← Book details Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 33

Sashe 13

Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin bikin buɗewa ne, Iyalan Alhaji Nasr Hadejia suka tawo, daga nigeria. Aka yi bikin buɗewa cikin farin ciki da murna, har aka bude, dukkanin farinciki ya wanzu a fuskarsu. A lokacin ba laifi sun samu masu shigowa daga wasu ƙasashen yawon bude idanu, sai dai wasu abubuwan da suka faru kafin buɗewa wurin shakatawa. Kudin hannunsu yayi mugun sauka. Babu wanda zasu dauki ma'aikata da wasu abubuwan. Daga shi kansa Hadejian har Yamini, suna cikin wani irin matsi, sai suka yi decided amsar bashi daga banki inda suka nemi Mayor Fahad ya shiga cikin lamarin, shi kuwa ya ce musu. "Ai kuwa ba sai kun nemi na banki ba, shi mutumin da ya taimaka muku, yana badawa, kuma zai baku da Amana" duk da Nasr Hadejia bai so ba, amma haka ya amsa domin ya lura Yamini ya amince. Don haka ya saka a ransa, zai amsa amma matuƙar akwai ruwa a cikin zasu hakura. Don haka suka tsayar da lokacin da zasu je amsa,
**
*Present*
Sakarwa kanta, ruwa tayi tana tsaye a gaban shawa, baki daya kanta sarawa yake. Idan idanunta ba karya suke mata ba, tabbas taga wani abun da ya tsaya mata a kai, a lokacin da suka bar wurin yar sanda, akwai wani abu da ta san shi tsawon shekarun rayuwarta, daga baya kuma ta daina. Wani irin sarawa kanta yayi, tare da zubar da jini daga hancinta, tun shekarun baya take fama da wannan zubar jini. Sake ruwan tayi da karfi, tana me rike hancin, sai da ta d'ago kai sama, wani irin kara kamar na Harbin bindiga. Toshe kunnanta tayi, tare da zubewa akan gwiwarta. Hawaye ke zuba mata kamar an bude famfo domin dama idan ta fara irin wannan ciwon, ko a kaita asibiti. Ihu ta ta fara da karfi, wanda ya janyo hankalin mutanen gidan, har rige-rige suke na zuwa ɗakinta. Dakyar aka balle kofar ban daki, daura mata towel Ammyn Abbas tayi, suka fito da ita aka saka mata kaya, suka nufi asibiti da ita, a hanyar tafiyar ne Ammyn Abbas ta kira wata mata. "Dr Saddikah, gamu nan a hanya jikin Zeeno ya tashi fa " "Ok ku kaita zan zo yanzu." "Tow gamu a hanya." Ko da suka isa, an karɓe ta. Aka shiga bata kulawa. Kafin wani lokaci har an mata alluran da ya saka ta, barci. Lallai dan adam ba a baki kome yake ba, yanzu kake takama an jima zaka zama ba kome ba. Abin da ya faru kenan.

After all Dr Saddikah tazo, ta shiga duba matsalar. Sai da suka gama ita da sauran likitocin ƙwaƙwalwa, sannan suka fito maganarsu ɗaya ce, ta takura kanta da tunani ne, akwai abin da take son lallai ta tuna.
_Past_
Sun samu ganin Malik, har sun samu kudin kamar yadda suka bukata, sannan abin da ya kara sake musu jiki, haduwa da suka yi da wani mutum da ya ce musu.
"Nawa kuka cefanar da rayuwar ku? Mutane kala uku ne a duniya.
Na farko masu rauni
Na biyu masu karfi
Na uku masu bada umarni
A ko ina na duniya suna raye.
Suna kasuwancin su ne akan haka ga duk wanda ya kawo musu tsaiko su aika shi garin da ba a dawowa.... Silarsu mutane dayawa sun rasa wasu nasu. Wasu sun yi kuka, wasu sun mutu. A duk lokacin da aka tab'a su suna fada suna karawa Kasuwancinmu ne aka tab'a. Nawa rayuwarku take da araha kuka sayar musu? Lallai kunyi kuskuren shiga tsinanniyar dukiyar da bata da albarka sai tarin tsinuwar al'umma." Wannan maganar ya saka musu shakkar al'amarin Malik.
"Kusa ni ba karban dukiyar tsinanne bane mafita, biyan dukiyar tsinanne shaidani, ku gane rayuwarku ita ce fansar dukiyarsa ku maida mishi da kayansa. Domin baku yi magana da tsanannu ba. " Yadda suka yi cirko-cirko suna sauraren mutumin me zubin mahaukacin, basu san Malik ya tawo ba, sai da ya ce musu.
"Ku kyale shi, ku je mahaukaci ne!" "Eheee! Ni ne mahaukacin? Bayan saboda kai na rasa duniyar da nake ciki. Saboda tsanannen dukiyarka." Shiru yayi bai ce uffan ba, haka ya raka su Nasr Hadejia. Har suka bar garin, koda ya dawo kallon Mahaukacin yayi yana faɗin.
"Wai kai meye matsalarka da ni?" Tasowa mutumin yayi kamar zai dake Malik, ganin yadda ya taso, yasa Malik sunkutar shi, ya buga da kasa. Sai da kashin bayansa yayi kara.
Sannan ya juya zai tafi mutumin ya ce.
"Na hango iyakarka a cikin mutanen da ka yaudara,mutuwarka tana cikinsu. Kamar yadda aka haifa mana shaidani haka za a haifa mana waliyin da zai kashe ka." Dawowa yayi ya ce mishi.
"Zan zauna na jira mutuwata, matukar bai fito daga cikin su ba, kai tsinanne ne! Kai ku min waje da Mahaukacin nan"

-----
Destiny.

Bayan sun koma, kamar ba zasu yi amfani da dukiyar ba,haka suka daure suka yi amfani da shi, A lokacin Yayan Alhaji Nasr Abubakar ya zo daga Nigeria kamar yasan halin da ake ciki, ya zo mishi da wasu kudaden, dama akan bayan wata shida zasu maida kudin,. Sai gashi ko wata biyu ba a rufa ba, sun samu kusan rabin kudin don haka bayan tafiyar Alhaji Abubakar, wanda suke kira da Baffayi, suka hada dukiyar Malik suka fara shirin maida mishi, don haka suka fara tuntubar Fahad Albagwi akan zasu maidawa Malik kudinsa. A lokacin yayi mamaki domin kudin ba kadan bane, don haka ya ce musu .
"Ku kawo na maida mishi." Ganin yadda ya tsaya musu akan kome, so babu zancen zalunci ko damfara, suka dauki dukiyar Malik suka mikawa Fahad Albagwi. Suka tafi tare da gina rayuwarsu.
Ashe Fahada bai kaiwa Malik kudi ba, sakawa yayi a gaba ya cinye tass. Duk haka tun wata biyu saura yadda suka yi alkawarin, Malik ya fara tuntubar Yamini, shi kuma ya ce mishi ai sun turo tun wata hudu biyu ba, kasancewar tafiya ta kama shi zuwa Yemen. Bai gayawa Nasr Hadejia ba. Har ya tafi bayan tafiyar ne, Malik ya fara d'agawa Nasr Hadejia hankali. Karshe har Keivroto city yaje, amma babu wani abu me dadi, haka ya dawo. Kusan a lokacin Malik ya fahimci Fahad ya cinye mishi kudi ya gudu, sannan ya jefa mutanen da babu ruwansu cikin zancen yayi alƙawarin ba zai kuma takuwa musu ba.
Haka suka rabu, sai dai ko sati ba ayi ba, wasu mutanen suka zo aka kwace wurin shakatawar da sunan Malik ne ya turo su. Wasa wasa sai da ta kai hatta gidan da Nasr Hadejia yake an kwace kome na shi, ana cikin wannan yanayin ne,Yamini ya dawon yamini al'amarin ya kara kazamta domin a lokacin rayuwarsu ta zama mafi muni, domin barazana ake musu za a kashe su. Gashi a lokacin suna son ganin Malik abin ya ci tura. Bayin Allah nan sun ga rayuwa da iyalansu.
Wani dare me cike da tashin hankali, aka kawo musu hari, wanda yasa suka kora yaransu, amma ban da daya daga cikinsu, duk da sauran Yaransu gudu, Zeenobia bata gudu ba. Domin akwai shakuwa a tsakaninsu da iyayen. Amma sauran yaran suka gudu, ita kan bata gudu ba, koda mutanen suna zo buɗe musu wuta suka yi, a sanadin haka, harsashi ya shige mata kai. Faduwa tayi cikin jini don shekarunta basu wuce bakwai a duniya ba, abu daya ta rike *Wannan shi ne sakamakon Cinikin rai da kuka yi tsakanin ku da Malik, kunci dukiyarshi ya ci rayuwarku, Malik baya yafe dukiyarshi ko cikin uwarka ka shiga sai ka amayar da shi*
Daga wannan bata kuma sanin kome ba, daga wannan ƙwanciyar, sai da ta kwashe kwanaki ashirin a Asibitin. Kafin ta bude idanunta a wani dokan daji. A nan rayuwarta ta tabarbare, babu abin da ta tsana kamar karar bindigar. Kasancewar tana hannun yan ta'addan da suka kashe iyayen, su kansu basu damu da kansu ba. Balle ita, haka tayi ta kananun jinyar har wani rana da ruwan sama ya tsinka dam ya shigo gari, a lokacin ruwa ya korota bakin gaba, Alhaji Badaru Daniyal yana aikin aikin sayar da kifi, domin sana'ar da ya gada ne tun iyaye da kakanni. A wannan lokacin da ya same ya yi kokarin shigar da hukuma har aka mata jinya a hannun wata likitar ƙwaƙwalwa, jinyar da taci magudan kudade, tunda ta samu lafiya sai ta koma shiru-shiru. A kasancewar garin kusan rayuwar dabbobi ake wanda yafi karfin wani ya kwace abin hannunshi. Akwai wani azzalumi a bangaren garin da ya addabi Alhaji Badaru Daniyal, kullum sai ya zo ya kwace kudin sana'arshi.

Wasim sunanshi yana amfani da sunan Malik, yana.cin karen shi babu babbaka. A wannan lokacin duk inda Alhaji Badaru ya saka kafa, Zeeno da Abbas suna tare da shi. Ana haka ya tab'a zuwa ya saka Alhaji Badaru a gaba sai da ya bashi kudin. Kallon shi Zeenobia tayi, haka ya wuce shi da Yaranshi. A hankali kullum sai ta ganshi. Ranar da yazo babu kudi yasa a rufe Alhaji Badaru da duka, a gaban su Zeeno. Bayan sun gama suka tafi. Kallon su Zeeno tayi. Kafin suka nufi wurin Alhaji Badaru, d'ago shi suka. "Sannu baba, ba zasu kuma zuwa ba." Ta fada, tana me shiga shagon ta dauko danko. Ta gyara shi sannan ta ja. Bakin Ruwa ta tafi ta tsunto duwatsu....
*Hi......! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A'ishah. +227 84 50 64 76 500*
[8/28, 6:46 AM] Mmn Khaleel: CINIKIN RAI....9
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
<<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>
Yau babu editing
Chapter 13 · 0% Book details