← Book details Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 33

Sashe 27

Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai bayan isha ta farka, kanta sayau ta farka, a hankali ta nufi banɗaki, sai da tayi wanka da alola, tazo ta gabatar da sallah magariba da isha. Sannan ta sha fresh milk, ta koma saman gadonta. Ta zauna har karfe daya na dare, tana zaune sai a kawai ta fara jin motsi me matuƙar hatsari, a hankali domin motsin da bai da hatsari da karfi ake yin shi, motsin da ake cutarwa kuwa a tsanake ake yinshi.

Dauke wutar gidan aka yi baki daya, shiru tayi tabbas ita ke nima, mayafi da dauka ta rufe fuskarta, a hankali ta bude kofar, watsa silallar da ta dauka tayi a wardrobe dinta. "tak-tak⁴!" Taji motsin kafarta, a hankali ta koma dakin, koda suka zo ganin kofar a bude, yasa suka shiga da wuƙake a hannunsu. Rufe kofar tayi bayan sun shiga dakin. Wato, baka jin kome sai karar kartin maza. Kamar zata hallaka su, sai da ta musu dukar kawo wuka, sannan bude kofar. Shiga duba gidan.
Basu nan, kafin ta nufi kofar dakin su Black, ta tashe su, dama a bisa ka'ida babu wanda ya isa ya fito kome ya faru basu fitowa sai ta basu iznin. A hankali suka bude. "Ku haura sama ku dauko min wasu yan iska a saman ɗakina." Da sauri suka nufi dakin haka suka fita da su, aka jibga su a cikin motarsu, sannan ta shiga motar har zuwa kamfanin Menk Jordan, taje ta ajiye su. A hanyar dawowarta suka hadu da ASP Zulfa. Dauke kai tayi kamar bata ganta ba, tsayar da motar suka yi.
"Ke sauko daga motar, muje Office din mu!" Fitowa Zeeno tayi tana faɗin. "Me nayi?" "Ki bawa hukuma hadin kai, muje." Janyo hannunta tayi, tana faɗin. "Ki bar ni na tafi, mun bar gida babu wani me iya kare su daga wata masifar." Juyawa Zulfa tayi tana faɗin. "Kin tab'a tunanin bayanki?" Fisge hannunta tayi tana me juya bayanta. "Me ya hada ki da yan bakar daba?" Shiga motar tayi, tana faɗin. "Wannan matsalata ce" daga haka suka barta a wurin, suna isa gida suka shiga bin dakunan. Suna dubawa sai da suka tabbatar kome normal, sannan suka koma daki suka kwanta.

★★★
Baki daya wannan al'amarin Elbashir, Malik ya bari da chakwakiyya, domin bai tab'a ganin yarinya me taurin kai yana bashi, turawa Malik sakon yayi.
*Assalamu alaikum! Ina kwana Malik yarinyar nan fa bala'i ce."
_Lafiya lau, ka kawo min ita._
*An gama*
--------- Zeenobia bata nime Elbashir ba kuwa sai da ta cika wannan lokacin, kuma bai kuma turo mata wasu yan daban ba, haka tayi ta zuba idanu, karfe biyu na rana aka kira number ta, dauka tayi tana faɗin. "Malik Menk Jordan ne?" "Baki da tarbiyya ne, yau karfe tara na dare mu haɗu a bakin Waterfall, zamu isa Island"

"Hmm!" Ta fada tana lumshe idanunta, a hankali tayi ta niman wasu abubuwan ta, kashe kiran yai, zobenta me dauke da camera, sai abin wuyarta me dauke da Camera. Kafin wani lokaci ta ware kayan da zata tafi ganin shi, ta kira Amjad. Ta gaya mishi halin da ake ciki, bakiɗaya tsoro ta bashi, domin be tab'a ganin hatsabibiyar Yarinya irinta, yana da labarin abin da ya faru, domin shi ya saka mata tracking camera a motarta, a kan idanunshi fadar farko ya faru, tsabar tsoro sai da yayi fitsari a wandon shi, tabbas idan ya sake tasan abin da yake shiryawa sai ta babbake shi da ranshi domin Zeenobia ba zata yafe mishi ba.

"Hmm! Ina ga ko zaki hakura da Malik Menk Jordan din nan ne?" Ya fada mata a sanyayye. "Karya kenan! Wallahi tunda aka kai wannan matakin ai an gama kome sai na hadu da shi."
Kamar zai yi kuka ya ce mata, "Don Allah a hakura da Malik din nan, kada ki manta mu muke nima, amma ace muke bin shi da yaki kamar akwai kasada hakan!" Murmusawa tayi tana faɗin. "Ban tab'a fail mission ba, duk abin da na saka a raina sai na cika shi don haka akan Malik Menk Jordan ba zan fara ba, kuma dole ya saka hannun jarinshi a kamfanin mu!.............._Hhhhhhh, a haduwa da Malik ya zama Jidali!_
*Assalamu alaikum......! Guys wannan littafin na kudi ne! 500₦ normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A'ishah. +227 84 50 64 76 500*
[30/08, 8:42 pm] usmanlauratu71: CINIKIN RAI....18
Beauty and the beast.
Mai_Dambu🌚
<<<<<<<<<<<|=|>>>>>>>>>>>
Kamar ya sake zawo a wandonshi ya ce mata. "Zeenobia ayi haka a hakura da shi kawai." "Bata lokacinka kake kawai, amma tabbas sai na ga Malik duk abin da zai faru sai ya faru!"
Tabbas yaso haka, amma bai tab'a zata haka abin yake ba, domin ta ga Malik duk ta haukace, fisabilillahi sai kace akanta aka fara samun matsala, kome sai taci da karfi, sai kace jikar iliya dan mai karfi, gaskiya ba zai yarda da wannan zancen ba.
"Chairman kayi hakuri, amma na yanke kuma haka zan aiwatar da abin da nayi niyya." Daga haka ta kashe wayar tana me kallon wardrobe dinta, tabbas dole ta kure a daka domin zata gamu da Malik, domin bata son ta isa wurin shi yayi mata kallon bata kai wacce ta dace da ya hadu da ita ba. Kallon madubin mirror dinta tayi
Ta juya tana kallon bayanta, d'aga pillown kwanciyarta tayi tare da kwashe atm dinta, ta dauko abaya ta daura, sannan ta fita shiga motarta tayi tana faɗin. "Dole yau na gyara kaina da jikina." Ta fada tana bawa motarta wuta.
Ita kanta tana jin wani irin d'auki na son ganin gawurtaccen zakin da ya hana kowa sakat, so take ta ga yadda ya samu damar yake bugawa kowa mulki kamar masarauta. BINTUN BATUL SALOON WORLD AND SPAN.
Gyaran jikin da saloon ake a shagon, kamarsu dilke, lalle, da Makeup. Ba karamin wuri ba ne, domin yaran masu kumbar susa ne, da matan manyan suke zuwa wurin. A hanyar titin da zai kaita wurin suka hadu da ASP Zulfa. Bin motar tayi da idanu, a hankali ta bude file din gabanta. "Sajan Barau yarinyar nan, me yasa bata da kamun kai?" "Madam bata da laifi fa, haka iyayenta suka watsar da ita, kuma ta daura rayuwarta a kan haka!"

"Allah ya kyauta" "Amin" ya fada.

★★★
Demark
Zaune suke a dinning room, kowacce da abinda take bukata. Kallon juna Wahida suka yi da Nadrah. Suka dauke kai, "Wahiba ina Maidah?" D'aga kafad'arta tayi tana faɗin. "Tana can dakinta!" "Atikah ajiye abincin ki je ki kirata" domin yau ta lura Wahiba bata jin yan surutun.
Lokacin da Atikah ta isa dakin, ta samu tana shiryawa ne, cikin girmamawa ta ce mata.
"Jaddah tana kiranki!" "Tow gani nan" ta fada tana gyara zaman yan kunnenta. "Tow!" Atikah ta ce mata, a hankali ta juya ta cigaba da abinda take, sai da ta gama sannan ta shiru tana tuna maganar da Lalla Salmah ta gaya mata jiya.
_Ni ban aiko ki, ki zama yar kallo ba ne, na aiko ki ne domin ki rabe Malik, Jalilah zata miki kome, domin itama tana da fushin Malik bana son ki gaya mata gaskiya. Kada ki sake Nadrah ta rena ki domin zan mugun sab'a miki._
Ta rasa yadda zata yi da ranta, yau kwana biyu da zuwanta, idan ta cire Wahiba da take kulata, sauran babu me kulata kowa ta kansa yake, a hankali ta fito a dakinta jikinta a sanyayye. Koda ta isa dakin cin abincin, baki daya hankalinsu na kan abincinsu. Zama tayi ta fara kokarin zuba abincin. "Ki sake jikinki, nan ma kamar gida ne. Ki daina zaman a daki kamar wata bakuwa." "Hmm! Kin san bakon da yazo birni daga kauye dole ya koma dodon kanshi." Juyawa Nadrah tayi tana kallonta, domin itama yau da safe Babanta ya kara mata magana, akan lallai ta samu shiga ga Malik. Domin an turo Maidah ce, domin ta samu Malik. Yadda ya tsara mata kome, da yadda zata na dragging din Maidah har ta ji ta gaji ba zata iya shiga rayuwar Malik ba.

Wahiba da Wahida, basu kai su shekaru ba. Amma kuma suna sane da cewa Dad ɗinsu anyi maganar aurenshi da Nadrah aka fasa. Amma kuma dawowarta wurinsu yasa baki daya suke shiri da ita musamman Wahida domin tafi Wahiba kirki da saukin kai, amma kuma idan ka gansu su uku, zaka dauka cewa halinsu daya ne.
"Jaddah kin gayawa Dad saura kwana biyu, Birthday dinmu?" "Kici abincin zamu yi magana idan na gama!" "Na koshi!" "Kin san dai ba zai saurare ki ba, idan baki ci abinci ba." "Jaddah don Allah ki saka baki ni na gaji da Demark mu koma Keivroto kinji.!" Inji Wahiba. Kallonta yan matan suka yi, ta saka fuska kamar ba ita tayi magana ba, dama ba gwanar magana ba..
Chapter 27 · 0% Book details