← Book details Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 33

Sashe 19

Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Idan baka manta ba, rashin tsaurarra tsaro yasa aka samu matsalar da har yau yake jinya, idan har Malik bai kiyayye rayuwarsa ba, me kuke so yayi?" Shiru suka yi, suna kallon juna. "Yaushe ka dawo?" Lalla Salmah ta tambayi Elbashir, tab'e baki yayi ya ce mata. "satin da ya wuce, ina Maidah?" "Tana lafiya, next up week zata tafi Demark, akwai course ɗin da zata tafi tayi akan karatunta na wata shida." Gyada kai yayi, sannan ya cigaba da kallon jaridar da yake gabansu. Kallonta Shatima yayi ya ce mata. "Gashi kusan lokaci guda Nadrah zata gama karatu da su Wahiba da Wahida. " Murmushi tayi ta ce. "Eh wallahi, Yaran Nuratu sun girma! Har yau ba a samu danginsu ba ko?" "Ki tambayi Malik shi yake da masaniya akan zuriarsu." Tabe baki tayi tana faɗin. "Naga ai kafi mu kusa da Malik, kai zaka riga mu sanin kome." "Nima bani da ikon sanin kome, sai abin da Malik ya gaya min, ba zaku gane cewa Malik Menk Jordan ba kome yake sanarwar ba, sai abin da ya zama dole Ppl dinsa ba kowa ya sani ba, sai shi kaɗan shi."
Kallon agogon hannunshi yayi ya ce. "Oopss... Sorry ashe yau ba zaku samu ganawa da shi ba, sai nan da wata sati." Ya mike yana murmushi, "what!!?" Lalla Salmah ta zare idanu, kamar zata fasa ihu. "Yanzu don Allah meye haka? Duk wannan wahalar ace ba zamu samu ganinshi ba?"

"Akwai matsala ne idan baki ganshi ba? Ko akwai wani abu ne rashin ganin Malik din?" Yadda ya tsare ta da idanu,yasa ta sunkuyar da kanta, ta ce. "Ko ɗaya." Ta mike tana faɗin. "Allah ya kai mu." Inji Shatima dama shi bai wani damu ba, harka ce ta siyasa, kuma suna fitowa yake gayawa Elbashir abin da ya kawo shi, ita kuma ba haka ba ne, kudirinta akan dole sai tayiwa Malik tallar Maidah ne.

Haka suka fito daga tsibirin ranta a bace, shi kan Shatima bai yi wani mamaki ba, domin yasan darajar Malik kafin ya yarda a ganshi tow sai kayi kamar kana yi, don haka ya sakawa ransa sallama, Indai Malik ne ko wancan watar da ake ta bala'in akan abin da ya faru suna tare a Green House. So shi bai wani damu ba.

-----
Lokacin da suka iso gida, maid dinta suka tare ta, bala'i da masifa ta tare su, sai fada kamar zata doke su, babu wanda ya kulata.
★★★
United States of America.
New York.
Anan suka sauka, a wani apartment me kyau na fita hankali, ba kowa yake zama a cikin apartment din ba, sai manyan mutane ko Celebrity da yan matan yan siyasa. Sai da aka yi sati biyu tana sauka span a kasar apartment din ana mata gyaran jiki. Kafin ranar da ta cika wata guda,aka fara kaita kamfanin Baazar ta dauki hoto tare da musu tallar wasu abubuwan, kamar kamfanin kayan kayan kwalliya, sai kamfanin sarrafa kayan sawa, D&G, sai na turaren explore. Watan ta biyu a US, suka wuce Dubai inda tayi tallar wasu abayas, tallar ya janyo aka gayyace ta bikin karrama Celebrity a London, tare da Vogur babban gidan mujallar Ingila, me cin gashin kasa, wanda yayi promote Halinta haded, Rawda Muhammad, da sauran hijabs girls, duk wannan tafiyar sun shi ne, da Salim duk inda ta saka kafarta yana biye da ita. Kayan da ta saka doguwar riga ne, shiffon material aka dinka mata, shi me shegen kyau, shara-shara me azazzben kyau da ɗaukar idanu. Kanta wani turban ne, da aka yi like net, fuskarta an yi mata normal makeup, da kayan makeup na milan, daga takalmin kafarta zuwa jakarta, abin dubawa ne domin ta nutsu tana abu gwanin ban sha'awa.
A lokacin da suka shiga hall din, hankalin kowa ya koma kanta, musamman kamfanonin da suke buƙatar sabuwar fuskar da zata musu talla, kuma abin da Mr Amjad yake bukata kenan, ta zama wacce duniya zata yayyata da zuzzutatta. Kowa ya santa duniya ta san wace ce ita, kowa ya gane ita wace ce, kuma haka ya faru. Domin a cikin wurin taren mutane dayawa sun bukaci ganin Manager ɗinta, da suke yi sponsored ɗinta, babban burinshi ne.
Kafin wani lokaci gidajen tv da na radion, Gista da Keivroto ya dauki labarin ana yayyatawa ana kara zuzzuta Zeenobia, yarinya daga getto area, ta zama shaharariyar da ba a zata ba. Dakyar ya yarda ta saka hannu a kan wasu kamfanoni guda biyu, zata yi aiki da su na wata biyar biyar, domin baki daya baya son sharararta ya wuce haka.

Haka kuwa aka yi kamfanin farko daga Gista take na sadarwa ne, ita zata na musu talla akan wasu abubuwan su. Sai na biyu kamfanin kayan kwalliyar mata ne, sai da ta kai manyan gidajen jarida masu zaman kansu, sun sayi hoton fuskartar. A wannan tafiyar sai da ta kwashe wata hudu cur kafin ta dawo gida, tsabar ta gaji, sai da ta kwana uku bata iya ko lekowa, sai ranar na hudu ta fito ta shiga cikin gari, a nan ta samu garin ya cika da poster dinta, murmushi tayi har ta. Wani shagon cin abinci, dake dare ne kuma ta saka riga me hula da facecap. Haka ta fita ta sayi abin da zata saya, a hanyar dawowarta ne, suka yi kicibis da Asp Zulfa suna patrol. Dauke kanta tayi zata wuce da motarta suka tsayar da ita. Ko a cikin dubu ta sauya shiga zata gane ta, balle a ita daya kaya kawai ta sauya. "Miss Zeenobia, ba a taba sauyawa tuwo suna ba, tun duniya na kwance balle yanzu sa take zaune da gindinta." Cire facecap din tayi tana lashe dark red lips dinta ta ce mata. "Kina bukatar selfi ne?" Murmushi Zulfa tayi tana faɗin. "Ina selfi amma ba da watsassun mutane ba." "Keee yar sanda!" Tayi wani karkata baki irin na samu na yan daba, ta ce mata. "Ki iya bakinki!" Ta juya zata shiga motarta, rike rigarta ta bata Zulfa tayi tana faɗin. "jagaliyarcin ya motsa ne?" "Na rantse da Sarkin da yake busa numfashi idan, kika dame ni sai na kaddamar miki, na gaya miki." Tayi tsaki tana shiga motarta, "Na kama mutane biyu da suka lokacin da kika kashe Ayuba da Wasim." Cak tayi ta tsaya tana kallon Zulfa in confidence ta dauka a motar tana me nufar Zulfa. "I'm glad da abin da kika yi, sai dai ki sani ni naci dubu sai ceto, idan har kina da zarra tow ki kwamushe ni, Zeenobia nake Xnoo, yar kunama karamar su Babbar su." Ta wuce tana me barin motar, sai da ta tashi motar sannan ta bud'a musu hayaki. Tayi gaba abinsu.
★★★
2weeks.
Mika mata file yayi, ya ce mata.
"Zaki musu tallar sati daya, kamfanin abin sha, ture file din tayi tana faɗin. "Ina son kudi zan tafi Ofishin haraji ne." Murmushi yayi ya dauki wayar shi yayi kira. "Hello bani takardar harajin nan!" Can sai ga Salim ya shigo, mika mishi takardan yayi, ya mika mata. "Zeeno gashi nan" sake bude drower dinsa. Ciro wani kwali yayi ya ce mata. "Gashi nan" murmushi yayi yana kallon yadda ta ruɗe. Kallonshi tayi na wani lokaci, kafin ta ce mishi "me zan yi da shi." "Bude ki gani mana" a hankali ta bude kwalin tayi, zare idanu tayi kamar zata fasa ihu. "Kina tsammanin zaki yi aikin nan, babu wani abu ne sannan ki duba motarki, kina babban yarinyar babu mota na more rayuwa! Ga wannan katin ki tafi bankin golden bank a cire miki password ɗin da kike so, sai a cigaba da sharholiya." Murmusawa tayi tana faɗin. "Dole ayi sharholiya a al'umma charity House." Ta fada tana kallonshi. "Kinsan me yasa na zuba miki kudinki ta golden bank? Domin mutanen Malik da Yaransu a wannan bankin suke amfani da shi", ware idanu tayi tana faɗin. "Yaushe zamu fara nufar Malik din!" "Da sauran lokaci"
Gyada kai tayi ya dauke kome ta fita, murmusawa yayi tana fita, Salim da MD suka shigo. "Me ya rage Chairman?" Murmushi yayi ya ce mishi. "Ta fada komarmu! Ita ce abin harin mu, domin Malik ba zai kamu ta dadi ba, dole sai da tsananin hawa." "Kenan Malik kifi ne da ba za a kama shi ba, sai an watsa mishi tanna da kwari!"
D'ago idanu yayi ya ce mishi. "ita ce tannar tawa!"
Murmushi yayi ya ce " Musu, rayuwarta wadancan mutanen ne, idan kana son ganin farincikinta, ka yiwa mutanen hidima!" Gyada kai yayi suna masu jin dadi a ransu.

-------- Zeenobia kuwa motar ta dauka ta nufi bankin, yayi duk abin da zata yi, lokacin da ta shiga bankin mutanen da suka ganta, sai ta zama celeb domin kuwa kowa rubibinta suke. Bayan sun gama mata kome da girmamawa,a hanyar fitar ne suka hadu da Mr Shatima, har ga Allah kallon da yayi mata, ta tafi da imaninshi. Kara kallonta yayi yaga yadda take taku a nutse yasa shi shagala da bin ta da idanun.
Gyada kai yayi, Hadi P.A din shatima ya ce mishi. "Yallabai baka san ta bace, ita ce yar tallar nan ta Baazar da Vogur." "Hadi ayi wani abu a kanta, tayi min sannan a tura mata kyautar ban girma a account ɗinta. Domin kuwa kaiwa Manager magana." "An gama Yallabai!" Murmushi yayi yana imagine yadda zai sarrafa yarinyar, domin kuwa yana cikin mutanen malik masu mugun son mata, shi yasa tun rabuwarsu da uwar Nadrah bai wani kara aure ba, domin baya son damuwa, shi yasa ya bige da bin yan mata musamman yan kananun Celebrity, yana kashe musu kudi kamar yayi hauka.
Chapter 19 · 0% Book details