← Book details Gargada So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 98

Sashe 46

Gargada So Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Ni’ima nawani irin numfarfashi ta kama Mama tace “Mama ina ganin jira” dasauri Mama tariketa gam ajikinta tace “zomu bar nan wajen” Mama na rike gam da ita suka shiga fita daga wajen batama gani da kyau she’s just feeling suffocated, gaban wani shago suka tsaya Mama ta zaunar da ita da sauri tana jinginata da bango tashiga shagon tasayo ruwa tazo tabata da kyar Ni’ima ta kurba kawai taji ruwan na mata daci abaki tofarwa tayi akasa kaman taci magani takalli Mama tace “Mama jinake kaman an daura dutsen ukudu akan kirjina, Mama ni Hawwa zata maida mahaukaciya? Ni Hawwa zata rainama wayau? A ina tasamo mai kudin nan bata taba bani labarinsa ba? Mama yaushe suka hadu? Yaushe har akazo ana maganan aure har ina ganinshi asibiti dazu danaje? Mama ita harta isa taboyemin abu nata eh”? Taba wani irin huci ta bubbuga kirjinta tace “Mama ni mijin nawa ya sakeni yau ita a aureta yau ni za’a watsama kasa a idanu? Mama tayaya Hawwa zata fini eh? Tayaya zata fini”? cikeda rashin jin dadi itama Mama tace “Allah yasani banso ba, ke kinga yanda nake alfahari da mai kudi kike aure kuwa Ni’ima? Dukfa cikin kannenki kin fisu goshi, kece mai auren mai kudi, kece wacce tai makaranta, mijinki yabaki mota kina gidanki flat mai kyau kina aiki a hospital, Amman yau duk sai naga Aliyu jaririne a inda masu kudi suke, yo ai duka duka arzikin Aliyun ma baikai miliyan hamsin na kudin sadakin Hawwa ba” wani irin shedanin radadin zafi Ni’ima keji aranta har wani sosa gaban riganta take ta saman hijabi, tadauka she will be happy tunda Hawwa tai aure at least yanzu Aliyu nata ne ita kadai but kuma ganin yanda mijin Hawwan yahadu ga dukiya, ga kyau, ga gata saitaji kaman ciwone gareta ya warke amman wani ciwon yafito dayamafi nada azaba, tana kallon Mama tace “Mama tayaya Hawwa zata fini aduniyan nan eh? Tayaya Mama? Akanme zatayi s’a haka ta auri dan gidan Mangal, Mama kuma bata taba fadamin tamasan yan gidan Mangal ba wlh, ai badaga sama yafado ba sun hadu ne somewhere somehow amman taboyemini dayike makirace ita yar boko datai kwantai, yaushe suka hadu har suka fara soyayya? Mama ni Hawwa zataciwa amana eh? Ni zata ha’inta ta yaudara? Babu wani abu nawa da bana gayamata fa Mama, amman ni taboyemin, ashe saisa tace ko mijina kadai yarage aduniya bazata aureshi ba sabida tasami wanda yafishi akomi, Mama did you realize abinda Hawwa tamin ko? Hawwa play with my intelligence, she belittle me, tabuga wasa dani tanunamin tafini iya mind games” tashiga shesheka tana huci jikinta har kyarma yake, Mama na kallonta itama duniya ta mata zafi tace “munafuka ce, ke bakisan yanzu kasami mai kudi boyewa ake ba’aso asani ba, ai Hawwa bata sonki kwadayin Baban Yaseer yasa ta tsaya arayuwanki” cikin wani irin murya Ni’ima tace “Mama tayaya zan bata auren nasa gidan Mangal da dan su tsaneta eh? Mama tayaya zanyi? Inaso na gayamusu yar iska ce Hawwa maza takebi duk yan sandan office dinsu sun kwanta da ita, Mama help me, yazanyi Hawwa bata chanchanci irin gidan nan ba, tafi dacewa da gidan wahala da gidan kaskanci, Mama bai kamata Hawwa ta auri mijin dayafi nawa karfi ba wlh Yazanyi Mama? Mama banso tasami cigaba arayuwa Mama ni auren ma banso tayi tamutu ahaka, sonake Hawwa ta wulakanta na ganta on her knees tana begging dina for something, Mama ta yaya zan lalata auren nan” kanta Mama tashafa tace “yanzu ai saikin fara koma mata sannan zaki iya bata auren, kibari nafara zuwa na sulhuntaku tukunna, kidena damuwa shikuma Aliyu zan kirashi ya maidaki” Gyadamata kai Ni’ima tayi, Mama tamike tace “muje” tashi tayi sai alokacin tamasan bata saka takalmi ba haka suka wuce ta shiga mota ta tafi.
**
Chapter 46 · 0% Book details