← Book details Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 33

Sashe 11

Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bana kwai na, sai da zakara don haka da ita zan amfana!"
--
A kan hanyarsu ta dawowa gida ne, suka tsaya a traffic jam. Yan sanda ne suke bincike, "Kai Xno ga mutuniyar!" Juya kanta tayi zuwa ga inda yake nuna mata, kafin ta tabe baki ta ce. "sun fito cin na goro!" Ta fada tana dauke kai, domin ta gama gajiya likis. Dama da gayya ita kanta Asp ta fito kan titin. Sake mutanen da suka tare take, kafin su Zeeno su iso ta saka an tare hanyar, dauke kai Zeeno tayi.
"Ina driving license din ku?" Banza suka mata. Ba ƙaramin kunya ta ji ba, domin ana ta wucewa da kafa, kuma ana kallonsu.
"Ina magana kin min banza!" Babu wanda ya d'ago kai ya kalleta, hannu ta kai da niyyar zata cire key din motar. Zeeno ya kai mata wani irin duka da bayan hannu, faduwa can tayi, kamar an cillata. Sauka daga motar Zeeno tayi tana me cire top din suit din jikinta, a hankali ta shiga nad'e hannun white shirt din jikinta tana faɗin.
"Kul ki ce zaki tab'a min mota ta, zan kyale ki ne domin kakin jikinki idan ba haka, kul ki kuma shiga harkata!" Mikewa Asp Zulfa tayi tana faɗin. "Kika saka hannunki a jikin Yar sanda." Wani juyar da kai tayi tana faɗin. "Idan ta kama na zane ki zan yi ki tsaya a bakin aikin ki."
"Da shi haka yana nufin duk wanda ya nime saita miki hanya, sai kin kashe shi dalilin da yasa kika kashe Asp Ayuba kenan?" Rintsa idanunta tayi, ta nufi Zulfa da wani irin sassarfa ta cukume ta. "Idan kika kara kiran sunan tsinannen can, sai ja tura ki idan na tura shi, ki bincike idan kin samu labarin wanda ya ga lokacin da na kashe shi, ki zo nan a gaban jama'a ki saka handcuffs." Daga haka ta koma cikin motar ta zauna. Wani irin kallon banza Zeeno ta aikata mata, tana mata gargadi.
*Past*
"Kai ku sake mishi zakunan nan!" Haka suka sakar mishi dabobbin. Yarda bindigar yayi ya nufi zakunan da mugun gudu, kamar yadda suka nufe shi. Oho faduwar gaba asarar maza, a fusace Mayuntan zakunan nan suka nufe shi, aikuwa aka rungutsume akayi wata kazamar arangama, a duk inda aka raya fansa, tow zaka samu tsoro da fargaba bai cika samun matsuguni a wurin ba. Haka ce ta faru da Malik, domin a duk lokacin da ya dunfaru wani abun da ya shafi fansarsa. Haka suka hautsine da wani irin fada, me tashin hankali. Kafin wani lokaci,ya watsar da gawarsu, ya mike yana karkad'e jikinshi yana kallon inda Dulma yaƙe. Hannu ga saka a cikin aljuhun wandon shi ya dauko cigarette, ya kunna tare da zukar hayakin ya hura a sama.......
*Hi......! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A'ishah. +227 84 50 64 76 500*
[8/28, 6:46 AM] Mmn Khaleel: CINIKIN RAI....
Beauty and the beast♡
Mai_Dambu
005
“Kai Shu'iba ka rufawa kanka asiri, ko a tashe ka da nakiya. Ko kuma a turo yan bindiga dad'i su alburushe ka.” har ga Allah maganar tayiwa Lalla Salmah zafi. “Shi yasa baku rabuwa da abin kunya a kowacce magazine ba. Ai gara Malik ya tsare kansa da dukiyarsa ce,ba mutumin banza ba ne." Tana gama fadar haka ta mike zata bar kwaryar Majalisar. “Ya tabbata dai yan PKO party basu da abin faɗa, tunda karen farautar da suke karewa ta kusan kare mishi. Shugaban majalisa a tsige Malik Menk Jordan kawai.”

Shiru tayi sannan ta cewa shugaban majalisar koli. “Yallabai kafin ka yankep hukunci ka fara nazari, idan kace zaka biyewa yan amshin shata zasu kaika su baro ka, su basu da nasu sai na wasu. Kullum ra'ayin wasu ke yawo a kansu banbancin uban nan gidansu da Ubangidan mu kenan.” daga haka ta fita ta bar kwaryan majalisar koli da hayagaga.

Tana fita ana mika mata wayarta, amsa tayi tana faɗin. “Elbashir ina ka shiga ka bar ni sa tashin hankali? Kasan abin da ya faru kowa?” amsa maganar yayi da cewa. _Ina sane, sai dai Malik ya hana ni dawowa ne, ya ce nayi fucus din matsalar gaba na, amma please ki tuntubi Mr Shatima, a madadina ya je ofishin jam'iyyar PKO yayi magana akwai lauya malik._

“Shi kenan, zan tabbatar haka ya faru.” ta fada tana me kashe wayar. Tasan dole yau ta isa Keivroto city kome dare tunda har Malik ya iya hana Elbashir Jamal Arab dawowa tow wannan shi ne lokacin da ya dace tayi kokarin ganin ta shigar da bukatarta. Sai dai izuwa yanzu take da damar shiga ga Malik ko dan Maidah tunda an soke zancen Nadra Shatima. Dama tun can ta tsani yarinyar sai kuma aka yi rashin dace Malik yayi rejected ɗin bukatar Shatima. Domin bata mantawa a lokacin yan mata dayawa sunso shi. Haka ko Wahiba da Wahida, basu amshi Nadrah ba. Shi kuma Malik yana tafiyar da rayuwarsa ne daidai da fahimtar Yaran. Bayan abin da zai tab'a ran su, shi yasa ya dauke su a garin Keivroto ya mai da su demark su yi karatu. Da wannan damar itama take amfani idan zata taso Gista ta tura mishi Maidah. Sai dai wani lokaci bata jin wani gamsashhen bayanin sun hadu ko basu hadu ba, ba kamar duk lokacin da Nadrah taje ba, tana samun ganinsa. Ko last year kafin Mr Shatima ya mai da Maidah Demark wurin su Wahiba da Wahida, Malik da kansa ya bashi Shawaran ya mai da ita wurinsu, sannan ya dauka rashin aurensu daga Allah ne, don baya son haka ya tab'a relationship ɗinsu. Koda yake taji a bakin Mr Khamis Shatima ne da bai da sirri, bai san itama burinta ta tura yarta ga Malik din ba ne. Murmushi tayi, izuwa yanzu ta koyarwa Yarta duk abin da zata kama zuciyar namiji, imma ta koya mata yadda zata iya daukar kowanni abu daga namiji, imma ya kama da affairs ne da namiji ta yarda, amma bata son yarta tayi mu'amala da wani namijin domin tana bukatar yadda yarinyar zata kama Malik. Tow amma me yasa Malik yaki auren Nadrah Khamis Shatima? Domin tasan kuma yarinyar tafi yarta kyau, nagarta da son jama'a. Banbancin ta da Maidah koda yake ai Barewa bata gudu danta yayi rarrafe, halinta halin Yarta. Koma mene ne ohon musu kanta ta sani, ba wasu ba yarta ta samu shiga ga Malik ko nawa zata barar zata san yadda zata cusa yarta ga Malik. Koda kuwa zata kama da bin malamai da bokaye ne sai sun mallake shi.
**
A cikin abun da bai wuce sati daya ba, aka d'aga curfew inda aka bar kowa, dakin Ammyn Abbas ta nufa, tana me shiru. D'ago kai Ammyn Abbas tayi tana murmushi. “Zainaba” a hankali ta iso gabanta tare da riko hannunta. “Gaya min akwai da wani abu ne?” kansa a sunkuye ta ce mata. “Ammyn aikin da na samu, sun ce min lallai dole sai dai na zama me gayyato musu mutanen da zasu saka hannun jari a kamfaninsu. Kaina ya kunce ban saba ba, ban iya mu'amala da.” murmushi tayi tana me zaunar da ita ta ce mata. “Inji waye ya ce ba zaki iya ba? Zaki iya mana, kika iya daukar na wasu ma balle naki, Allah ya sa'a.” “Ina son tsoro ne kar a samu matsala, na ga sun addabe ni da lallai na fara aikin ne, shi yasa na fara jin kamar akwai wata manufa a kasa.”
“Ki yarda a ranki zaki iya, sannan ki saka nutsuwa a ajiye jagaliyancin nan, ki fuskanci reality dinki, da yau Alhaji Badaru Daniyal yana raye kina nufin zai barki ne a haka? Shi ya so ya inganta Miki rayuwar ne, bai da burin ki rike wuka ko gatari.”

D'ago kai tayi Idanunta sun yi jajjur, har wani kyali suke, alamar ta tuna wani abin da ya shafe ta, kasa tayi da kanta tana faɗin. “Ba laifina ba ne, ayayinda ake tunanin mika ni ga gidan Marayu, shi yayi adopt dina a matsayin second child dinsa, ya tafi ya bar min abu biyu masu daraja. Ammyn don Allah bani da wani abin da ya shafi past dina ne, ina son sani wace ce ni?”
Girgiza kai tayi, sannan ta ce mata. “Bayan takardun da na baki, babu wani abu da na sani game dake, shima Alhaji bai san kome ba, sai abin da aka baki.”
“Shi kenan na gode ma haka, ba mamaki Allah ya turo ni rayuwarku ne, shi yasa na kare nan. Amma ina ji a raina kamar ina da wata rayuwar.”
“Allah ya sa.” Ammyn Abbas ta fada, tana me dauke kanta daga Zeenobia din, har tafi daga dakin.
Bin tayi da idanu, tabbas bata yi hankali da zata gaya mata kome ba, bata samu nutsuwar da zata gaya mata daga wacce duniyar take ba, amma bari tayi digging kad'an daga cikin rayuwarta da abin da suka sani.
***
Zeenobia
_Past_
Alhaji Muhammad Nasr Hadejia, Dan asalin garin Hadeja ne na Jigawar Nigeria, bahaushe ne, da kasuwanci ta shigo da shi garin Fisto kasancewar garin da yake tsubirin lord island, kasancewar gari me dauke da manya manyan duwatsu, halo dai hade yake da ruwa me kyau. Garin Fisto yana daga cikin jahohin Gista da ake yawon shakatawa da bude idanu, sai dai wani abu daya da yake maida garin baya shine kabilanci. Kabilanci yayi tasiri da garin, musamman yadda har turawa suna zuwa yawon buɗe ido.
Chapter 11 · 0% Book details