← Book details Gargada So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 98

Sashe 43

Gargada So Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Zaunar da Baba Khaleel yayi kan gadon dakin Salman yashigo yabashi crutches din ya karba ya ijiye yawuce yafita sannan yadawo wajen Baba stethoscope dake office din yadauka ya makala a kunne sannan yadauki abun auna BP yazo wajen gadon yadan kalli Baba in very cute and dan shagwaba voice yace “Baba don’t pay attention to whatever she says” yashiga auna BP Baba duk Baba yana kallonshi, chan ya saurari pulse nashi da heartbeat sannan ya ciccire komi yace “jininka yahau kadan a little sleep da magani will help zansa akawo ma” yajuya zai fita ahankali Baba yace “Ibrahima!”Juyowa Khaleel yayi ahankali babu wanda yataba kiran sunanshi ahaka sai Baba, tsayawa Khaleel yayi gaban gadon gently Baba yace “kaima likita ne”? Ahankali Khaleel ya gyadamai kai yace “eh” gyadamai kai Baba yayi saikuma ahankali yakai hannayenshi dake rawa rawa yakama duka hannayen Khaleel yarike Khaleel ya kalli yanda yarikemai hannu yayi shiru, baki Baba yabude ahankali zaiyi magana saiya fashe da kuka irin na manya dinnan, Khaleel yayi shiru yana kallonshi sai kawai yaji he’s feeling bad, like really bad, he can’t remember the last time he felt this bad for anyone in his life, cikin murya mai raunin gaske dan maganganun Ni’ima sun taba Baba dudda bai nunaba yace “yau Ni’ima ta goranta mini, ta zageni, ta zagi y’ata duka agabana” cikeda damuwa Baba ya tsagaita kukan saiya kalli Khaleel yace “Ibrahima zuciyata batamin dadi ko kadan banmasan mesa nake gayama ba amman har cikin jinina nake jinka wlh, Allah ya dauramin kaunarka kaman danda na haifa” Baba yaja hanci yace “banda komi ko ada chan kaji nake gasawa da sauransu Hawwa tana around shekara 6-7-8 haka mukai hatsari mahaifiyarta tarasu nikuma nadawo haka saida aka guntulemin kafa daya, da kyar da wayyo Allah nasata tagama sakandire Allah yamata baiwan iya dinki kwandala nawa babu akaratunta na jami’a ita tasa kanta hartai masters tace zata fara aikin yan sanda, Hawwa ke kula damu da kannenta komi na gidana Hawwa ne, wata kila inda bata daurama kanta dawainiyan mu ba ta takura kanta harta fara aikin yan sanda ba da hala by now tayi aure nima inada laifi” ya goge hawaye yace “babu mai neman y’ata babu maison ya aureta an tsani Hawwa na, bansan yanda zanyi ba, hawan jini yakama Hawwa sabida tunani da damuwan mesa batai aure, kanninta hudu mata duk sunyi aure hadda yara, yaran unguwa dasuka taso tareda Hawwa wasu yaransu hudu biyar ma, dudda bata nunawa dan tanada jarumta da taurin zuciya amman damuwa yamata yawa, narasa yanda zanyi babu maison auren Hawwa na wayyooo Allah na kaico na amma y’ata gorin aure” Baba kawai yacigaba da kuka da zuciya daya, shi kadai yasan kalan damuwan dake zuciyansa, Khaleel yakai kusan 2min kallon Baba yake chan kaman mai koyan magana yace “inaso na auri Hawwa Baba!” Dawani irin sauri Baba yadago kanshi yakalli Khaleel danjin zancen yayi kaman saukan aradu, bakinshi har rawa yake yace “Ibrahima kace zaka auri Hawwa?” Gyadamai kai Khaleel yayi ashagwabe, bayan hannu Baba yakai ya goge fuskansa tass da sauri yana kallon Khaleel din yasake maimaitawa. “Ibrahima kace zaka auri Hawwa”? Gyadamai kai Khaleel yayi yace “eh” Dasauri Baba yace “kasanta ne”? Gyadama Baba kai yayi sounding like sangartaccen yaro din nan yace “inada Baby her name is Noor antaba kidnapping nata shine Dady na yakira wajen aikinsu ita ta tayamu nemo Noor lokacin nafara ganinta kenan” sosai Baba ke kallon Khaleel da yanda yaron ke magana kana ganinsa kasan dan gayu ne irin yaran masu kudin nan, yan gata he’s so adorable, washe baki Baba yayi yay kosasshiyar murmushi saikuma ya dakatar da murmushin yace “Maza da dama sunsha zuwa suce sunason Hawwa dazaran nace su turo magabatansu shikenan bazaka kara ganinsu ba, bazan takura maka ba Allah yasani zuciyata ta natsu dakai idanhar da gaske kake kanason Hawwa kaje kazo da iyayenka zuwa layinmu da magriba, kome yasamu ka kawo zan baka auren Hawwa, idan yaso bayan ta warke sai ayi maganan tarewa da sauransu kaji, layinmu yana nan kayin gwadabe babu wanda baisan Baba gurgu ba kuzo ina jiranku” ahankali Khaleel na kallonshi yace “okay Baba” the way yake sounding whenever he talks kaman Baby yasa baba yace “shekarunka nawa Ibrahima?” Ahankali yace “32yrs” murmushi sosai Baba yamai sai kawai yakai hannunshi ya shafa kanshi zuwa gefen fuskanshi yace “Allah maka albarka yarona” murmushi Khaleel yayi kadan saikuma kawai yahau gadon yazauna kusada Baba kaman dan yaro yadaura kanshi kan kafadan Baba, shi kawai yanason Baba without any reason.
[9/23, 8:59 PM] M Shakur: 💫GARGADAN SO💫

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 3️⃣8️⃣

Sundanyi nisa ahanya yasa hannu yadauki wayanshi yayi dialing number Babanshi, Musbahu PA Excellency ya dauka yace “Khaleely Babanka na kan chamber” cikeda isa yace “I don’t care kaimai waya” cikeda lallashi Musbahu yace “Allah huci zuciyan yallabai bari na kaimai” Khaleel na kan layin kusan 5min sannan yaji muryan Babanshi a speaker yana excuse me sai chan Excellency yayi magana cikin so da kewa yace “Khaleely na ya akayi? Ina tsaka da meeting? Meya faru bakada lafiya ne”? Dan kishingida yayi murya chan kasa yace “I will send you address na wani anguwa kasameni awajen by 6, kazo da trust friends naka” dasauri Excellency yace “angama yarona zanzo, but meke faruwa lemme know wat I’m coming there for” shiru Khaleel yayi kaman bazaice wani abuba chan yace “I want to marry someone Pops” dasauri Excellency yace “aure? Aure Son? Ba mamanka is the one handling all of that for you ba, an mata screening ne ita wacce kakeson auren? Why do I have to come our lawyers da Malamai can take care of the aure for you, is my presence necessary”? Kai tsaye Khaleel yace “ai nasan dasu nace kazo Pops” dan tausasa murya Excellency yayi yace “I know, I know, karka bata rai I didn’t mean to hurt you, zanzo kawai nayi mamaki ne this is the first person dakake neman aure da kanka batare da Mom naka ta zaba maka ba ta auro maka ba, wacece yarinyar?” Kai tsaye yace “that police girl” dan zaro idanu Excellency yayi yace “you mean officer Hawwa wacce ta ceto Noor? That criminologist”? Murya chan kasa Khaleel yace “uhmm” dan shiru Excellency yayi sai chan yace “Khaleely are you sure about this decision? Cus naga yarinyar is hot tempered, bakaga yanda kuketa fada rannan ba, and you guys are almost age mate fa dan ba karaman yarinya bace, banson wacce zatazo tana baka ciwon kai ba tana wahalar da d’ana fa, I dislike stubborn girls” ahankali Khaleel yace “I can handle her Pops, I just wanna have fun with her Pops don’t worry” dan murmushi Excellency yayi cikeda kaunar yaron nashi yace “you know I will always give you kome kakeso ko? You have my support, see you by 6, I love you yarona Khaleelyn Babanshi” dan smiling kadan Khaleel yayi ya katse wayan ya yar agefe yadago kanshi yakalli Salman yace “I want every info akan mahaukaciyan nan and that photo boy of hers” gyadamai kai Salman yayi yace “yes sir” kallon driver yayi yace “Sam’s house”.
Chapter 43 · 0% Book details