← Book details Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 33

Sashe 8

Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kana ganin shigarta kasan sai a hankali kawai, domin daga sama har kasa zaka gane abin ya motsa ne. “Zeeno ko zamu raka ki ne?” da ta watsa musu harara tilas suka janye kudirinsu nason lallai sai sun bita. “Paul fito min da bike dina.” jikinsa na rawa ya fitar, ya shiga karkad'e mata. Tana isa wurin ta saka key ta tashi machine din, wangale mata kofar gidan yayi. Ta cilla kan babban titi a guje. Ta ina zata fara ma? Ta ina zata shiga? Babban asibiti ta fara nufa, inda ta shiga bin lunguna da yake cikin garin. Har ta isa asibitin, shima da kyar aka bude mata kofar, tana shiga cikin asibitin ta wuce emergency room.
Mikewa Dundurosu yayi yana faɗin. “Xnoo!” takawa tayi har wurinsa ta kalli Chu-chu da take barci. “Ya jikinta?” numfashi ya sauke sannan ya ce mata. “Sunce zuwa dare zasu sallame ta, sai dai kuma ina ga an kama Black.” cizon leɓenta na kasa tayi sannan ta ce. “Ba gani ba ne, sun yi ram da shi ne, amma ai sun san mutane na, wani shafaffe da mai ne zai kama min iyalai na?” saka hannu tayi a cikin aljuhun wandonta, ta ciro katin banki ta mika mishi. “zan tafi ka tabbatar idan an sallame ku, ka isa lafiya ko kuma ku kwana a nan, bayan nan kada ka saka rayuwarka cikin kasada.” ta dunkule hannunta, shima ya dunkule na shi, suka dan naushi juna, alamar Goodluck.

Yadda ta fita bata tsaya ba, nufar shingen yan sanda tayi, tana zuwa kafe machine din tayi, ta nufe su. “Xnoo! Da fatan lafiya dai?” murmusa musu tayi sannan ta ce musu. “Ina dan gidana da kuka kama?” shiru suka yi, kafin suka yi kasa da murya. “Xno yana can babban office din mu, nasan Ammar yana can yana ƙoƙarin ganin an sake shi, ai ba zamu iya rike miki shi." Murmushi tayi sannan ta bar wurin. Kai tsaye babban office din yan sanda ta nufa, duk inda ta wuce babu wanda yayi yunkurin dakatar da ita, tana isa office din ta kafe machine din. Ta cire hilmet ɗinta nufi cikin office ɗin. Tana shiga ciki ta hadu da dan sanda da ya su a sake black. "Ranki shi dade, da Kanki?” “Eh ina mutumina?” shiru yayi sannan ya ce mata. “Kiyi hakuri amma.” gyara tsayuwarta tayi, sannan ta ce mishi. “baka ji me nace ba ne?”

Numfashi ya sauke, sannan ya ce mata. “ina jinki sai dai matsalar sabuwar ASP muka samu tana da zafin kai sosai.” dariya tayi sannan ta ce mishi. “Zafin kai fa? Ok ina take?” shiga cikin sosai suka yi don dama suna baƙin kofar shiga ne. Fitowar Asp Zulfa daga office ɗinta yasa suka tsaya cak. “Xno gata nan!” ƙoƙarin danne fushinta Xno tayi tana me saukar da murya. “Ranki shi dade, nazo niman belin Yarona ne.” kallonta tayi na wani lokaci. Kafin ta ce mata. “Kallonta a wulakance Asp tayi tana dandana wayarta. “Waye d'anki anan?” nuna shi Xnoo tayi.
“Ok wancan dan ta'addan masu tadda zaune tsaye? Ko ba shi ba ne?”

“Ina ga ke bakuwa ce a wannan yankin, muna tarban bakinmu da karammawa ce, sai gashi ke a rashin dace kinzo lokacin rashin sa'a. Please sake min shi, domin ya kai mara lafiya asibiti ne aka kama shi.” Zeeno ta gaya mata. “Meye shaidarku?" Ciro wayarta tayi ta mika mata, tana faɗin. “Asibitin da ya kai mara lafiyar ne suka zari kudina, sannan bayan nan idan baki gamsu ba zamu iya zuwa ki gani da idanunki!” mika mata wayar tayi tana tab'e baki ta ce. “wannan hujjar bai gamsar da ni ba, domin naji labarin kina cikin yan daban da suka yi kaurin suna?”

Cizon leɓenta tayi, tare da matse hannunta. "Yar sanda, ba bincike nazo ki min ba, belin Yarona na zo beli.” yadda Zeeno tayi magana ne ya bawa Zulfa haushi, ya Zeeno tana yar daba, mara yanci zata mata magana kamar wata me yanci, bayan ita kaki ne a jikinta. “Kai bude wancan cell din ka watsa min wannan mara kunyar a cikinsa na ga waye ya tsaya mata a faɗin garin nan.” dariya Zeeno tayi tana faɗin. “Ni ba fada nake nima ba, amma tabbas zaki yi kuskuren da zai janyo hankalin waɗanda suka tsaya min ba ni mutumina!” hannu ta kai da nufin hankad'a Zeeno. Cikin wani irin zafin nama,. Zeeno ta juyar da ita daga nufin hankad'ata, karshe ita ta fadi warwas. “Kinga yar sanda ba fada na zo ba, don Allah ki bani mutmina!”

“Kika kifar da Yar sanda a bakin aikinta? Lallai yau zaki sani!” Ciro waya Zeeno tayi ta shiga latsa wasu number, can kuwa aka dauka. “Yallabai gamu a Office din yan sanda, ta kama min Black kuma tana son lallai sai ta keta min jikimata." Kashe wayar tayi tana kallon Zulfa da ta kallo wasu irin kwagirin domin dukkan masu laifi wasu tika-tikan dasu.

Nufar Zeeno tayi, amma kafin ta iso an kira layin. “Hello yallabai?” shiru tayi. “Yallabai yan jagaliya ne masu tadda zaune tsaye fa, idan aka sake ta ai.” shiru tayi tana kallon Zeeno da ta koma daya daga cikin kujerun cikin office din ta zauna tare da fara fyeduwa. “Ok Sir!” ta fada ranta a matukar had'e. “Ke yar sanda! Ba gaba da gaba, ko ta baya irinki goma sai sun shirya, kinga da kira daya. Me zai faru idan kika kara aikata makamancin irin wannan kuskuren.” Takawa tayi har gabanta. “Tube jami'ai irinki nake a bainar nasi na zane mazaunan su, sannan na saka su, su lashe ƙasar takalmina.” ta wani d'ago mata takalmin kafarta, ta nuna mata tana murmushi. A fusace Zulfa zata nufeta. “Madam gaskiya kibi umarnin na sama dake, idan ba haka ba.” shiru tayi, tana gani aka bude Black. Zeeno ta riko hannunshi suka bar Office. Har harabar office suka nufa, ranta na soya tabbas yar sanda nan, taci albarkacin Mr Amjad, haushin da bata sauke a kan Zulfa ba, shi ta sauke a kan Black. Domin tsinka mishi mari tayi. Sunkuyar da kai yayi, “Kasan yadda ka zubda min da mutuncina? Har ni yar sandan can zata rufe? Me yasa baka kira ni farkon al'amarin? Kasan waye na kira ya musu magana? Kada ka kuma min wannan gangancin." Daga haka ta cilla mishi key din machine din, ta nufi wurin motarta. Daukar hilmet yayi ya saka, sannan ta shiga motar tana me tadda shi. Horn tayi me karfi da tashin hankali. Fitowa Asp Zulfa tayi ta zuba mata idanu. Sannan ta wani juya tare da d'aga musu kura. Fyaduwa sajan Barau yayi yana me dariya. Kallonshi Zulfa tayi ya daina, “Waye ya tsayawa wannan yarinyar da commissioner ya kira ni da na kyaleta?”
“Yar kunama kenan, yar karamar mace sai babbar kasada, tayi nata tayi na me karamin karfi. Yar jagaliyar da babu irinta.” juyawa tayi tana faɗin. “Akwai files ɗinta ne a Office din nan?” gyad'a kai yayi yana kallonta. “Muje ka bani.” dariya yayi yana faɗin. “Madam me zaki duba a cikin files ɗin? Ki rufe shi kamar yadda aka rufe domin babu wanda ya isa ya bude har ya kamata, kada ki manta halin da ake ciki na case din Prime minister.”

Wuce shi tai tana faɗin. “Ba ni file ɗinta." Haka ta wuce, duk yadda ya so ya mata bayanin wacce Zeenobia amma fir taki saurarenshi. Haka ya wuce ya shiga duba tsofin kundi har ya ciro mata, ya fita ta kai mata. Office ɗinta ya kai mata, tana zaune ya ajiye mata. Tana waya, da alama da babba take wayar sannan ta ce mishi. “Ok Sir Allah ya kawo ku lafiya, amma an samu zaman lafiya domin an dakatar da zanga-zangar babu wani abu, sai case din Prime minister. Naji kace Arshad Abdul Qayyum, zai zo don haka na ajiye kome cikin kulawa, babu abin da na tab'a tunda zaku wuce da shi. Capital Crud” shiru tayi kafin ta ce. “In sha Allah sir, amma a dan bani damar wani ayyukan please Sir akwai aikin da nake bukatar farawa." Murmushi tayi tana sosa goshinta.

“Ok Sir!" Ta fada a kunyance, domin idan na an gaya maka tana sa matukar kunya ba, ba zaka yarda ba don irin manta nan ne masu yanayi biyu kunya da mutunci, haɗe da zafi me yaji. Ajiye wayar tayi. “Sajan Barau ka kawo?” gyada kai tayi. Mika mata yayi a hankali ta amsa. Ta karkad'e shi tana kallonshi. “Jami'a na musamman zasu zo daga Capital Crud City, sune zasu amshi case din Prime minister.” “Ayya kice dama kwantar da tarzoma kika zo yi?”. Gyada kai tayi tana buɗe file ɗin. Hoton Zeenobia ne, me dauke da manyan rubutun sunanta. Zeenobia Nasr Hadejia. Kura mata idanu tayi kafin ta fara buɗe shafi na biyu.
Chapter 8 · 0% Book details