← Book details Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 33

Sashe 22

Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Radio me jini, a bar zubata haka, uwar masu surutun Keivroto!" Tura baki tayi tana faɗin."Jadda kin ganta ko?" " Ai matsalarki surutu, ki bar baki su shigo, barkan ku da zuwa, sannun da zuwa Maidah." Gyada kai tayi, tana murmushi. Hajiya Jalilah ta ce mata, "Sayyadah Qudussiyah. Ya aka ji da jama'a." Murmusawa tayi tana faɗin."Alhamdulillahi, muna kan fama dasu, sai godiyar Ubangiji." Gyada kai Hajiya Jalilah taii, bata ce bata da madubi ba, kafin ta fara harkan nan da take a boye,sai da ta zauna a Diana Menk Jordan, foundation. Asalin taimako suke bawa mabukata da yan gudun hijira, tare da yan cirani.

Dare daya ta gudu, kafin daga baya taji labarin an mai da shi, Salsabilah Menk Jordan, sunan mahaifiyar Menk Jordan, bayan rasuwarsu, ita ta dawo nan suka cigaba da kula da wurin, duk da tasha bakar wahala, ko da yake ai ba ita za a ce tasha bakar wahala ba, hatta Malik sai da yayi kamar ba zai tab'a samun kome ba, kafin Allah ya nufe shi da dawowa, masu ganin ba zai tab'a dawowa da abin da aka kwace mishi, tow kuwa sai da ya shafe musu hadda.
"Ina Lalla Salmah!" Murmusawa Maidah tayi tana faɗin. "Maama tana can tana fama da majalisa." "Allah sarki Ubangiji ya dafa musu, aikin kenan idan kana raye dole ka tashi ka nima, idan baka nima ba kare sai ya fi daraja, duk da akwai mutanen da suke da Sa'a amma kuma niman na kai yana da fa'ida! Atikah?" Ta kwalawa wata mata kira. "Yes Ma!" Ta amsa cikin girmamawa. "Ga bakuwa nan ki kaita dakin da yake kusa da na Nadrah!" "Ok Ma!" Tazo ta amshi kayan me yi mata jagora har cikin gidan, "Baby zan tafi, Sayyadah Qudussiyah zan tafi! Yan mata Wahida ko! Zan tafi" "Allah sarki na zata zai zauna sai dare" "A'a ina da abu me muhimmanci!"

"Allah sarki, sai yaushe!" Satar kallon Jadda tayi taga hankalinta yana kan mage, sai Sayyadah Qudussiyah ta bukaci haka. "duk da tserewa tarbiyyar da kika yi, har yau dai gidanku ne nan, duk lokacin da kika so zaki iya zuwa ki dauke shi kamar gidanku" gyada kai tayi tana faɗin. "In sha Allah!" Sannan ta fita a gidan tana ajiyar zuciya. Wannan shi ne zuwanta na farko bayan barin Foundation din shekaru kusan sha takwas, hawaye ne ya zubo mata.

Su uku kamar yadda suka taso, kallon fuskar Wahiba tafi kamar da Nuratu kamar me, Wahida ce dai take kokarin hango fuskar waye tabbas tasan fuskar. Amma ta manta baki daya ta manta fuskar waye, lumshe idanun tayi tana jin dariyar Nuratu. Bude idanun tayi tana kallon gefen ta. _Idan har na samu Malik dole zai hakura da kiyayyar shi, ya bani abin da nake so._ kauda kai tayi hawaye na zuba mata. "Ku zama shaida idan na kuma ganin, Jalilah sai dai a maidani gidan kaso, amma tabbas sai kashe ta." Hawaye ne ya zubo mata da gudu da gudu. Ta zauna zaman jiranshi amma aka samu tsinannen da ya shiga rayuwarsu ya lalata kome.

"Ku fita min da ƙaruwar nan, ko na kashe ta" kuka tayi tayi tana kara kukanta, "Malik!!! Ka yarda da ni, ban san kome akan abin da ya faru ba, wallahi ba zan tab'a barin a cutar da Nuratu ba!"
Kuka take sosai har suka isa gida, rabonta da tayi kuka haka, ta manta. Tana shigowa gidanta. Kalamanshi masu zafi suka kara dawo mata. "Ke tsinanniya ce mara albarka, tsiya da lalacewa sune zasu ta bibiyar rayuwarki, kiji da kyau yadda kika bata rayuwar Nuratu Allah ya tsine Miki! Magajiyar Ƙaruwai!" Wani irin abu ne ya tsaya mata a makoshi. Tabbas Malik yayi gaskiya ita magajiyar Ƙaruwai ce, ga gidanta ta cika da karuwai, ita kanta bata taɓa tunanin maganar zai tabbata ba sai yau. Tara dukiyar take amma har yau ba zai yi albarka ba, domin da zina da wasu abubuwan aka same shi. Wucewa ɗakinta tayi abin da ake fada akan Malik gaskiya ne, yawun shi da dukiyarshi Bala'i ne.

---------
Tun bayan fitar ta, Sayyadah Qudussiyah ta Sunkuyar da kai, hawaye ne ya zubo mata. "Sayyadah wallahi ban san abin da ya faru ba, a daren ranar na san mun je gidan Lalla Salmah kuma mun ci abinci mun fito, daga nan muka tsaya muka a kofar gidan Lalla Salmah muka shiga Mota. Daga nan ban san kome ba, sai farkawa nayi na ganni a asibiti. Sayyadah wallahi ban san kome ba, taya zan dauki Nuratu da bata da wadatacen lafiya, na cutar da ita, Sayyadah meye amfanin rayuwata idan na lalata rayuwar Nuratu. Don Allah sayyadah kada Malik ya ce ya fasa aurena. Ban san ya zanyi!"

Tabbas nuratu ba ta da laifi, amma waye zai yarda da ita? Bayan an gama bincike an gano biyanta aka yi ta kai Nuratu aka yi lalata da ita. Bayan ta dawo da ita Keivroto tunda Malik yace matukar ya ganta zai kashe ta, yasa ta rufawa kanta asiri ta anan ta zauna daga baya tsangwama da take fuskata yasa ya gudu babu shiri.

Zare medical glass dinta taii, domin har aka gama Nuratu ta haihu ta rasu, Jalilah bata da labari, sai bayan wani lokaci ta hadu da Sayyadah Qudussiyah ta gaya mata mutuwar Nuratu, a ranar tayi kuka tare da cewa In sha Allah wanda yayi sanadin rabata da Malik da Kawarta sai Allah ya mishi, sama da abin da ya mata. Hakika an cutar da ita. Kuma gefe daya Malik ya kara kiyayyar shi da tsinuwar shi yayi tasiri, tasan darajar rashin ahali domin iyayenta hatsarin mota jirgin ruwa suka yi, ita kuma aka sace ta, aka kawo ta Demark, ta sarafa kafin ta fada hannun Alhaji Menk Jordan......
*Hi......! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A'ishah. +227 84 50 64 76 500*
[8/28, 2:27 AM] Maman Sadiq Da Khadijah: CINIKIN RAI....14
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
Maniyyata sun fara payment! Jiran me kike?
<<<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>>>>>>>
```Love looks not with the eyes, but with the mind, and therefore is winged cupid painted blind.```
<<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>>>>>>>>
"Jadda ya dai?" Nadrah Khamis Shatima ta tambaye ta, tana kallon yadda ta shiga damuwa. "Ba kome, kawai wasu abubuwan ne idan ka tuna bayan baka da yadda ka iya sai kaji zafi a ranka." Gyad'a kai tayi tana faɗin. "Haka ne, amma kome yayi zafi maganin shi Allah." " Na yarda da haka, sai dai a wata rayuwar, Allah yana sane yake barmu da mugayen halaya. Domin ya ga yadda zamu yi, barin mu a haka shi ne babban tashin hankali."
Ganin yadda Nadrah ta makale tana son jin me ya faru, yasa ta basar da abin ta mike tare da barin falon. Idan ka zauna da Yaran zaka fahimci kowa da halinshi. Nadrah Khamis Shatima tana da masifar son jin kome, shi yasa kullum kafin kaji labari a bakin wani a bakinta zaka fara ji. Yayinda Wahida Malik Menk Jordan, ta kasance me yawan fara'a da son mutane, da surutun tsiya kamar Radio. Wahiba Malik Menk Jordan kuma sai ta kasance miskila mara son magana, ga dan banza reni da gani-gani. Sannan idan Ubanka ba wani ba ne, bata kula ka. Gashi tana da ilimi sosai, amma magana bai dame ta ba, bayan wannan halin Nadrah yarinyar tana da kirki sosai, domin ba kowa yake iya jure zama da Wahiba Malik Menk Jordan ba, domin kusan kullum sai ta mata rashin mutunci. Amma tana like da ita, tana hakuri hakan ne domin mahaifinta ya rarrasheta da tayi hakuri ta zauna da halin Yaran. Duk da babban damuwarta, shi ne ta samu kusanci da Malik kamar yadda uban ya ce, akwai wani abu daya da suke kokarin ganin sun cusawa yaransu, shi ne dole yaran su bayyana jikinsu ga Malik ta haka sha'awa zata saka ya ga ya bukaci yaran daga Khamis Shatima da Lalla Salmah wannan shine buƙatarsu da kuma kudirinsu.
Shirin su na rikito da Malik ba karami ba ne, sannan idan har akwai abin da suke hari tow dukiyar Malik ne, shi yasa duk abin da suke har kwanan gobe babu nasara, amma zasu cigaba da fafutukar ganin sun sami hakarsu ta cimma ruwa.

Amjad
Sintiti yake daga Office dinsa, zuwa bakin Office ɗin. Baki daya hankalinshi a tashe yake, kai yafi ma ganin hankalin shi zaune take da gindinta, wayar shi ce tayi kara ya ɗauka tare da sakawa a kunnenshi.
"Chairman gata nan ta shigo kamfanin!" Hadiye yawu yayi, bai taɓa kawowa a ranshi zata dawo yau ba, sai gashi ta dawo ɗin. Sai da ya sauya kaya sannan ta wuce office dinshi domin Mss Mary ta gaya mata yana son ganinta.
A hankali ta tura kofar, yana zauna a kujeranshi, zuba mata ido yayi. "Ke kuma haka ake rayuwa?" Dauke kai tayi tana kallon waje, "Nasan bai kyauta ba, amma a madadin haka sai ki tsaya ki ji me zance miki, ba wai kiyi gaban kanki ba. Gashi nan zaki hadu da Elbashir, duk abinda zai faru, ya faru amma ka da ki sake baku hadi da Malik ba, shine kawai zai yarda da bukatarmu"
Chapter 22 · 0% Book details