← Book details Gargada So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 98

Sashe 21

Gargada So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Knocking kofan tayi aka bata izini ta shigo, DIG ne kadai a office din yana duba some files yasa glasses a idanu yace “yauwa Miss Hawwa” saramai tayi tace “Sir” ijiye file din yayi tareda zare glasses dinsa yace “ease please” sauke hannunta tayi yace “you solved that case brilliantly Officer kudos” dan murmushi kadan tayi tace “thank you Sir, you trained me after all” murmushi yamata ba karya bane yana alfahari da Hawwa in this task force yace “yanzuma I have another case for you” kai tsaye tace “nakira su Hayatu ne Sir?” Hannu ya girgixamata yace “no ke kadai sukai requesting for” kallonshi tayi alamun bata gane meyake nufi ba, yace “I got a call from Excellency they can’t find wani bodyguard nasu and they want you to look into it suna tunanin anyi kidnapping dinsa shima so they want you for the job” kawai jitayi ranta yabaci gabanta kuma yafadi, tadai daure tana kallonshi batare datai magana ba, DIG yace “please kije and investigate, Hawwa bance kije kifara fada da yan gidanba, rayuwansu da namu ba dayaba, this people ba’a Nigeria aka haifesu ba a kasan waje sukafi rayuwa so don’t expect them to act like us, masu kudi basa tunani kaman yaku bayi irinmu, just do your work without interfering in affairs nasu, be professional about it and keep me posted, am I clear?” “yes Sir” Hawwa tafadi ranta ba dadi, hannu yakai aljihunshi yadan zaro kudi yan 1k kusan na 15k yace “gashi kisa fuel a car naki” hannu tasa ta karba tace “thank you Sir” kofa yanuna mata yace “zaki iya tafiya” juyawa tayi tafice, babu yanda zatayi harkan police dama duk wani harka daya danganci hukuma ba’ama Oga gardama koda yace ka fada cikin wuta ne dole you must obey, obey before complain yana daga cikin slogan nasu, office nata tawuce zama tayi kan kujera tareda dafekanta tadan fuzar da iska taja drawer tadauki wayanta da car key tamike tafito tawuce wajen motanta tabude tashiga taja tafita saida ko ta tsaya tasha fuel cus gidansu da nisa ahaka har takai gidan tsayar da motanta akayi security suka leko yace “Hello Miss wakike nema”? Anatse tace “DIG sent me here” magana yashigayi awaya kusan 5min sannan yace “booth please” booth tabude musu suka duba akai scanning motan sannan aka bude mata gate din da sauran gates din daidai tana shiga gidan kawai taji gabanta yafadi hakanan, wani arnen Lexus jeep tagani black a compound din tinted ga security awajen daidai yarufe back seat din yajuyo yanabin motan Hawwa da kallo, parking tayi itama tadan fuzar da iska tareda kashe motan ta kashe AC tadauki wayanta tana kokarin kiran DIG ta sanar dashi ta iso akai knocking glass na motan hakan yasa ta dagokai ganin security da uniform yasa ta sauke glass na window cikeda girmamawa yace “afternoon Ma’am, Yallabai yace kishigo mota he will brief you aciki meeting gareshi and he’s running late” the thing is batasan Baban ne ko yaron ke nementa ba dudda tasan yawanci manyan mutanen nan haka suke basuda time amman saita bisu yanzu haka? Motanta ta kalla hakan yasa security yace “you don’t have to worry about motanki Ma’am ko ina kike za’a iya kawomiki kokuma adawo dake har nan kidauki motan ki wuce” dan ijiyan zuciya ta sauke tace “okay” hakanan she’s feeling so uneasy, bude motan tayi security ya matsa gefe tadauki wayanta da jotter tanada pen makale a aljihu already ta maida kofan tarufe tamai key tasa key a aljihu, Salman sai kallonta yake baitaba ganin police mace da uniform yama kyau kaman itaba, she’s damn beautiful, gashi tai rolling gyale akanta abinta sai tai kaman balarabiya, dan kallonshi tayi, cikeda good etiquette yanuna mata jeep nasu yace “after you Ma’am” gaba tayi yana biyeda ita har sukai wajen motan daidai takai wajen motan ta tsaya Salman yataho yasa hannu ya bude mata motan kamshi mai bala’in dadi yafara mata sallama da sanyi kafin idanunta su sauka kan Khaleel dake zaune cikin motan yayi crossing legs yana sanye da Ralph Lauren polo custom fit oxford shirt white dayayi folding dogon hannun, as usual babu kusan botura 3 na gaban rigan bai makala ba kana iya ganin kirjinsa, yasaka AMI Paris logo track short brown, short din yau ma baikai knee ba adan cinya ya tsaya, kafafunshi sanye da slides na Yeezy brown suma ga kumbunan kafanshi farare tass agyare diddigenshi kaman kasha sabida yau fari tass yasha spa pampering, writs nashi daure da agogon nexus pro smart watch, yasaka Burberry brown shades dasuka mai shegen kyau yana zaune cikin motan comfortably yana rikeda wine glass da wine keciki yana kallonta kaman yau yafara ganinta, juyawa Hawwa tayi azafaffe bawasa ko nonsense kan fuskanta takalli Salma dake tsaye abayanta tace “mai gidan nazo gani ba dan masu gidan ba!” Tajuyo ta kalli Khaleel tareda nunashi da hannu cikeda cin mutunci tace “Babansa nazo gani!” Wow! Har kirjinsa Khaleel yaji sigan maganan Hawwan cus she stepped on his ego and pressed it sooo hard!
💫GARGADAN SO💫

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣0️⃣

FOLLOW MY TIKTOK ACCOUNT DAN SAMIN FIRST UPDATE NA NOVEL DIN NAN💃
https://www.tiktok.com/@mshakurr?_t=8pnC3XYCgvl&_r=1

Zafi kirjinshi kemai sabida abinda ta fadamai tamugun rainashi yarinyar, wlh baitaba haduwa da any of this creatures data rainashi ba like this girl in his 32yrs of life, but zaiyi maganinta, ko gezau baiyiba balle yayi wani alamu na zaiyi magana, cikeda girmamawa Salman yace “Excellency bayanan but he specifically made it clear kiga Yallabai on his behalf” da dan fushi kan muryanta tace “children like him manta sakon da aka basu suke” ba Salman ba har sauran security dake wajen da shi kanshi Khaleel din saida suka kalli Hawwa, ta kirne fuska tajuya tace “I need to check in with my Boss” tai maganan tana barin wajen motan tai chan gaba tana ciro wayanta tashiga kiran DIG ringing daya ya daga tace “Sir Excellency bayanan fa zan dawo” dasauri yace “ohh na manta ban gayamiki ba Mr Khaleel will attend to you, ki tambayi Mr Khaleel za’a kaiki wajensa kiyi magana dashi” wayan na kunnenta tadan juyo takallo motan dataga Khaleel yajingina abinshi da mota kaman ma bacci yake da dan damuwa kan fuskanta tadan rage murya tace “Sir naga Khaleel din wai saidai na shiga motanshi cus meeting zashi he will update me on our way” dasauri DIG yace “to kishiga mana, Senate president namu na bukatan service namu don’t ruin my reputation, kishiga tsoro kike duk rashin jinsa he can’t do nonsense with Nigeria asset, let’s take the case quick I have to go” ya katse wayan, zare wayan Hawwa tayi daga kunnenta tana kallon screen din gabaki daya zuciyanta bayamata dadi, ta tsaya awajen taki motsi Salman yataho yace “we are running late Miss” juyowa tayi takalli Salman da idanunta dahar sun kada sabida bacin rai sai kawai tawuce fuu azuciye kaman zata tashi sama, kai tsaye ta shiga motan ta zauna akan kujeran dake facing na Khaleel, Salman yazo yarufe musu motan ya zaga ya shiga gaba driver yaja motan mopol daya na gaba daya na baya suka shiga titi, dan ijiyan zuciya Hawwa tasauke no matter wat dai tasan ba kasheta zaiyiba with all this people around.
Tunda ta shiga motan taki dagakai ta kalli inda yakema tsabagen yanda batason ganinshi jiranshi take yagayamata abinda zai gayamata amman shiru. Tundaga boot na kafanta Khaleel ke kallo dake kyallin polish gwanin kyau har zuwa fuskanta, kusan 5min kallonta yake baya ko kyafta idanu, sannan yakai wine glass din bakinshi ya kurbe duka tass ya ijiye glass din yabude dan fridge na wajen yaciro kwalban wine yana budewa yashiga zubama kansa cikin wine glass, cikin murya datake adan shake mai bala’in dadi da zaki and calm yace “Hawwa Mamman Alhassan! Age 29, graduate of Bwari LGA school, BSC and MSC degree holder in criminologist, a police officer assign under a special Anti Kidnapping task force led by DIG, currently running PHD in same field, First daughter of crippled old man with 6 younger siblings, 4girls married, brother in uni last sis in boarding house at Minna, Mom died when you’re young, raised by step mom” dago kanta Hawwa tayi ahankali tadaura dara daran idanunta akanshi daidai yagama zuba wine din ya ijiye bottle din yadauki glass din da hannun dama yajuyo yakalleta kaman yanda take kallonshi, heart melting smile yasakin mata tareda nuna mata wine glass cup din yace “cheers” sannan yakai baki, ya akayi yasan everything about her like this daga jiya zuwa yau? Zare cup din yayi daga bakinshi yarike yana kallonta, danne duk wani tsoro Hawwa tayi tadanmai murmushin keta tace “wow I must be interesting! Wannan daga tsakanin jiya da yau harka haddace bio na” dan murmushin tayi tai bending head kadan like a little baby cikeda raini tace “interesting, tell me how many hours kabata akaina kana kokarin haddace all this? You don’t look like wanda keda saurin hadda” cikeda bakin iskanci Hawwa ta zaro idanu tadaura hannu abaki kadan tace “don’t tell me Pops boy baiyi bacci ba all night cramming information dina yake dan ya karanto mini first thing daya ganni today” baki zuciyan Khaleel yafarayi yadan fara huci, cikeda son ta cusamai bakin ciki tace “dama wat was I expecting from a jobless guy? You have nothing doing, so u have all the time dazaka dinga binciken background din mata” Kaman wuta haka Khaleel yaji maganan aransa amman saiya daure ya danne yana kallonta yace “a jobless guy that have the whole time in this world to put arrogant girls like you in their rightful place” murmushi kadan Hawwa tayi tace “kanka akeji, can you skip the talk and cut to d chase? Wani sako Babanka yabaka kabani”? Yatsine fuska Khaleel yayi saikuma yasa hannu yazare glasses na idanunshi ya ijiye a gefe ya juyo ya watsamata sexy mugayen idanunshi dakeyi kaman zasu kulle sabida bacci and bawani bacci yakeji ba yace “there’s no any bodyguard that’s missing, I just wanna play with your time and have some fun with you!”.
Chapter 21 · 0% Book details