← Book details Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 33

Sashe 12

Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kasancewar kasuwanci ya kawo Muhammad Nasr Hadejia, kuma abin burgewa yana da ilimin addini da na boko, wanda yasa shi kallon garin a matsayin garin da za a cigaba sosai. Sai dai wani abu biyu da ya dakushe garin. Kabilanci da zalunci, haka yasa shi fara binciken da bibiyar hukumomin haraji na garin Fisto, Allah ya bashi sa'a zuwan farko ya hadu da Aswad Yamini. Shima dan kasuwa ne, a'a Balarabe daga kasar Yemen. Shima mutum ne mai matukar son kasuwanci da cigaba. Don haka a tare suka yi decided yadda zasu gini bakin tsibirin. Yadda zai bada abin da ake bukata, domin ginin zai kasance a cikin ruwa ne, kamar yadda bora-bora island yake. Wannan shine kudirinsu. A lokacin Alhaji Muhammad Nasr Hadejia yana da matar shi har da Yaransa biyu mata, a garin su Hadeja. Sai dai bai yarda ya kawo su. Aswad Yamini yana da matarsa da dansa daya a garin domin a tare suka zo Fisto.

*Present*
Police headquarters.
“Har yau babu wani shaidan dan da za a iya kama Malik shi, abin da na sani mu jami'an tsaro, zamu yi tafiya kafada da kafada, da hukumar binciken farin kaya. A duk lokacin da sahihan shaidu suka samu a cikin tabbatar an kama Malik tare da gurfanar da shi a gaban kuliya. Na gama magana.”
“Ok sir!” bakidaya an sandan suka amsa, sannan kowa ya mike tare da shugaban yan sanda bakiɗaya. Suna fita yan jarida suka nufe su. “AIG wai da gaske ne kuna yiwa Malik aiki.?” inji wani dan jarida. Shiru yayi kafin ya bada amsa wani gidan jaridar ta kuma wurga mishi tambayar. “shin yau babu tabbacin Malik zai fuskanci kotu kenan? Shin Malik yana da ikon juya kowanni bangare na siyasa kenan?” duk da ba a bashi izinin yayi magana ba, amma dole ya gayawa duniya cewa hukumar yan sanda basu yiwa Malik aiki.
"Yaku yan jarida ina son na sanar muku cewa, hukumar yan sanda basu bin bayan kowanni bangare fecce aiki da gaskiya da Amana, sannan da ace yau hukuma ta kama Malik da laifin kashe Prime minister, da ba a rufe awa ashirin da hudu ba, ba tare an kama shi ba. Duk wani hujjojin da ake bukata mun tanada shi, sannan duk wani binciken da ya dace, anyi bai da masaniya a kan kashe Prime minister."

"Sai dai har yau muna da labarin cewa, Malik Menk Jordan shi ne yaron da ya kashe Manyan yan siyasa da jami'an tsaro uku, shekaru kusan arba'in da suka gabata, shin wannan ba hujja ba ne da zai iya rufe shi har abada ba?" Kallon dan Jaridar AIG Yasir Aswad Yamini yayi, kafin ya ce mata.
"Har yau muna kan bincike.”
“Yallabai²"
Suka shiga kiranshi, amma ina yan sanda sun kare shi. Har ya isa cikin motarsa. Kallonta yayi ta zuba mishi idanu.
"Omooooo! Me yasa kika zauna a nan zafi ba zai dame ki ba?"
"Taya ba zan zauna ba? Wallahi kaji tsoro Allah, akwai cases sun kai ashirin akan Malik Menk Jordan, me yasa kake tsoron bayanan laifinsa ko kai ma kana tsoron mutuwan ne?"
"Mutane irinku, kullum tunanin su hango laifin wasu baku tab'a zama ku fahimci me yasa wane ya zama haka." Bata bari ya kawo karshen zancen ba, ta bude motar zata fita, riko hannunta yayi ya ce mata.
"Me yasa kike fushi?" Idanunta cike da takaici ta ce mishi. "Ok ya batun binciken ki?"
"Sake ni!" Bakinsa a dai-dai kunnenta, "let me kiss you." Ture shi tayi, tana faɗin.
"Ni ba yar iska ba ne....." Sumbatar ba zata ya kai mata, ta wani ware idanu ta. Hura mata isa yayi. "Asp zaki iya tafiya!" A hankali ta bude kofar ta fita, kallonta yayi yana murmushi. "Ki kula min da kayan alatuna. Zan gayawa Auntynki!" Bata saurare shi ba, tayi gaba. How comes? Taya zata dauki wannan al'amarin.

Haka ya tafi ya barta da Faduwar gaba, tasan Aunty Fannah, da Bala'in kishi. Musamman akan Mijinta bata hada shi da kome ba.
-----
Kamar yadda suka bukata yau ta fara zuwa aikin, sai dai tunda ta isa bata zauna ba. A tarihin rayuwarta wannan lokacin shi yafi kome bata wahala. Sai yawo suke manyan ofisoshin gwamnati, da gidajen masu kudi,babu karya wanka iya wanka yau tayi shi. Shi yasa duk inda suka je cikin ruwan sanyi suke samun ganawa da Mutanen da ta je gani.
Past.
Daga cikin abubuwan da Nasr Hadejia da Aswad Yamini, yasa suka samu ganin Mayor na wannan lokacin, domin a basu damar Fahad Albagwi, a lokacin ya basu full attention dinsa, sannan ya basu damar gini a bakin tsubirin, tare da dauko masu gine-ginen zama daga kasar Canada.
Duk wanda ya saka gaskiya a cikin al'amarinsa, zai ga gaskiya domin a kasa da wata uku suka gama ginin, tare da fara kokarin bude shi, a lokacin manyan attajiran Fisto da Keivroto suka yi ta zuwa......
*Hi......! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A'ishah. +227 84 50 64 76 500*
[8/28, 6:46 AM] Mmn Khaleel: CINIKIN RAI....!
Beauty and the Beast♡
007
_Wace ce Xno?🌚 Da za a wani dame mu da ita, yar daba da ita😏🚶🏽‍♀️ sai mun bindige yar tusa kanwarka tutu, yan comments section aji tsoron Allah 🙄🙄😏 ku daina abin da kuke._
<<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>>>>>
_Past_
"Ni Malik!" Ya nuna kanshi, yana me kallon ilahirin mutanen da suke wurin. Sannan ya nuna su da yatsa. "Bani da had'i da ku, sannan shi bai da haɗi da ku, don haka kowa ya kama gabansa, idan ba haka ba tow kuwa zan mai da hankali wurin girbe rayuwarku." Ganin yadda ya iya kashe dabobbin da Dulma yaƙe takama da su, babu tausayi balle imani, yasa suka fara ajiye makamansu, suna barin wurin domin kuwa suna son kansu. "kai Malik waye kai? Kana abu kamar wani mutum, bayan kowa yasan cewa uwarka ma karuwa ce."

Wani irin b'acin rai yake ji, idan ya tuna abin da ya faru, idanunshi a rufe suke, a hankali ya buɗe su, sunyi wani irin jajjur tare da ƙwanciyar jini a cikin ƙwayar idanun. Ya juya tankar juda. Cillar da sigarin yayi ya juya kofar kegin zakunan ya ballo wani murtakakken karfe, ya nufi dulma da zazzababen gudu, yana isa wurin kafin Dulma ya ankara tuni ya zuba mishi karfen a tsakiyar kansa, zubewa yayi jini na fita ta hancinshi da baki da kunne, sannan ya juya wurin motar da ya zo da shi, ya ciro igiya, ya daure kafar Dulma ya daura da boddy motar, ya shiga jan shi. Kafin ya shiga cikin ma'aikatan, ya ciro mutanen da aka kama su, tare da sake mutanen da suke aikin bauta, sai da ya tabbatar da ya sake su, sannan ya rufe ma'aikatan ya zuba nakiya ya saka mishi lokaci, ya tattara dukiyar da ya gani, kudi da wasu abubuwan matasa da maigidanta da suke wurin ya mikawa. "Kuje da shi, duk wanda ya iya tuka mota, ya tabbatar ya ja sauran mutanen" daga haka ya shiga motarshi, sauran mutanen suka shiga motar da mutanen Dulma suke amfani da shi. Sai da yaga fitarsu, sannan ya take musu baya, yana jan Dulma. Har suka fitar daga Hill and Tim town, sannan ma'aikatan Ma'adinan ya fara fashewa da rushewa. Kome na wurin kamawa yake da wuta. Bakidaya ma'aikatan ya lalace ya kone, ya kuma rubta cikin ramin da suke hako kuzan. Yana hango rubtawan. Wani smirk yayi irin na tsantsanar mugunta da zalinci. Haka ya cigaba da gudun ganganci da Dulma, har ga shiga cikin garin Fiston ya tsaya a daidai kofar birnin. Ya sauka a motar, ya kunce dulma ya daura a kofar birnin. Sannan ya wuce zauna a saman motar. Yana kallon gawar Dulma har yau wutar da yake ci a ransa bai mutum ba, baya ji zai mutu. Kome zai yiwa mutanen ba zai tab'a wucewa ba. Domin bai ji ya huce ba.
Wasu daga cikin mutanen Shu'iba sun kai mishi labarin abinda ya faru, kamar zai yi hauka haka yake ihu, kamar ya fito daga maboyansa ya fuskanci Malik amma sun hana shi, domin babu Allah ya cikin al'amarin Malik. Yana ji yana gani Malik ya kashe mishi dan uwa, sannan ya rubuta a gefen fuskar gasar Dulma.
*Dan daudu idan ka gama gudunka, namiji yana jiranka* wannan abin da ya faru, ya sakawa Alhaji Nasr Hadejia, shakkar shigar Malik cikin lamarin, domin dai har ga Allah babu yadda za ayi su nemi taimakon dan daba, kuma makashi mara imani. Ko da yake a wani bangaren sun kammala aikin bude wurin shakatawar.
Chapter 12 · 0% Book details