Sashe 5
Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
ya shiga cikin motar ya dauki kiran. "Ranka ya dade." _Kayi kuskure Prime minister, sauka lafiya_ kashe kiran aka yi, wasu mutane da ba asan daga ina suke ba, suna zuwa suka budewa janye p.a da driven, suka budewa motar prime minister wuta, sai da suka tabbatar da ya kama da wuta, sannan suka wuce a babur dinsu. Lokacin dasu Mr Amjad suka fito, ganin motar prime minister duk da jami'an tsarosa bai hana a kashe shi, an tashi motar da wuta ba, take duk suka juya kowa ya cikawa bujensa iska, wannan tashin hankalin ba karamin firgita Mr Amjad yayi ba dole tasa ya koma kamfanin S digital art. Yana shiga bai tsaya parking me kyau ba, ya nufi cikin kamfanin, a firgice yana ji kamar ya tsula fitsari a jikinsa. Kai tsaye elevator ya shiga, sai da ta ganshi cikin ya tabbatarwa ya tsira, ya sake ajiyar zuciya. "Wannan wacce irin masifa ce, taron dangi akan Mayor Malik Menk Jordan ba shi ne mafita ba, tabbas." Wayarshi ce ta yi gunji, sai da ya zabura, kamar zai gudu kafin ya tuna ai wayar shi ce take tsiwa domin da zasu shiga taron ya sakata a gunji. Dauka yayi yana faɗin. "Hello!" _Kada ka karya da abin da ya faru, ai dama ba iya nan ne shirin ba. Ka fahimta ko_ "Ni wallahi da zaka cire ni a cikin wannan lamarin da naji dad'i, Tunda aka iya kashe babban minista akan idanunmu, bamu iya me kake tunanin zai faru? Ku shafa min lafiya" ya kashe wayar, yana isa floor 9 ya bude kofar, jikinsa yana rawa ya nufi office din MD, kamar wanda aka koro shi ya isa office din, "ku bani ruwa ina jin ƙishirwa ne" mika mishi ruwan Salim yayi, sai da ya shanye ruwan tass, ya nime kari. "Sir lafiya?" Ajiye goran yayi ya ja kujera ya zauna, duk suka zuba masa idanu. "Zeeno baki tafi ba ne?" Mikewa tayi tana faɗin. "Eh Yallabai Amjad. " Sauke numfashi yayi ya ce. "Hussain wani matsayi take bukata ma?" "Security service!" "Ya miki haka?" "Eh yallabai!" Kallonta yayi ya ce mata. "Zeeno naso na baki matsayin da zaki na, nimo mana manyan mutane suna saka hannun jira ni a kamfaninmu, na sha gaya miki ke kyanki shine jarinkie, akwai mata dayawa da suke niman matsayin da kika taka, Zeenobia idan har kika amshi security service, harajin da gwamnatin jahar Keivroto take amsa a hannunku duk wata ba zai kai ba, zaki cigaba da bangar siyasa ne? Shekarunki nawa?" Sunkuyar da kai tayi kasa ta ce mishi. "Ashirin nake!" "You see! Kiyi amfani da damarki, akwai Mss Mary zata hadaki da Dauduwa, ta kware a fannin sauya salon mutum da fasalinsa, albashinki dala dubu dari uku, kudin US. A cikinsa zaki samu dala dubu hamsin ki biya kudin haraji, me ya fi miki." Juya idanu ta yi, ta ce mishi. "I,m satifai, idan har zaku bani dis moni, I kan do anitin!" "Yes good gurl yanzu ya yarda zaki iya, tunda kika yi magana da turanci, Hussain bani list na sunayen nan!" Ciro mishi kundin yayi ya mika mishi, a hankali ya bude yana kallon shi. "Ikon Allah kace har ka tura baki daua saura daya ne kawai ya rage?" "Yes Chairman na tura baki daya, wanda ya rage na Mayor Malik Menk Jordan ne!" Sarawa kanta yayi, ta dafe da karfi. "Lafiya!" Suka tambaye ta, "lafiya lau! Zan tafi." Mai da kundin yayi ya ce mishi. "Ajiye akwai dayan fa na baka, bani na bata!" Bude drower din yayi ya dauko mishi wani kundin. "yawwa Dauduwa zata gayyace ki, ga wannan su zaki fara jaraba sa'arki akansu." Juya Idanunta tayi ta ce mishi. "Wancan na farkon fa da ka mayar da shi?" A razane ya ce mata. "Wancan ai konawa zamu yi, kai Salim dauka ka je ka kona, kunna mana tv ta ji abin da yake faruwa, sunan da yake jikin wannan kundin bala'in duniya ne da tashin hankali ke yarinya ce, da babu ruwanki. Kada ki tsoma ranki da zuciyarki cikin wannan lamarin. " Murmushi ta yi ta ce mishi. "Tow amma kada ka kona, bari na ga yadda zan ji da wadannan zan dawo kansa." "Anya zaki iya?" Kunna tv aka yi ta juya tana jin labarin. _A yau garin Keivroto city ya tashi da mummunan al'amari da rabon a fuskanci haka tun shekaru talatin da suka wuce, lokacin kashe Mr Jahid Khan mahaifi ga Mr Khuldu Jahid Khan, me manyan kamfanonin hakkar ma'adinai, kuma Uba ga jami'iyyar adawa ta CDL civilian democrats labor, bayan nan ba a kuma samun tashin bom haka ba, sai dai shaidun gani da idanu sun ce wasu matasa hudu suka gani da babura, inda suka sauka suka idda mugun nufinsu, tare da kashe Mai girma Prime minister, a halin yanzu ana danganta mutuwar da Shahararren attajirin ɗan kasuwa, mai girma Mayor Malik Menk Jordan, wanda aka tabbatar da cewa anyi taron nan ne domin a kawo karshen mulkinsa inji wata majiya. Idan baku manta ba, Mayor Malik Menk Jordan shine mutum na farko da yake da kashi casa'in a na kamfanonin a garin Keivroto city, sannan yana da sahalewan shuwagabannin Kananan Hukumomin ɗari da shida, bayan nan dan kasuwa ne da ake zarginsa da hamdama da babakere, ga abin da wani ganau yake fada_ sako wani murya suka yi. _Gaskiya idan ka cigaba da barin Mayor Malik Menk Jordan yana abin da ya gadama, wata rana Keivroto city zata zama makabartan binne mutane amma ace babu wanda ya isa taka mishi burki sai abin da yaso, fisabilillahi taya za a rayu?"_ Kashe tv Salim yayi ya ce. "Da ina jin labarin Mayor daga nesa ne amma yau da naji ya kashe prime minister na yarda mutumin nan shaidani ne, Zeenobia Kinji ko?" Kallonsu tayi tana faɗin. "Ya naga kun razana, shi ne ya baku tsoro? Ni kuma gani nake ba kome ba ne." "Ke ki raba kanki da masifa Mayor Malik Menk Jordan ba kanwar lasa ba ne...... Zeeno #Beauty #Beast #RomanceS #Tycoon #WeatherMan #Top-notch #Rumors #Jelousy #Cursed #Mai_Dambu [8/28, 2:22 AM] Maman Sadiq Da Khadijah: *CINIKIN RAI......* Beauty and the beast♡