa” dasauri Mama tace “suka koroki fa?” Dan murmushi tayi tace “Mama kibar mafarkin nan saina dawo kawai”.

Hawwa da Ramla nafita, Baba da Aminu suma suka fice zuwa bank kai gold, Ni’ima na shigowa unguwan tai parking motanta taji dadin yanda bataga Baba ba, ijiyan zuciya tasauke takalli fuskanta ta side mirror ganin komi daidai yasa tabude kofan tafito tashiga gidan da sallamanta Ammi ce kadai a tsakar gidan tana wanke kayan Hawwa dana Ramla taga Ni’ima that’s the last person datai expecting taga agidan nan tsayar da wankin datakeyi tayi, Ni’ima ta shiga shigowa tana tahowa har inda Ammi take, babu wasa kan muryan Ammi tace “me kikazo yi agidan nan?” Dan murmushi kadan Ni’ima tama Ammi ta duka gabanta takai hannu zata karbi bahon wankin tace “kawo kayan na wanke miki Ammi” kul! Ammi tafadi azafafe dayasa Ni’ima ta tsaya chak, ahankali tace “Ammi kin shararamin mari haryau inajin zafin hannunki a kan kunci na baki hakura?” Ammi na kallonta tace “tashi kibar gidan nan I don’t want to talk” ahankali Ni’ima tace “wajen Hawwa nazo wannan dabanganta ba nasan batanan bari naje nazauna najirata” tawuce tadauki kujera tazauna a tsakar gidan Ammi tabita da kallo sai kawai ta dauke kanta yacigaba da wankin datake bata sake cemata uppan ba.
**

Faduwa gaban Hawwa yayi jin abinda Khaleel yace wanda har saida yagani yanda ta tsorata hakan yamai dadi kawai yadauke kai Hawwa ta kadakai cikeda karfin hali tace “ka gwada kaini hotel kagani!” Tai kwafa kawai tadauke kanta ta jingina da kujera tana zancen zuci, ada kafin tasanshi kamshin turarenshi namata dadi yanzu ko dazaran taji kamshin yana reminding nata of yanda takejin haushin sa da tsanan sa da kinsa, sunyi kusan 30min tafiya sannan sukakai wani building dataga an rubuta The couples dream world aka bude musu gate suka shiga parking sukayi wani babban mutum yafito sanye da suit zuwa wajen motan driver yafito yabude ma Khaleel tunda ba Salman yafito Hawwa naji tsohon na cewa “welcome to The couple dream world Sir, we are so honored and pleased to have you” dan gyadamai kai Khaleel yayi yajuyo tareda leko motan yamika mata hannu yace “Police girl mun iso hotel din let’s go” hannunta tasa ta kabar danashi azuciye tafito daga side nata da aka bude mata tazagayo tsohon yakara bowing yace “welcome to the couple world Ma’am” dan gyadamai kai kadan Hawwa tayi ranta abace, Khaleel yace “after you” gaba mutumin yayi shikuma ya matso dab kusa da Hawwa bata ankaraba taji yakama hannunta hade hannuwansu gam yayi Hawwa takalli hannun tashiga kokarin kwace nata tace “cikamin hannun” make mata kafada yayi kawai yajata, duk yanda Hawwa taso ta kwace hannunta takasa Khaleel sai tafiya yake abunshi driver yabisu da kallo dasauran mopol nashi, yau shakara kusan ashirin ina aiki dasu bantaba ganin Oga yayi kyau dawata kaman yar sandan nan ba, they look so great, Allah kasa itace sanadiyan gyaruwansa” shiga ciki sukayi Hawwa taga kayayyakin amare ne da ango ajere kaman irin su veeke james dasu xtrabrides datake gani a IG irin wajen ne, yana jerawa da ita ahankali batare daya kalleta ba yace “banso ki dinka bridal dress dinki da kanki kinji yarinya!” Yadan kalleta dauke kai Hawwa tayi, Khaleel yace “I want them to do it for us” murya kasa kasa itama Hawwa tace “dazakaji nawa dabaka kashe kudin nan ba cus they will be no any wedding” office aka shiga dasu dasauri wata yoruba woman ta taso dasauri tace “welcome Sir” kawai ta rungume Hawwa tace “welcome Ma’am, you guys makes a very very lovely couples congratulations”.
[9/29, 3:42 PM] +234 806 486 0007: EPISODE 4️⃣9️⃣
Chapter 56 · 0% Book details