← Book details Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 33

Sashe 25

Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ko kwana ɗaya baa yi ba masu kudi, suka shiga mishi sallama, last dai abin da ya faru shine wasu sun zo gidan sun mishi kashedi. Daga haka sai tsintar gawar shi aka yi ya rataye kanshi, duk da masu binciken gawa sun tabbatar da ba kashe kai bane, kisan kai ne. Haka ya d'aga hankalin Diana wacce bata kawo haka Aranta ba, sai da ta kusan zarewa, kafin Allah ya nufeta da dawowa dai-dai, karshe bayan rasuwar shi ta musulunta, ta koma Salsabilah,. Abin haushi suna wannan rayuwar aka kwace musu kome nasu, hatta passport da zai fitar dasu kasar an kwace haka yasa Malik ya shiga tashin hankali, ga Mamanshi da bata da lafiya. Haka wata rana ana ruwan sama, ta fara rawan dari yaron nan ya rasa yadda zai da ita, dole ya shiga niman wanda zai taya shi su kai Mamar asibiti be samu ba. Dole haka ya dawo, sai a wani tsohon wheelbarrow ya dauka ya sakata suka tafi asibitin, yadda zaka san an shirya kashe su domin da ya kaita babu wanda ya damu ya duba ta, sai ya ajiye kudi haka suka barta a dandaryar kasa, ya fita yana yawo kwararo-kwararo. Kafin a hanya motar Jahid Khan ya buge shi, bai damu da buguwar ba, ya tashi.....duk da ba yawa managing.....
*Assalamu alaikum......! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A'ishah. +227 84 50 64 76 500*
[28/08, 7:47 pm] usmanlauratu71: CINIKIN RAI....16
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
Ai dama kome a shirye yake, don haka Jihad Khan ya fito, yana faɗin. "Yarona! Ina zaka a cikin wannan daren? Ina iyayenka?" Girgiza kai Malik yayi yana faɗin. "Babana ya rasu, Ummata tana asibiti, zata mutu don Allah baba ka bani kudi a duba ta!" Ya fada yana me rike kafar Jahid Khan.
"Ai kai Yarona ne, dole a kula da mahaifiyarka, muje na ganta." Riko hannun shi yayi suka shiga motarshi, suka nufi asibitin, kallonta yayi in pitiful kafin ya ce. "Ina Director na asibitin nan?" Baki daya asibitin aka taru musamman Drs da nurses, "ku duba lafiyarta kafin na dawo!" "Ok Sir!" Suka fada, sannan ya rika hannun Malik suka fita. "Yarona zan baka wani aiki, kafin ka dawo za a kula da ita kaji." Gyada kai yayi. Daukar shi yayi har wani kofar gida, ya mika mishi ƙaramar bindiga. "Ka shiga gidan nan, akwai Hashim Zubair, ka harbe shi. Shine wanda ya kashe maka Babanka ya dauke maka dukiyarka. Ka tattara fushinka a zuciyarka, ka dauki fansarka!" Gyada kai yayi, sannan ya fita daga motar, ya nufi gidan ba tare da wani abu ba, ya buga ai kuwa lauyan babanshi ya bude mishi kofar, "A'a Malik kai....!" Sake mishi harbin yayi har sau uku. Faduwa Hashim Zubair yayi, a wurin bai shura ba. Shima kuma Malik ko da ya gudu, ya sami Jahid Khan yana jiranshi, don haka yana Isa wurin shi, Yan sanda suna cafke shi. "Shine ya kashe babban Lauyan nan ta fafutukar kwato hakkin talakawa, a tafi ea shi." Sake baki yayi yana kallon Jahid Khan. Har aka saka shi a motar yan sanda. Haka suka tafi da shi, a hanya yayi ta dambe da su har suka yi hatsari. Ya fita dakyar, daga nan bai tsaya ko ina ba sai asibiti, koda ya isa ya samu Mahaifiyarshi ta rasu, tsayawa yayi akan gawar har aka zo aka tafi da shi, ba a taba kai mutum gidan yari babu shara'a ba, sai akan Malik, tunda aka kai shi, ake dukanshi da azabtar da shi, sai yayi wata shida a dakin da babu haske ko kaɗan, sannan aka fito da shi. A lokacin Jahid Khan yazo yake bashi labarin shi ya kashe iyayenshi, shima anan aka kawo shi, tow makabarta shi ce, Malik bai ce mishi kome ba, domin a zaman da yayi cikin gidan ya koya mishi shiru ko nace mutuwar Iyayenshi ya saka ya koyi hakuri da shiru, wasa wasa sai da Malik ya kwashe shekaru sama da goma sha biyar a gidan Yari, an manta da tarihinshi a lokacin muka hadu da shi, amma kafin mu haɗu Malik ya gawurta a cikin gidan Yari, domin sai da ya kwace duk wani matsayi da masu fada a ji a cikin gidan. Malik ya samu karfi tun a cikin gidan yarin, domin Yaran da yake dashi a cikin gidan suka fito tow kasuwanci suka fara mishi, misali fasa kori, sayar da kayan maye, shiga harkan siyasa, Yaranshi sun yi karfin suna..
A lokacin sai da ya kai babu wani ne tarin matasa irinsa, gashi a cikin gidan ya karasa makarantar shi na secondary, ya kuma hada da matakin diploma a cikin gidan Yarin. A lokacin da na shiga cikin tura ni aka yi na kashe shi, domin yana gidan wani dan siyasa ya bashi aiki aka yi kuma aka samu nasara, jam'iyyar adawa ta tura ni na kashe shi, amma ban kashe shi ba, an yanke min hannu.

Dawo labari.
Kallon hannun shi yayi dungulumi ya ce mata.
"Malik Menk Jordan, shi ya yanke min hannu. Yarinyar ban tab'a ganin fusataccen mutane irin Malik Menk Jordan ba, domin hatta gashin jikinshi a fusace take, a tsaye-tsaye haka suke. Lokacin da na dawo na samu an daina yayi na, dole na koma gefe da Yarana, muna tab'a Kasuwancinmu.

A lokacin da aka kafa Jam'iyyar PKO Malik da kansa ya kafa ta a gidan Yari, sannan aka samu nasara, a take aka fitar da shi ta hanyar yan majalisunsa, yana fitowa ya saye duk wani kusan gwamnatin, kafin ya shirya tsaf, ranar cika Mayor Jahid Khan, a cikin Bainar nasi, Malik ya kashe shi da duk wani me taimaka mishi sai da Malik ya ga bayanshi, sannan ya shiga bibiyar makasan Iyayenshi, a lokacin da aka ce Malik ya kashe Mayor Jahid Khan, sai da ta kai kowa rufe gidan shi yake, domin kuwa garin Keivroto ya samu tashin hankalin da rikici, yadda suke kokarin zubda jini, yasa Malik shiryawa ya nufi cikin gari, aka yi ta bata kashi sa mutanen Jahid Khan, rigimar da ta janyo dole mahukunta suka dauke kansu, domin rigimar cikin gida ce, Malik sai da yayi ta bin manyan mutane yana kashe su a cikin gari, a gaban Jama'ar gari, haka yasa mutane suke mugun tsoronshi, da kace musu ga Malik gara mutuwarsu.

Sai da ya share Keivroto tass, sannan ya amso dukiyarshi, ya shiga harkan kasuwanci da siyasa kamar me, bayan shekara biyu, Khuldu Jahid Khan ya dawo domin fansa, a gaban jama'a Malik ya mishi dukar kawo wuka.

Wannan yasa shi daina fuskartar Malin gaba da gaba, ya shiga bibiyar shi ta baya, sai dai bai sha dadi ba, domin da Malik ya fahimci haka, sai da ya mishi illar da ya bar Keivroto da kafarshi. A hankali kome ya fara typing daidai,.kafin kuma Malik yayi hatsari bayan mutuwar wasu abokan Kasuwancinsu."

Shiru tayi kafin ta ce mishi.
"Malik bai da rauni ne?"
Kura mata idanu yayi kafin ya ce mata.
"Rauninshi Nuratu ce, ita din Marainiya ce daga gidan Marayun Demark, kamar kanwa take mishi, a lokacin yana da Yarinyar da yake so, Jalilah karshe an ce Jalilah ta sayar da nuratu ga wani Bature ya lalata mata rayuwa inda ake daurawa Malik sharrin yayiwa Marainiya ciki, kuma a haka Malik ya amshi cikin sai dai basu kasar nan, suna Demark."
Chapter 25 · 0% Book details