← Book details Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 33

Sashe 16

Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Daukar karfen tayi tana nuna shi da karfen. "Kar na kuma ganinka a nan yankin daga yau, yankin Baba na ne tashi ka. " Dakyar ya tashi ya ja motar shi, ya kawo yayi ta jigilar kwashe mutanenshi ya zuba su cikin motar. Sannan ya bar wurin.
Damshi da dumi taji a hancinta, a hankali ta d'ago fuskarta zata yi magana, sai zubewa tayi a wurin, da gudu mutanen kasuwar kifi suka rufa mata, tare da daukarta suka nufi asibiti da ita. A lokacin Dr Saddikah ita ta tsaya akanta. Sai bayan awa awa daya ta fito daga kanta, tana kallonsu. "Yarinyar nan rayuwarta tana cikin hatsari, me ya faru?" Shiru sukayi kafin daga baya, suka bata labarin abin da ya faru. Ai idan ranta yayi dubu ya b'aci, yadda take fada kamar zata dake su. Haka yasa suka sunkuyar da kai. "Bamu da zabi ne, ba zamu so fadawarta hatsari ba"
"Gaskiya a kula da rayuwarta!" "In sha Allah!" "Abin da yasa nake magana, a kowani motsa jiki da fushi harsashin kara nutsewa cikin kanta yake. don Allah ku kula da ita."
Abun tausayi haka suka yi jigun-jigun, sai dare suka bar asibitin. Hmm tashin hankali wanda ba a saka masa rana domin kuwa sabon tashin hankali aka kuma haifarwa. Domin washi gari sai yan daba sun kai mota ashirin, lokacin ta farka domin har asibitin suka biyo ta. Lallai a fito musu da ita, suka fara bibiyar dakuna da aka ki fito da ita, da gudu Dr Saddikah ta nufi dakin tare da rufewa lokacin Ammyn Abbas tana bata abinci. Rufe kofar dakin tayi. "Dr lafiya?" Ammyn Abbas ta tambaye ta, "babu kome" dukar kofar aka yi da karfi, tayi maza ta fisgo hannunta suka fada ban daki.

A hankali ta cire hannun Dr Saddikah, ta ce mata. "Ammyna da Abbas kuma fa?" Fauce hannun tayi ta daki wurin key fita yayi ya cilla cikin dakin daidai shigowar su, sake dukar kofar tayi sai da ta balla. Cire piece na kofar tayi, tana faɗin. "Allah sarki me ya kawo ku?" Ta fada tana fitowa, nufar wurin Ammyn tayi ta shagwab'e ta ce mata. "Ammynay bani naci" jikinta na rawa ta shiga bata abincin tana ci. "Kee!" Yatsar hannunta ta kai baki ta ce mishi. "Dalla yi min shiru, sai na koshi waye ya gaya muku ana magana idan ana cin abinci." Gyada mata kai suka yi, ta cigaba da cin abincin. Har suka tsaya idan aka ga basu dawo ba, wasu ma zuwa suke kafin kace me sun cika dakin. Tana gamawa ta cewa Ammyn ."Ammyna bari na share musu tantama. Waɗannan suna bukatar kulawa, kai bani abin kunnan nan" mika mata yayi har da radion ta kura karar, sannan ta cewa Ammyn. "ki rufe shi kar ya ga abin da yake faruwa ya fara jin tsoro" a hankali ta juya, "zaku taka min baya ne, ko kuma zan tara muku nauyi ne?" "Mun zo yin dagga-dagga da namarki ne!" Had'a hannun tayi tace musu. "Idan na sake ku da hannu, Ni ce zan yi jinya gara na nime bulalar da zan iya gabatar muku da kaina." Karfen gadon ta shiga kokarin ɓallawa, sai da ta karyo shi, abin da ya basu tsoro kenan. Suna ganin kamar ba bil adam ba ce. Takowa tayi har gabansu, ta sunkuyar da kanta. Kafin ta d'ago kai sama jini yana zuba. Daga hancinta Idanunta rufe motsin takunsu kawai taji kanta yana sama, gyara rike karfe tayi koda ya iso kafin ya sauke mata,.ta daki mafitsaransa. Durkusawa yayi akan gwiwarsa ya fasa ihu tare da zubewa a gabanta. Take kansa tayi ta tsaya akan shi. "Mu cigaba ne?" Fita suka yi da baya-baya. Har suka isa wajen sai da sukayi kamar kafa goma a tsakaninsu, kafin suka tsaya, karfen wancan mutumin ta dauka hannu bibbiyu. Ta kalle jini na zuba daga hancinta, gogewa tayi tana kiran su, Dr Saddikah kamar ta fasa ihu. Ciwon yana ta'azzara ne. Abin tausayi yarinya ta koma kamar wacce aka kara mata wani abu. Da gudu suka nufeta babu tausayi ko imani balle jin kai. Haka suka rufeta da mugun nufi.
Ihun kartin maza kawai yaƙe tashi a wurin suke da yawa suke da ihu, ba mamaki na mutum ba ce, aljana ce domin a cikin minti arba'in, ta tara su a wurin. Karkarya musu cinyoyi da hakarkari. Masu nisan kwana da lafiya suka yi ta juyawa a guje. Bata kyale su ba haka tayi ta binsu tana kai musu duka. Har suka fito harabar asibitin, da gudu suka yi ta juyawa da motarsu, har suka bar asibitin. D'aga kai sama tayi tana son jinin ya tsaya. Kafin ta yanki jiki ta fadi.
<|=|><|=|>
*Present*
"Me ya faru da har ƙwaƙwalwarta ya kuma tabuwa? Kun manta halin da take ciki ne? Ya kamata a kula da lafiyarta domin kuwa rayuwarta tana cikin hatsari sosai."
"Babu wanda ya bata mata rai, sai dai a yan kwanakin nan, uzuri ya mata yawa bata hutawa kuma Hutawa tana cikin ka'idodin kula da lafiyarta, amma zamu kula da ita don Allah ayi wani abu!" Inji Ammyn. Tausayi Zeeno ya kuma shiga ransu. "Ita domin wani yayi farinciki ita zata fadi. Ban san yadda zamu yi da Zeenobia ba, mun bar wancan garin ne domin ita, yanzu kuwa rayuwarta ta kuma fadawa matsala!"

"Idan aka ce za a mata aikin cire shi, dole za ayi rasa rayuwarta, amma kuma dole a rabata da shi domin tana kara shekaru lafiyarta zata kassara sama da yanzu, idan muka yi sake zamu rasata."
"Dr Saddikah ya samu yi?
Chapter 16 · 0% Book details