Sashe 2
Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
BOOK ONE 001 Keivroto city. Sau dayawa mutane suna amfana ne da abin da yake, zuwa gare su ba abin da suke tsammani ba, wani lokaci abin da aka samu shi ake iya ado da shi domin lullube wata rauni. Raunin da zata durkusar da mai shi zuwa faƙiri ba ƙaramar rauni ce ba. "Xnooooooooo!" Shi ne sunan da gungun matasa marasa ji irin ta suke kiranta da shi. Bude idanu tayi tana kallon silifin dakin. "Wayyo Allah na, bakin na rayu kamar Cinderella ba, ko na rayu kamar wata Barbe Queen, amma yau na kare a sansanin jagaliyawa."cizon lips dinta tayi tana buɗe window ɗakinta. "Wani dan iskan ne ya min kiran mafarauta? Zanci uban mutum idan na fito ku watse kafin na fito" "Allah ya huci zuciyar ki Yar kunama." Lumshe idanunta tayi, tana me rufe window din ɗakinta, ta nufi hanyar da zai sadata da cikin gidan. Daidai ana buga kofar. "Zenobia! Please open the door!" "Ke ba jiya Babanki ya ce kar ya kuma ganin ki da ni ba?" Ta fada a tsawace. "Mtseeeeeew abinci na kawo miki " "ko ba abinci ba, uban abinci." Ta wuce gefen drower ɗinta, ya dauko toothpaste da brush dinta. Kasancewar gidan Babban gidan hayace kuma irin me dauke da dakuna rututu ne, har da gidan sama. Ita tana hawa na uku ne. Ta fito daure da towel a saman kanta, domin Allah ya mata baiwar gashi. A hankali idanunta ya sauka kan Kawarta. "Xno ina jiran ki" dauke kai tayi tana tafiya abin ta, ita kuma ta shige dakin ta fara gyara mata, ƙasan gidan kamar kasuwa kabilu ne mabanbanta daga kowacce kusurwa na garin ƙasar *Gista*, tun daga hawa na biyu idanun jama'a ya fara hango musu Yar kunama take suka fara watsewa, ita din kamar zakanya ce bata tab'a yarda ta haɗa kanta da sauran, wasu mata biyu dattijai ne suka shiga wanke ban dakin tare da saka garin kumfa da maganin kashe ƙwayoyin cuta. Sannan suka dauraye ban dakin, koda ta iso. Amsar bokitinta wasu matasan yan mata suka yi aka zubo mata ruwan zafi, aka surka sannan aka wuce da shi ban daki. Shiga ban dakin tayi, tana kallon shi. " Inna ki rubuta abin da babu a gidan nan kafin nan da an jima." "An gama yar albarka." Ta fada tana juyawa, yau ya dace ta fara aiki amma sam bata jin aikin a kanta. Sai dai Alfarman da Mr Amjad yayi mata ya isa kome ya kuma isa ya saka ta fahimtar rayuwar ta zata juya, murmushi tayi tana kallon kanta, yo dakyar ta gama secondary school, bayan ta gama ta shiga college shima dakyar ta samu damar yin diploma a fannin Kasuwanci. Sai da Inna ta kuma karfafa mata gwiwa ta shima wai gudun kar a rena ta duk da haka bai hana ka fahimci, yadda take cin Uwar uban turanci ba. Idan.kana niman me tozarta turanci. Ba shakka Zeenobia ita ce za a fara bawa Award shi yasa ta kare mai da hankalinta kan dabancinta, jama'a dayawa na masifar tsoronta a waje, amma cikin gidan ita ke bin mutane da luma. Domin sune ita, sune rayuwarta, daidai da rana daya bata fatan ta nisance su. Ita tasan darajar su, shi yasa ko mutuwa zata yi bata fatan ya dauke ta akan idanunsu. Wanka ta fara ta fara jin ihun mutane, bata fasa ba sai da ta gama sannan ta fito. Kallon wani matashi tayi fuskar shi ya b'aci da jini alamar duka aka mishi. "Wani dan shegiyar ne ya dake ka Abbas?" Ta tambaya duk da tana can baya ne, darewa aka yi aka bata wuri. Juyawa yayi ya kuma juyawa. alamar irin dolo ne. "Abbashena waye ya dake ka?" "Wai... Wai ... Wai" takowa tayi ta rike hannunsa. "Gaya min!" "Wai don na dauki madara na bawa Hibba shi ne yan uwanta suka dake ni!" Ya fada hawaye yana zubo mishi. Mahaifiyar sa kan bata iya magana ba, sai share hawayen take. "Gaskiya basu kyauta ba, ai kowa yasan yadda yake son Hibba bai dace a ci zarafinsa ba. " Rike hannunsa tayi ta ce. "me kake so nayi musu?" "Ki gaya musu su daina duka na" rike hannun damansa tayi har dakin Mamarsa da take kuka. "Ammiy kuka kike ne? Na zata zaki daina kuka ai tunda Allah ya bashi rai da lafiya, kuma babban engeering ne, manyan kamfanonin suna niman sa amma ganin sa a haka suke tsammanin ba zai iya ba, sai dai ki sani ke ce kike karya mishi kwarin gwiwa. Daga yau Abbashena babu shegen da zai kuma dukanka" ta fada tana barin dakin. Kallon shi uwar tayi a raunane. "Mahaifinka ya ja maka wannan rayuwar, da bau cusa kansa cikin wancan rayuwar ba babu me cutar da kai." Cak Xno ta tsaya. "Me kike nufi Ammiy?" "Ba kome Zenobia" lumshe idanu tayi ta wuce abinta. Tana jin babu dadi amma na yau yafi na kullum yawa, tana shiga dakinta ya rufe tare da sake towel din. "Ke dai baki da hali haka kawai sai kin sakawa,mutane talauci hankalinki zai kwanta." Murmushi tayi ta cigaba da shirin ta, bata damu da Hafsah Ameen da take dakin ba. Yankar da yake kwance a gefen kafad'ar ta, take shafawa ta ce. "Hafsy? A ranar da kuka tsince ni, haka kuka same ni da wannan tabon?" "Eh da wannan oscar din muka same miki." "Hmm!" Shiryawa tayi tsaf sanye da riga da skit na American suit, dark green, sannan ta kwaso wasu kaca na sarkoki ta zuba a wuyarta, hannun ta kuwa kai kace wani gasar nuna zobuna ake, sannan ta dauko wani mahaukaciyar takalmin me bakin tsawo ta saka. "Xno! Office din zaki fara zuwa da wannan shigar kamar kunce hauka?". Kallon kanta tayi a madubi ta ce, "nafi tunanin daga turu nake madadin kuncen hauka." Ba a bin ta bashin bakar magana ko kai uban waye. Gefe guda kuwa Xno bata da damu da ado ba, ko da yake ai ba laifinta ba ne, rayuwar dabanci ya fi mata armashi sama da wani paint a fuskarta. Tozali da farar hoda ta shafa a fuskarta, sai lipglow da ta goga. A hankali ta kalli kanta. "Ina girmama namijin da zai." Juyawa tayi ta watsawa hafsy kallon banza. "Zanci mutuncinki" ta fada ba tare da ta bari ta karasa zancen ta ba. "Allah ya huci zuciyar Yar kunama!" Murmusawa tayi, sannan ta nufi hanyar waje. Itama Hafsy ya fito tana take mata baya. "Don Allah kar a takalo rigima, kwana biyu bani da kudin biyan beli." Juyawa tayi ta kalli aminiyarta ta ce mata. "Bani jakata" mika mata jakar tayi tana faɗin. "Allah ya bada sa'a first time in office!" Murmushin gefen baki tayi, tana faɗin. "Ba ni da lokacinki" ta nufi hanyar sauka kasa, riga da wando ne a jikinta, rigar palazzo pants grey colour sai shirt shima grey top din rigar black, sai sarkokin da ta saka a wuyarta. Asalin halittar gashin kanta, nad'e shi tayi bayan ta daure da ribom, sannan ta daura black turb akanta, wanda ya mata masifar kyau. A hankali take sauka a stairs din. "Ina kwana Aunty." "Lafiya lau, yan makaranta." "Barka da safiya Yar kunama" "Barka dai Mr Umar!" Har ta iso kasa, juyawa tayi tana kallon ilahirin gidan. "Yau ba wani abu ne sabo?" Da sauri kowa ya tawo in da take, suna me son duba sabon abin da take buƙatar son sani. "Babu Zenobia!" Lumshe idanunta tayi tana faɗin. "Ina Abbas?" "Yana daki" murmushi tayi ta ce mata. "Mami ki kula da shi!" Sannan ta ce musu. "Babu kome kuka ce?" "Babu kome Yarnan" "shi kenan, ku min addu'a yau zan fara aiki." Ta fada tana nufar wurin motarta, da wasu gungun matasa suke tsaye a jikinsa. Irin motar nan ce mara koda ko murfi caterpillar, ta shiga mutane hudu uku suka shiga baya, suka tsaya. Gefen drive ne yana jan motar. "Kai ni kofar gidan su Hibba!" "An gama!" Wucewa da ita yayi kofar gidan da babu tazara da tasu. "Amma Uwardakina akwai son rai, kin san dai Abbas ba lafiya ne da shi ba." Juyawa tayi tana kallonsa. "Sai aka yi yaya?" Shiru yayi bai ce kome ba. "Na zata kai me tausaya mishi ne? Ubansa ya gina wannan gidan ne domin saka haya, yadda zai tallafi rayuwar d'ansa daya tal, kasrshe ya mutu ba a san mene ne sanadi ba, ya kuma rabta sunan al'umma a cikin takardan gidan, kasan wahalar da muka sha kafin gidan ya zama mallakarsa? Kuma kana cikin gidan kana raye nawa kake biya a wata? Son of bitch?" Ta fada kamar zata kifa masa mari. Dai-dai isarsu kofar gidansu Hibba kenan. Ajiye jakarta tayi da yake kan cinyarta. Sannan ta nufi bayan motar ta, sauka daya daga cikin matasan yayi yana dadin. "Uwardakina me zan baki?" Kwagiri. "Mika mata driven yayi, bata amsa ba ta juya tare da nufar inda matasan suke. Mikewa matasan suka yi, tare da cewa. "Idan don wancan mahaukacin kika zo, tow maza ki juya." Jinjina kai tayi sannan ta ce musu. "Wani dan iska ne ya dake shi?" "Ai mune muka dake shi bakidayan mu!" "Kunyi kuskuren dukansa, bani kwagirin nan Dondurus!" Ai kuwa yaci sunansa domin irin labtaceccen kato ne na bugawa a mujalla. Ya mika mata kwagirin, cire top din rigar ta tayi ta mika mishi. "Uwardakina wannan aikin na mune!" Inji daya daga cikin matasan. "Black bari naci ubansu." Yes sunanshi ya dace da shi, idan muka yi al'akari da yadda ya kasance baki sosai, "hahhhh! Wai ita zata iya damu ne, an dake shi kiyi abin da zaki yi." "Uwardakina ki kyale su, baki san yana yin kwarewar su ba." Inji driven,Juyawa tayi ta watsa mishi kallon banza ta ce mishi. "Duk abin da na kasa a gabana bana jin tsoronsa, sai dai ban saka a raina ba. Paul!" Ta kira asalin sunansà0pa. Tana rike da bulalan, tana juya shi yadda zaka san ranta ya kai kololuwar b'acin, nufarsu yayi cikin zafin nama, ta shiga tsakiyar su. "Ke yar jagaliya, ki tafi idan ba haka ba zamu zane ki, mu miki tumbur." "Na yarda idan daya kanku yayi nasarar ko kwarzanar jikina, zan bari ku min duk abin da kuke so,