← Book details Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 33

Sashe 10

Cinikin Rai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Washi gari kuwa Yamini shi da kansa ya taso ya dauki Alhaji Nasr Hadejia, izuwa farfajiyar gidan gwamnati. Sun taras da mutane, musamman manyan baƙi don haka suka tsaya su jira. Bayan kamar minti Talatin sai ga sakataren Fahad ya fito dake an isar mishi da yayi baƙin. Duk da kasancewar sun same mutane a wurin bai hana sakataren isowa wurinsu ba, ya ce musu.
“Ku iso ana kiranku.” mikewa suka yi, tare da bin bayanshi, a cikin ofishin Mayor. Cikin girmamawa da mutuntawa Mayor ya mike tare da tarbansu yana faɗin.
“Malik sune mutanen da suka zo da nufin raya garin Fiston, amma Shu'iba da Dulma sun hana su, har nan suka zo suka min kashedi. Malik na kira ka ne, domin ka taimakawa bayin Allah nan, suna san cigaban jahar nan ta fuskar Kasuwancinmu.” duk da basu ga fuskarshi ba, amma baki daya basu wani gamsu da shi ba, domin kuwa ba a niman taimakon dan daba akan yan daba yan uwanshi. Hadin kai ne dasu, d'ago hannunshi me dauke da zobban ya yi musu wani alama.
“Wai ku gabatar da sunanku?”
"Aswad Yamini, wannan abokina Alhaji Muhammad Nasr Hadejia.” a hankali ya juyar da kujeran ya zuba musu idanu, mutum ne mai tsannanin kwarjini da cikar halitta. Mutane da matukar ka kalle shi sau daya sai ka sunkuyar da kanka ƙasa. Domin yanayin zubinsa kamar zubin zaki ne, rintsa idanun Yamini yayi yana jin wani irin yanayi. Domin kallo daya yayiwa Malik ya hautsina mishi tunani, banbancin shi da Nasr Hadejia da ya kuma kallonsa ido ciki ido har sau biyu. Duk da wannan yanayin bai hana shi jin kamar ya zuru da gudu ba.

“Had'ejiya ta Jigawar Nigeria?” da sauri Alhaji Nasr ya d'ago suka kara kallon juna a karo na uku. Mikewa yayi yana me fashewa da dariya, Fahad Albagwi ka had'e ni da dan uwana dan kasar kakana. Ai ni na samu aboki waye ya isa ya ce ba zasu gina wurin shakatawa ba. A shelantawa duniya na tsaya musu. Ai ko don albarkacin dan kasata na tsaya musu. Yamini kai ma ɗan uwana ne, domin Mahaifiyata yar yankin jaziratul arab ne.” lallai sun taki sa'a kuma sun dace. Sai dai basu san cewa akwai ragon azanci a amincewa Malik. Musamman yadda tambarin shahararsa tasa ya fantsama yayi wanka da munanan ayyuka ba, mutum ne ya yayi wanka da zunubai babu iyaka.
Don haka suka bada yardansu tare da yarjejeniyar habbaka Kasuwancinsu. Amma ya boye musu makasudin amsar alaƙarsu.
“Batun ma'aikatanku da suke hannunsu, zan amso su kafin rana tayi tsakiya.” ya duba agogon hannunshi. Sannan ya juya yana kallon Fahad. “Albagwi alkawari.” gyada kai yayi, sannan ya fita. Bin bayanshi suka yi da idanu. “Mayor hankalina bai kwanta da Mutumin nan ba, idan abun nan ba zai yiwu ba, mu hakura ko Yamini?” murmushi yayi sannan ya ce mishi.
“Ni kuwa naji kamar alkhairi, koda kuwa akwai matsala ba zai gaggare mu ba. Kwantar da hankalinka.” haka suka amince da Malik domin kiri-kiri Alhaji Nasr Hadejia yaki karban Malik, ba don kome ba. Sai don sanin duk inda aka samu dan daba zai yiwu ya ki taimakawa yan uwansa.

Shu'iba da Dulma.
Malik ya jima yana nimansu, ba don kome ba sai don akwai tsohuwar gaba, wanda suka jima da shi a ransu, sai dai bai samu damar ramuwa ba, domin kuwa basu tab'a zama wuri guda. Asalima wasan boya suke da shi, shi kuma yayi alƙawarin duk wanda ya gaya mishi inda suke zai mishi kome, ana haka Fahad Albagwi ya tura mishi sakon ganinsu. Ana gab da zaben kasa.
Dulma dan uwan Shu'iba ne, kaninshi cikin su daya, a duniya babu abun da Shu'iba yake so sama da Dulma, domin ta kai, hatta matar da ya aura tunda Dulma ya ganta ya ce, yana sonta. Babu musu Shu'iba ya bar mishi ita. Karshe azaba da wahala ya kashe Yarinyar, tun daga lokacin Shu'iba ya samu damar auro mata Dulma ya shiga abin da yake so da su.

Hill and Tim town.
Ana kiran wurin nan haka ne, sakamakon duwatsun da suka kewaye wurin, kuma akwai ma'adinai irinsu kuza, ana hakarsa na fitar hankali. Ba ƙaramin samu suke ba. Sannan sun kwashe maza matasa da yan matasa,. Suke musu wannan aikin cikin azaba da wahala, dalilin wannan dukiyar da yake kasa yasa suka watsar da duk wani cigaba da ya dace su samu. Musamman a fuskar garin, domin idan suka gyara garin su waye zasu musu wannan aikin? Duk matasa zasu samu abin yi. Shi yasa wurin suka kawata shi da nauyin azaba kala-kala. Babu wanda ya isa ya gudu, akwai zakuna masu gadin mutanen, domin kuwa idan mutane suka ne gudu bude zakunan ake suyi fata-fata.
Koda Malik ya bar ofishin gwamnati, bude motarshi yayi, masu kula da lafiyar shi suka fito suna me niman take mishi baya, d'aga musu hannu yayi. Ya dauki wata local gun, sannan ya shiga motar bayan ya dauki wata glass na Prado ya saka a fuskarshi, fuskar shi a kame, na zaka ɗauka yana dariya ba.

Haka ya juya ya fita, a duk lokacin da yayi irin su wannan shirin, tabbas ba ƙaramin al'amari ba ne, jinjina kai Elbashir Jamal Arab yake, yana faɗin. "Allah ka jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya, amma tabbas maza sun fita farauta." Haka ya koma cikin motar ya zauna, tare da kunna wakar rosta.
Tafiyar kilomita bakwai ya kai shi, Hill and Tim town.
Tun kafin a bude mishi kofar shiga town din ya fara musu barna, har ya isa cikin sansanin, koda yake fushin sa ba a kan kowa yake saukewa ba, akan wadanda suka tab'a shi ne.

*present*
Koda yake kusan rabin ayyukan da tayi, bata jin akwai wanda ya kai na yau, shi yasa tayi kokarin ganin ta nime haduwa wani dan kasuwan da zai zuba jarinsa. Sai dai batayi nasarar haduwa da shi ba. A gajiye ta fito daga ginin ta fito inda Black yake jiranta, wurga jakarta tayi tana faɗin. "Wash Allah na!" Ta zauna a cikin motar tana mika. "Ina zamu?" Idanunta a lumshe ta ce. "Akwai inda yafi gida ne?" "Babu" ya bata amsa, sannan ya ja motar suka bar wurin.
"Chairman! Yarinyar nan ta kawo abin da bamu zata ba, mu kyaleta haka!" Murmushi Mr Amjad yayi ya ce mishi. "Ban gama gamsuwa ba, sai tayi min abin da3 zan barta. Amma ka sani duk kudaden da take samo mana, na hannun jari bai kai na babban kifi ba." Shiru MD yayi ya ce mishi.
"Akwai matsala, idan har aka sake kifin ya sake ya zama me k'aya za a wahala."
Chapter 10 · 0% Book details