← Book details Gargada So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 98

Sashe 49

Gargada So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da kallo kawai taji yafara kwanta mata arai itama ta tashi tashiga dakin Aminu ya kwaso sauran kayan yafito, Ammi takalli Hawwa data kirne fuska tace "lafiya naga ranki abace" dasauri ta gyara fuskanta tace "bakomi Ammi" hannu Ammi tamika mata tace "tashi mutafi gida to" ahankali ta sauko daga gadon Ammi narike da hannunta suka fito Khaleel na tsaye tareda Aminu yagansu sun fito duk yanda yaso yadena kallon Hawwa data haderai tadauke kai yakasa daga Ammi har Aminu saida sukaga kalan kallon da yakema Hawwa kaman zai hadiyeta da idanu, har wajen motan sukazo Hawwa tace "ina keken Aminu"? Dan sosakai Aminu yayi zaiyi magana Khaleel yace "I'm taking you home dakaina" yasa hannu yabude musu bayan mota yace "Mom shiga" ahankali Ammi ta shiga shikuma Aminu ya zagaye shiga gaba abinshi Hawwa ta kalli Khaleel da idanunta dahar sunyi ja, Ammi ta leko ta window ganin yanda take hararan Khaleel tace "shigo mana Hawwa" danne komi tayi sabida Ammi ta shiga taki rufo kofan yadanyi murmushi yasa hannu yarufe yashiga gaba ya kunna motan he can't even remembers d last time dayayi driving haka yaja motan su Salman na binsu abaya cikin wata Lexus. Aminu sai hira yakema Khaleel, adan hankali yace "me kake karantawa a school" Dasauri yace "computer science engineering but nagama project nakeyi" gyadamai kai Khaleel yayi baisan kodan shi baida siblings bane but he kind of love siblings nata barinma yanda yaga suna sonta and suna sonshi ahaka har gida parking yayi Hawwa tabude tafito azuciye Baba yace "oyoyo oyoyo" kawai ya rungumeta yace "mara lafiya yaya jikin eh patient" dan murmushi tama Baba yace "naji sauki" da gudu Ramlat tafito tana zuwa tai wajen Khaleel tace "Ya Khaleel oyoyooo sannu da zuwa good morning" kallon Ramla yayi kowama na wajen yayi saikuma yayi murmushi, sosai Hawwa ta tsare shi da idanu he looks so good dayana murmushin, he just loves yanda suka nuna suna sonshi, cikeda wasa yace "Ram......" dasauri tace "Ramla sunana" gyadamata kai yayi yace "nice name" zatai magana Ammi tace "ke kibar mutane su huta" Baba yace "zoka zauna Ibrahima" dasauri Hawwa tasaki hannun Baba tawuce ciki abinta su Ammi da Ramla suka bita sai Baba da Aminu suka zauna awajen, Baba ya kalli Khaleel yace "sannu da kokari Ibrahima Allah yabaka lada nagode da komi" dan sauke kamshi kasa yayi Baba yace "yau zan sanar da Hawwa zancen auren ku" ahankali yace "Ibrahima Hawwa matarka ce yanzu kaine keda iko da ita bani ba, Alhamdulillah tasami Ipy an salla mota daga asibiti ko yanzu kace zaka tafi da ita ban isa nace a'a ba" Baba yasake shiru yace "inaso ka sanar dani yaushe kakeso ta tare? Kanaso ayi taro ne? Zanso na gayyaci yan uwan marigayiya mahaifiyarta dake kauye da nawa yan uwan, yanda akai auren mudan sanar da mutane bikin suzo wannan shine ra'ayi ma amman kai me kakeso?" Shiru Khaleel yayi baitaba biki ba as far as public is concerned haryau anamai kallon mara aure ne dan ba'a taba sanar da bikinshi waje ba, hakanan kuma ya kalli Baba ya kalli siblings nata kawai sai yaji he wants to throw wedding for them, sister su batai aure da wuri ba is only right he lets them celebrate her, and one last final point is kodan ya kular da Hawwan yanuna mata he can actually get duk kalan macen dayakeso yasamu aduniya yanaso yayi biki ayi su dinner yayi kissing nata in public yatabata bayanda zatayi, wani, Kayataccen murmushi yayi yace "Baba inaso ayi biki, nan da 3weeks" Dasauri Baba yace "dubamana date Aminu" calendar Aminu yashiga yana duba date yace "July 24th kenan Baba ranan asabar" ahankali yace "Baba I will handle everything zan kawo katin biki da komi" yakalli Aminu yace "kome akeso kamin message" Dasauri Aminu yace "banda number ka" kiramai number shi Khaleel yayi yayi saving sannan yatashi yace "Baba natafi" Baba yamai murmushi yace "bye my son". EPISODE 4 Sosai Hawwa ke masifa aranta tana shiga cikin gidan, menene business din yaron nan da gidansu? She don't understand sun masan wayeshi kuwa, tana shiga gidan Umma tagani a tsakar gida tana gyara hatsi tana ganin Hawwa ta dauke kai Hawwa tawuce dakinta batare datace mata ci kanki ba, dakin kamshi Ramla tasaka turaren wuta, kwanciya tayi akan gado ahankali, Ammi tashigo tace "mezakici nadafa miki Hawwa?"Ahankali tadaura kanta kan cinyan Ammi tai shiru batamasan me bakinta keso ba, Ammi tace "bari zanje kasuwa sainamiki farfesu" gyadama Ammi kai tayi tace "Ammi kidauki ATM card dina akwai kudi" dan gyadamata kai Ammi tayi Ramla na shigowa dakin, Ammi tace "Ramla zauna da yayarki kome takeso kimata, bari natasa Aminu gaba muje kasuwa tare muyi cefane zan taho da flask ma asaka ruwan zafi banso daga yanzu kuna zagawa da ruwan sanyi kinjina baida kyau ma mace" gyadamata kai Hawwa tayi Ammi tadauki jakan Hawwan tazare ATM dan bawani kudin kirki takedashi ba, tanaso tasaima yarinyar abubuwa da yawa tace "natafi" atare sukace "saita dawo" tafice tna fitowa waje taga Baba da Aminu na magana dasauri Baba yadakata yace "Zainabu ina zaki"? Anatse tace "wai kasuwa zani Malam nadanyo cefane Hawwa tace zatasha farfesu kasan har yanzu bata iyacin abinci sosai, Aminu tashi muje ka kaini" dasauri Baba yamike yana rage murya yace "inataso muzauna muyi magana Zainab, to mutanen sun samin miliyan hamsin din sadakin Hawwa a account an bani gwalagwalan kuma amman na adanasu, kece mahaifiyar Hawwa inaso na zauna dake da ita mubata sadakin daganan sai mu karbi abinda ba'a rasaba mu mata kayan daki kekuma kiyi naki shirin kinfini sani dai" gadamai kai Ammi tayi tace "ba matsala Malam yau zamuyi maganan da daddare In sha Allah, Aminu tashi muje" tashi Aminu yayi daidai su Khadija na zuwa sunma Hawwa girki Baba ya dakatar dasu yace "ban kuma ce naji wani ya sanar da Hawwa zancen nan ba" Wucewa Ammi sukayi kasuwan, sun sayi kan rago, dadan yan abubuwan datakeso tama Hawwa girki dasu sannan tasiyo mata babban flask na ruwan zafi suna dawowa taga Hawwa ma na bacci tashiga girki Umma sai bambami take yanda yaran ta ke dakin Hawwa wlh suka shareta wajajen 3 Ammi tagama girkin sosai Hawwa taci takoshi sai yau ta iya taci abinci. Around 9 Hawwa na zaune kan gado tana duba wayanta tareda Ramla da yawanci ke tayata replying chats na yan wajen aikinsu dan kowa yaji tayi accident, Ammi nakan dadduma ta idar da salla but still tanakan dadduma tana jan charbi Baba yayi sallama yashigo dakin, da sauri dukansu suka dago kansu Baba yashigo yanama Hawwa murmushi yace "kinji sauki yarinyana? Wannan dakuka natsu ahaka me kuke da waya? Kinji sauki" Gyadamai kai tayi ahankali tace "eh Baba" kallon Ammi yayi dake shafe addu'a yace "kin idar Zainab"? Gyadamai kai Ammi tayi takalli Ramla tace "tashi Ramla je dakin Umma zamuyi magana da Hawwa" hakanan dan faduwa gaban Hawwa yayi wannan dahar suna kada Ramla waje maganan me zasu mata? Wani ciwo gareta aka fada a asibiti? Daidai lokacin Aminu yashigo dakin dawata yar jaka kaman ghana masgo amman bottega ne mai bala'in kyau Baba yanunamai gabansa yace "zoka ijiye anan" ijiyewa yayi Baba yace "zaka iya tafiya Aminu" sannan yayi gyaran murya yadauki kujeran dressing mirror yazo wajen katifan dab da Hawwa itama Ammi tazo dab da Hawwa tazauna kan katifar, Baba yakalli Ammi data gyadamai kai yayi gyaran murya yaciro wayansa yabude yace "Hawwa na aurar dake, ga sadakin ki nan" yanuna mata alert na wayanshi na 50M yace "miliyan hamsin da dirhamin gwal dari gasunan" ya jjjiga mata jakan gabanshi, bugawa kirjinta yafara tana kallon Ammi takasa magana badai Baba yaji haushin Ni'ima yace ya aura ma Baban Yaseer itaba, Baba na kallonta yace "Ba Baban Yaseer bane mijinki ba Hawwa, na aurar dake ga someone even better, wanda ya fisa, yaro mai kunya, yaro mai natsuwa, ga dattaku ga girmama na gaba dashi, sunan mijinki Ibrahim Khaleel" bugawa kirjin Hawwa yayi sosai Ibrahim Khaleel Ibrahim Khaleel waye kuma Ibrahim Khaleel? Kaman Baba yaji abinda take tambaya anatse yace "Mahaifin Noor! Wanda ya ceto rayuwanki yakaiki asibitinsa sannan yabiya masu motocin dakika bata garin hatsari" Wani irin zabura Hawwa tayi ta yunkuro daga jikin pillow data jingina dashi a bango tana kallon Baba maganganun da Khaleel yamata na dawo mata see you soon! Babu wacce nakeso da bazan iya samu ba, bakinta har rawa rawa yake tace "Pops Dasauri Baba da Ammi suka kalleta basu gane metake cewa ba arude tace "Baba wannan mutumin daya kawo yarsa jiya da daddare asibiti? Ammi likitan daya kawomu gida? Shi wai kuke cewa kun auramin?" Dasauri duk sukace eh Baba yace "ai yagayamin kusan juna kece kika ceto Noor da aka sace" hannu Hawwa tadaura saman kirjinta dake bugawa kaman zai fito dasauri, Baba yace "Hawwa" cikeda fushi Hawwa tace "Baba kasan waye Khaleel kuwa? Kunsan wakuka auramin? Eh Baba" shiru daga Baba har Ammi sukayi suna kallonta, zuciya ba dadi tace "Baba auri saki Khaleel yakeyi fa, dan shaye shaye ne Baba wih, dan giya ne Baba" tsayawa Ammi da Baba sukayi suna kallonta ganin basuce komiba yasa dasauri ta matso kusada Ammi dake kallonta tace "Ammi wih dan shaye shaye ne babu abinda bayasha, banda haka ga auri saki ya maida mata kaman riguna yacire wannan yagaji yasaka sabuwa, Baba ni koshine namijin karshe aduniyan nan bazan aureshi ba na tsaneshi, bantaba haduwa da wanda na irinsa ba, ko kadan baimin ba, kucemai banyin auren, Baba bazan zauna dashi ba" kallon Ammi Baba yayi, Ammi ma takalli Baba hankali tashe Baba yace "Zainabu anya Hawwa ita kadaine?" Dasauri Hawwa tace "Baba nataba maka karya ne? Baba wih Khaleel dan giya ne ga auri saki ni bazan taba yarda da auren nan ba gaskiya cus shi ba mijin aure bane" sosai Ammi ke kallonta saikuma ta kalli Baba tace "Malam gobe muje wajen malamin dakamin magana muma Hawwa ruqiya" turus saikuma yakalli Hawwa dake kallansu yace "Hawwa bakiso kiyi aure ne kin fiso kiyita zaman gida kawayenki na cimiki mutunci akan mazajensu"? Dafekai Hawwa tayi ganin Baba da Ammi basu fahimcetaba sun dauko magana daban, kaman zata fashe da kuka tace "Baba baku fahimce ni ba, bawai auren ne banaso
Chapter 49 · 0% Book details