Sashe 9
Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A ranar talata ga watan march, an kama yar shekaru goma sha biyar, da laifin duka Mr Martha's vineyard, a tsohuwar unguwar tabkin. Shiru tayi tana kallon hotonta a lokacin tana karama ne ba. Ajiyar zuciya tayi. Sake bude wani page tayi tana kallon. A hankali ta gama bude file ɗin, kusan duk laifuffukan da ta samu, laifi daya ne taga an saka babu hujja. “Sajan Barau!” ta kwala mishi kira. Shigowa yayi ya sara mata.
“Naga wani laifi amma an ce babu hujja, an rufe case din. Sannan wacce ita?” ajiyar zuciya ya sauke yana me cewa.
“shekaru goma sha uku, baya da suka wuce an tsinci gawar yan ta'addan Eagle bandit sakamakon ambaliyar da aka yi na kwacewar da Dam yayi, a cikin mutanen da suka tsira har da yarinya yar shekara bakwai a duniya, wacce ta manta da wasu abubuwan da suka shafi rayuwarta na baya. Lokacin ban jima da fara aiki ba, wannan al'amarin ya faru. Alhaji Badaru Daniyal shi yazo har Office din yan sanda tayi cike-ciken takardu, sannan ya amshe ta.
Matsalar da aka samu, shi ne tayi fama da matsanancin ciwon mantau, wanda ya sa ta koma kamar ba mutum ba, domin ba a san lokacin da ta dauka a hannun yan garkuwa da mutanen ba. Amma laifinta ba farko kamar yadda kika gani, Laifin duka tayiwa Martha's vineyard, domin a lokacin yayi kokarin wulakanta uban rikonta ne, ita kuma ta hana faruwan haka. A lokacin da aka kawo korafin DSP Ayuba, shi ya saka aka kamota aka rufeta, tun daga lokacin da aka sake ta, ba a kuma samun kyakkyawan alaka da ita ba, domin sai ta fand'are, Madam garin nan yayi shura akan zalinci, wannan zalincin shi ya samar da Xno, domin kare mutumin da yaƙe dawainiya da ita, Madam ban san zahirin gaskiyar abin da ya faru ba. Amma sakamakon sauya-sauyan wuraren aikin da nake samu, ban san dalilin da ya mai da ita cikakkar yar daba ba, sai dai dawowa na garin nan na fahimci tana ƙare gidan al'umma charity House.” shiru tayi tana kallonshi.
“Ko tana karuwanci ne?” ta tambaye shi, kafin ya ce mata. “Subhanalillahi, idan aka ce daba da jagaliyanci, tow kuwa babu sama da ita, domin da kankantar shekarunta, take dakawa maza gunba a hannu, tunanin tana hulɗa da maza duk ban sani ba.” mikewa tayi tana faɗin. “Dole mu dawo da case din da aka ce babu hujja, sannan ina da ayar tambaya akanta, domin ban yarda da ita ba. She acting over confidence.” “Ok Madam”. “Dole nayi digging a rayuwarta single mistake na samu a rayuwarta sai na bude mata wuta ita da dabar ta.”
****
Zeeno.
Koda suka isa gidan, jama'ar gidan kamar su goya su suke, sauka tayi a motartana faɗin. “Daga yau duk abin da ya faru, kafin a aiwatar da kome, a tabbatar da an sanar da ni kafin ayi wani aiki. Wannan mutuwar Prime minister, ya sauya mana kome don haka kada wani ya sake ya fada hannun wancar yar sandar domin ba zai mana kyau ba. Idan wani abu ya faru daku rayuwata ce zata cutu, wannan alƙawari ne da na dauka muku, don Allah ku dinga nazarin kome kafin ku aiwatar!”
“Ayya Zainobia kina da naki rayuwar ki kyalesu mana, kema kiji da naki rayuwar mana.” inji Hafsy. Domin tana masifar jin haushin ganin yadda Zeenobia take bada rayuwarta akan mutanen nan.
“Hafsat ba zaki gane ba ne, su din sune ni idan babu su, tow kuwa babu ni.”
Taɓe baki tayi, tana me wucewar ta domin tasan yanzu dai sai su raba hali akan mutanen da take mutuwa akan su, basu sumarta.
Tunda ta zube a saman gadonta take, sauke ajiyar zuciya. Exactly 3 year sanyi ne da ciwon kai yake bibiyarta tun safen yau amma baki daya ba ta ce ba. Don rabonta da wannan yanayin.
****
Green House.
House of representatives. Crud City Hall.
Yan majalisar kolin ne suka hadu. Shiru hall din ya dauka, domin tattaunawa akan abin da ya faru. Fitowa Assamblywoman, Mss Lalla Salmah ta zuba musu idanu kafin ta ce. “Izuwa yau duniya da sauran ƙasashen nahiyar Afirka, sun daura idanunsu akan Mayor Malik Menk Jordan, Ni dai ban laifin shi ba, kuma har abada ban zan ga laifinsa ba, domin kare kai da dukiyarsa baya nufin ya kare kansa a matsayin lusari ba.”
“Keee Lalla Salmah, babu me sauraren wannan zancen naki. Dole majalisar koli ta sauke Mayor Malik Menk Jordan, ko kuma mu ɗauki mataki akan dan ta'adda." Inji wani dan gajeren mutum me katon ciki. Dariya tayi tana faɗin. "Same scandalous wai suna da bakin magana, mutanen da basu gudun abin kunya.”
Kura mata idanu yayi har ga Allah, maganar ta bata mishi rai. Bai san lokacin da ya fara kokarin tsalleke wurin zamansa ya tsallako wurinta ba. “Idan ban miki shegen duka ba, Alqur'an uwata shege ta haifan!"
“Mr Abid ka kiyaye bakinka, Mayor Malik Menk Jordan ba kanwar lasa ba ne, don haka muje ga tattaunawar mu. Kowa yasan waye Malik, sannan izuwa yanzu abin da ya faru ya dace mu nazarci meke yake faru.”
“Yallabai, harkan Kasuwancin garin Keivroto city harka ce ta ban mamaki. Sai dai a bangaren ilimin rayuwa dole a fuskanci matsala, ba laifi ba ne idan Malik ya k'amk'ame kome, ai na shi ne. Kuma iyawarsa ya kai shi wannan matakin. Ko mutuwar Prime minister bana da ja tabbas bai da cikakken masaniya akan mutuwarsa.”
“Wai Lalla Salmah me kike son fada? Me kike son gaya mana? Waye bai san cewa kaf duniya Malik bai daukin ran kowa da daraja ba, har kwanan gobe Malik ubangijinsa shine kudi, matansa kuwa kartin maza ne kin isa ki kare shi da abin da ya faru, shekarun talatin da wani abu baya, tun yana daura igiya a matsayin zariyar wandonsa muka san Malik shi kare ne, wild dog ne da muka watsa mishi kashi ya bi yana haushi, duba kaina Lalla Salmah. Kin fito daga babban gida kada ki sake goyan bayan da Malik ya baki, ki tab'a nasabar gidan ku. Ka da ki zama me bawa kasungurmin dan luwaɗi goyan bayan. Ba zamu lamunci haka ba, don haka dakatar da Malik ya zama dole.”
“Shu'iba kada kayi wasa da rayuwarka,Malik ba abin wasan yara ba ne ka iya kalamanka domin duk tsohon da bai
Kunyar hawa jaki, jaki ba zai ji kunyar kadda shi ba........"
*Hi......! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP for information 08130269641*
[8/28, 6:46 AM] Mmn Khaleel: https://chat.whatsapp.com/KZbdBOduk2c2nLpNQp7Qh3
CINIKIN RAI....!
Beauty and the Beast♡
006
_Past_
A lokacin da suka zo ganin wurin dayawan su, sun yi fatan da sune suka kawata wurin domin ai sune yan kasa ba Nasr Hadejia da Aswad Yamini ba. Taya baƙin haure zasu zo su fi yan gari kawo cigaba har haka, wani abin ya tsaya a ransu. Matukar tsaya musu. Kuma ba iya shi ba, asalin su mutane ne masu matukar Kyashi da Hassada da wannan dalilin yasa suka buɗe iyakokin duk wani tubalin bakincikinsu, inda aka fara turo musu yan jagaliya suna yiwa mutanensu daukar amarya. Koda Alhaji Nasr Hadejia ya ga haka sai ya shigar da bukatar jami'an tsaro su shiga cikin al'amarin amma abin haushi sai aka yi rashin dace. Domin yan sanda bakinsu daya. Haka yasa jikinsu yayi wani zai ce me yasa suka nace da son suyi wurin shakatawa? Abin da mutum be gane ba, shi ne fisto yana cikin garuruwan da suke buƙatar a inganta su. Na farko zai samawa birnin cigaba, na biyu matasan garin da suke sana'ar daba da jagaliyanci zasu samu aikin yi, dattawan da suke sana'ar kamun kifi, zasu samu damar baje kolin sayar sa kifinsu. Sannan gari ne masu al'adar gargajiya. Wannan dalilin yasa baki daya mutane biyun nan saka zuciyarsu, akan lallai su kawo cigaba da garin.
A hankali kome ya fara kwace musu, domin a zahirin gaskiya yan daban sun dame su. Abubuwa biyu ya dame su, ga asarar dukiyarsu ga wasu daga cikin mutanensu a hannun yan garkuwa. Akwai wata rana da Alhaji Nasr Hadejia da Aswad Yamini suka hadu a gabbar tsibirin. Kowanen su, yana da damuwa amma dan samu kwarin gwiwa a tsakaninsu yasa suka sauke ajiyar zuciya a lokaci guda. “Hadejia ina ga ya kamata mu sake budar wurin Mayor Fahad Albagwi da wannan al'amarin, idan har muka yi haka tow ba makawa zamu samu adalci, kaf garin nan kansu a haɗe yake ba zasu sake mana mutanen mu ba.” kallon shi yayi sannan ya ce mishi. “Ni ma nayi tunanin haka, amma nasan Allah yana sane da al'amarin mu, Allah zai tsaya mana.”
“Ka saka mana lokaci mu tafi wurinsa, idan yaso sai mu shirya ba.” murmushi Alhaji Nasr Hadejia yayi ya ce mishi.
“Idan Allah ya kai mu gobe, sai mu tafi. Ina son na kira iyalina ne su zo da Yarana.”
Dariya suka saka ya ce mishi.
“ai ku yan Nigeria kuna da hakuri da juriya, ina zan iya wannan hakurin? Kawai malam ja sa Madam ta dawo nan, kafin nan karatunsu da kome nasu zai dai-daita.”
“Hmmmmm! Tow ya zamu yi? Kasan idan baka yi hakuri ba, ya zaka yi da hakkin Allah, shi Allah ya sauke hakkin mu da yake kansa, saura mu mu sauke wanda yake kanmu. Ina da Yara mata biyu, ina jin kunyar na bude idanu na kalle su bayan na sabawa Allah, sannan Allah ba zai kare mu ba. Sannan ba zai kare bayan mu ba, amma idan muka ƙare kanmu da iyalinmu Allah zai kare bayanmu bayan mutuwar mu.” jinjina kai Yamini yayi yana faɗin. “Na gamsu da bayaninka. Allah ya kare zuriarmu bayan mutuwarmu” “Allahumma Amin” da wannan suka ajiye zancen zasu tafi wurin Mayor Fahad Albagwi.