← Book details Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 33

Sashe 3

Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

idan kuma kuka sake sai na bulale muku, mazauninku." Ta fada tana kallonsu, tabbas sun san zata aikata amma abin kunya ce a gare su ana bada labarin kanwarsu tana soyayya da dolo irin Abbas. "kin ga Zeeno kin san." Zuba mishi kwagirin tayi a cinyarsa, tsalle yayi yana fadin "Amma da kin saurare mu ko, sai mu miki bayani" bata yi magana ba ta cigaba da zane shi, ganin yadda take watsar mishi da jikimarsa. "Zenobia don Allah ki kyale mu, ki shiga ki samu megida shi ya saka mu." Yarda bulalar tayi ta shiga cikin gidan, dattijo ne zaune, sai wasu kartin maza uku. "Yallabai barka da safiya." D'agi kai yayi ya zuba mata ido, kafin ya ce mata. "Kece Zeenobia!" "Eh yallabai nice Zeeno, Xnoo, Yar kunama." "Me yake tafe dake." Ya tambaye ta, cikin sanyin murya ta ce. "Ban zo nan da wata manufa ba, sai dai nazo na gaya maka cewa. Yarka tana son Abbas kuma shima yana sonta, Yallabai ina kaunar Abbas tun daga ranar da na fara ganinsa, amma sai akayi dace Abbas baya sona kasan abin da ake nufi da son maso wani karshen wahala. Amma ita Hibba yana sonta ne da dukkan zuciyarsa. Ko Mahaifiyarsa bata san yana son Hibba ba, amma ni ya gaya min, Yallabai duk da yana da lalura wallahi zai bawa Yarka duj wani farincikin rayuwa. Kaf kudin hayar da ake biya a cikin al'umma charity House nashi ce, a ƙalla ana biyan bera miliyan goma duk shekara. Idan luxury rayuwa kake so zai saya mata expensive stuff amma abu daya nake son gaya maka, idan kace ba zaka bashi ita ba wani abu bane, amma ka da a kuma aikata kuskuren dukansa." "Idan an dake shi me zaki yi?" Cikin fushi da dauki kofin jug din kwalba ta daki fuskarsa da ita, sai da yaji kamar yayi karo da bango ne, ta nuna mishi yatsa. "Ba da kai nake yi ba, wannan family issues ne." Sannan ta juya ga dattijon. "yau ranar sa'ata ce zan tafi wurin aiki, Yallabai xan tafi shawara daya xan baka shi ne, ka bashi Yarka ko kuma ka shafa kaji ba tattara su, sun fecce " sannan ta mike, ta bar falon. "Baba me yasa ka barta?" "Kasan yadda mutum yake ji idan abin da yake so ya rabu da shi? Exactly haka take ji, sannan akwai abin da na hango a kwayar idanunta, zata iya kome domin Yaron, tayi alƙawarin haka da zuciyarta. Ku kira min hibba " ••°°•• Tana fita ta mika mata rigarta black yayi, ta saka sannan ta zauna a motar. Daukar glass tayi ta saka, tana me cuno baki tana fitto wato feduwa. Suna isa trafficking jam, aka tsayar da motarsu. "Yan majalisar dokokin Keivroto suke wucewa a guje, sai da suka gama wucewa aka sake su. "Uwardakina ga motar Mr Amjad can." Kallon motar tayi, ta tab'e baki tana cewa. "Su suka sani" haka suka nufi Queen Elizabeth road. Kai tsaye wani katafaren Company suka nufa, sai hada hada ake kamar ana cin kasuwa a kofar Company. A hankali suka sulalle cikin compound na cikin kamfanin, suka yi parking a inda ake ajiye motoci. Sauka tayi Black ya mika mata jakarta Charles & Keith, a hankali ta maka a kafad'arta, tana tafiya ana bin ta da idanun. Saman building na kamfanin an rubuta, S..... digital art, tana isa bakin kofar aka bude mata kofar a hankali ta cusa kanta cikin building ɗin. Ware idanunta da suka sha tozali tayi tana kallon around na building. "Miss Zeenobia Nasr Hadejia!" Gyada kai tayi tana murmushi. "Kizo tare da ni " gyada kai tayi, sannan ta bi bayan matar da take sanye da dangalallen skirt iya gwiwanta. Elevator suka shiga ita da matar tana mata murmushi. Tana ganin matar ta danna number 9, a hankali yake walking around, tsayawa yayi aka bude shi, wasu yan mata ne suma ma'aikatan kamfanin. "Good morning Mss Mary!" "Morning helima morning Faither!" "Mss Mary an kawo sabuwar employee ce?" "Yes!" Dake babu wasa a fuskar Mss Mary yasa basu fadi abin da yake ransu ba, but sun kagu da su yi gulmarta domin azabar kyan diri da cikar halittar Zeenobia Nasr Hadejia wani abu ne da dole sai kaji a ranka. Infact there never met mace irinta ba. Suna isa floor dinsu suka fita, "sai an jima Mss Mary" tab'a juna suka yi bayan fitar su. "Ke she look familiar?" Inji Helima, zaro idanu Faither tayi tana faɗin. "Really?" "Eh na santa, but na manta inda na san fuskarta but na santa." Floor 9 suka isa, a hankali kofar ta bude, suka fito rights side suka nufa, tare da Mss Mary. A hankali suka isa wani kofa, Ciro card ɗinta tayi ta manna a jikin security door din ya bude, "waw" ta fada a kasa makoshinta, wani azazzben Office ne me masifar kyau da ɗaukar idanu. "Good morning Sir." D'ago kai yayi, ya amsa da "morning Mss Mary! Zeeno barka da zuwa " ya fada yana jin zuciyarsa da ransa ya biya da siffar yarinyar da take tsaye a gabansa, "moni sa" inji Zeeno, murmusawa yayi ya ce. "Mss Mary zaki iya tafiya ki turo min Mr Salim" "okay sir" mikewa mutumin yayi, yana faɗin. "Zeeno zauna, coffee ko caffeine ko tea?" "Coffee mara sugar!" Ta fada tana kallonsa. "Waw baki son kiba ko?" Murmushi tayi tana kallon office din."muna farincikin zuwarki wannan kamfanin me albarka, wanda muka bude ta kasa da mako shida. Sai dai har yau tana nan a yadda muka bude ta." Ya mika mata coffee ɗin, kallonsa tayi irin like how, ya ce mata."tunda muka bude ta muna bukatar masu daukar nauyin da wasu tallace-tallace kana da masu zuba hannun jari." Bude kofar aka yi wani kyakyawar matashi me tsawo da cikar halittar irinta maza ya shigo, ya ce musu. "Barkan ku." "Barkar dai Salim, ga Zeenobia Nasr Hadejia, Zeeno Xnoo Yar kunama ko?" Murmushi tayi ta daura daya a kan daya. "kwarai da gaske!" "Nice to meet you!" Inji Salim yana mika mata hannu. Itama mika mishi hannu hannu tayi, sannan suka sake hannun junansu. "Zauna Salim." Sauke numfashi MD na kamfanin yayi ya ce mata. "Mr Amjad ya bani labarinki, shi yasa muka ga dacewar mu baki matsayin me mu'amala da bakin mu da gayyato mana su, ta fuskar Kasuwancinmu." Hàdiye yawun tayi ya ce. "Ni kuma ya gaya min cewa, zaku bani aiki ta ɓangaren security service, domin shi ya dace da ni." "Haba Xno ba zamu dauke ki a matsayin wacce zata yi harkan tsaro ba, domin muna son kamfanin mu yayi achieve successful abubuwa Bama fatan wani abu mara dadi ya faru da mu, i hope you understand what I mean?" Tana jin abin da ya fada da turanci amma ita da ta tsani turanci taya zata iya rayuwa da abin da bata iya ba, babu boye -boye ta ce mishi. tace, "ba laifi idan kun bani shugaban security service. Hatta bera ba zan bar shi yayi shigo kamfanin nan ba, amma wend kuke ce min meka sifiki Ingilishi yu get rong idia, bikus na tsani Ingilishi ani mo!" Ta fada tana daukar jakarta. "Zeeno You can did it, zauna." "Sa kake ko saniya nace bana jin Ingilishi, i sa i no Ingilishi meye sai ma zauna da ku dole? Dalla ku bani wuri." "Idan baki amsa ba, zan kira Mr Amjad na gaya mishi, sannan zamu sauya miki damar haka, ko baki son rayuwar mutanen cikin al'umma charity House ya sauya ne? Zamu baku fili a gina muku makaranta da Asibitin da zai na kula da ku, sannan zamu dauki Abbas aiki a bangaren software!" Duk wanda ya zauna da Zeenobia Nasr Hadejia yasan Al'umma charity House da Abbas sune weakpoint, shi yasa suka kara tab'a inda take da yakinin aka. "zamu sauya miki rayuwa ki karbi aikin mu..." *Barka dai Ya kuke ya kwana dayawa! Gamu nan Top-notch mun dawo i hope zaku amshe mu hannu bibbiyu* #Zeeno #Beauty #Beast #RomanceS #Tycoon #WeatherMan #Top-notch #Jelousy #Cursed #Mai_Dambu [8/28, 2:22 AM] Maman Sadiq Da Khadijah: *CINIKIN RAI....*
Chapter 3 · 0% Book details