← Book details Carbin Ƙwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 17

Sashe 9

Carbin Ƙwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Adurk'ushe yasamu Mum tana kuka mai cirrai muryanta ma baya fita sosai Granny na zaune akan sofa dake kusa da gadon tad'aura k'afa d'aya kan d'aya tana ta girgiza kai alamun ranta amugun b'ace yake, Waje yasamu yazauna akan bed yana kallon su shima d'in yanzu matar Dad d'in shi ta'bata mai d'an farin cikin dayamu ayu d'in na labarin dawowar small Mom d'in shi gyaran murya yayi yana kallon Granny yace

"Granny idan rana tafito tafin hannu bai isa yakare ta ba Mom dakike gani *CARBIN ƘWAI* ce mai wahalar janyuwa kuma janta sai natsatse ba irin watsatstsu kamar matar Dad ba kudaina tada hankali akanta domin batasan inda yake mata ciwoba har yanzu ni a mahaukaciya nad'auke ta k........"

Baram sukaji anbanko k'ofa wanda hakan yasa suka maida hankalin kacokan ga k'ofar Dad ne da matar shi gaba d'aya ransu amugun b'ace suke kallon Granny Fatima daketa kuka har yanzu da Samran da kejifan su da kallon uku saura kwabo shima,
Cikin fusata matar Dad tace "Kajima kunne ka ko? Sunata zagina bansan me na tsarema bayin Allahn nan ba daga fad'in gaskiya abu yazamn min d'an zani, bakaman wannan yaron me ba'kin hali irin na yahudawa" saikuma tafashe da kuka tana kallon Daddy wanda shikuma hakan yasake b'ata ranshi

Cikin b'acin rai yace "Kai Samran rashin mutuncin ka ya isheni fa kakiyaye nifa inba so kake namaka baki ba mata ta amatsayin uwa take agareka abun yawuce rashin kunya yanzu harda zagi da cin mutunci saika ga mutane kadinga sum sum kamar munafiki kafa kiyayeni!"

Kan shi kawai yake kad'awa cikeda mamakin matar Dad yabud'e baki zeyi magana Granny takad'a mai Kai alamun yayi shiru,

Cikin sake so ta tunzura Dad tace "wai daga fad'in gaskiya nace saidai akai Shuwara can wajen dangin ubanta mu baza mu ri'ke shegiya ba sabida kar sunan family ya'baci shine d'an nan yatareni yanata gasa min maganganu kamar zai dake ni dole na kauce natafi kiranka shine mukaji yana cemin mahaukaciya gaskiya nibazan yarda ba kamin iyaka da wannan munafikin d'an naka"

Cikin b'acin rai Samran yadube ta daga ita har Dad d'in yace "Alhamdulillah da nayi farin ciki matu'kar za'ai min iyaka dake alak'ar mu dake babu abunda ya'kare ni dashi inba ba'kin ciki da nadaman sanin kiba mtssss" yaja wani shegen tsaki zai wuce Dad yace

"Samran agabana kake cima Mata na mutunci maza kadawo kabata ha'kuri yanzu kona tsine maka albarka!"

Cikin d'an mamaki Granny takalli d'an nata datake kyautata zaton baya cikin hayyacin shi yana cikin mayen sihiri tace "Suleiman kana tsine ma Samran kaima zan tsine maka yanzun nan kai Samran!" Takira shi da kakkausa-llafazi

Samran daya shiga shock da tashin hankali yakasa gaba yakasa baya ranshi sai suya yakeyi k'wallah tacika mai idanu ga kanshi dake masifar sara mai kamar zai cire dan shi ba ma'abocin yawan magana bane ahankali yajuyo yakalli Granny data mi'ke take kallon shi tace "jeka abinka Allah ya albarkaci rayuwar ka yakare ka daga sharrin mahassada da ma'kiya nafili dana b'oye" ajiyar zuciya yasauke ya amsa da "Amin" asanyeye yajuya yabar room d'in

Kallonta tamaida ga Fatima dake janyo trolley tana kuka wayanta ahannun ta alamun kira zatayi, cikin wani b'acin ran daya taso mata kawai itama saita fashe dakuka tazauna akan kujera jabb'ar dasauri Daddy yayo kanta matar shi kuwa saita juyar dakanta gefe tana jan tsaki dan ita bahaka taso ba,

Mom dake shirin kiran Shuwara tazo sukoma dan dama tasan hakan zata iya faruwa cikin tashin hankali tayarda wayan da trolley d'in tayo kan Granny ganin halin data shiga.

________________________________________________________________

Yammacin ranan Minal tadawo daga wajen lalle da gyaran jiki tana zaune ad'aki tana aikin chat kawai saiga text yashigo ta k'aramar wayarta kamar bazata duba ba saikuma tajanyo wayar cikin tashin hankali tami'ke tana sake karanta text message d'in kamar haka
_*Amarya Minal kinsha k'amshi mata awajen Samran Suleiman Jabbar duk dacewar ba'a gayamin aure ba amma nasamu labari agari dan haka inason ki kawo min kanki yanzunnan kona turama Samran dukkanin abubuwan damuke aikata wa nabaki nan da one hour KO kixo kona tura mai komai yanxunnan!*_

Gaba d'aya duk da sanyin AC dake d'akin hakan bai hanata jik'ewa sharkaf ba take cikin ta yakatsa da gudu tanufa toilet tana shiga taji zawo zuuuuu takusa minti biyar zawo na zuba da'kyar tasamu tafito daga toilet d'in gaba d'aya neman kuka tayi tarasa bata ta'ba tunanin Jibson zai samu labarin auren taba itako tashiga uku tabani talalace wayar tad'auka tadnnan mai kira amma harta tsinke bai d'aga ba atak'aice saida tayi mai miss call sama da talatin amma no response ganin ya'ki d'aga kiran tane yasa tad'auki key tafuto cikin tashin hankali taja motar,
Motan ta nafuta nasu Aunty Nafeesa nashigowa cike da mamaki Aunty tabi motar da kallo aranta tace any'a Minal lafiya take kuwa? baki tad'an tab'e ta'karisa tayi parking suka shiga cikin gidan.

Minal kuwa tafiya tayi sosai ta iso wani katafaren guess house mai suna *JIBSON GUESS IN* agigice tayi parking tafito tanufa cikin wajen.

________________________________________________________

Samran kuwa yana futa daga side d'in Granny directly park lot yanufa driven shi naganin shi dasauri ya'karisa yabud'e mai yashiga yatada saida suka hau titi ne driven yace "Yalla'bai ina muka nufa?"

Kanshi yad'an shafa yanajin yanda zuciyar shi ke bugawa yalumshe idanun shi sannan yazaro yawar shi Samir yakira saida takusa tsinke wa yad'aga yana fad'in "Allah yatai maki Dr mu!" Ya'karisa maganan cikeda barkwanci,
D'an tsaki Samran yaja sannan yace "kana gida ne?"
Samir jin yanayin muryan shi yasa yagane ba lafiya ba dan haka yace "Ina Jibson guess in muna meeting da y'an company Dad kasan baya gari koxaka zo nan kasame ni?"
Batare da Samran yayi magana ba yakashe wayan yana kallon driven shi yace "Jibson guess in xamuje"

"Okey sir" take driven yad'auki hanyar Jibson guess in

_______________________________________________________

*BAYNUUR*

Tunda tadawo take cikin tashin hankali da rashin sanin madafa game da Barbushe sai sa'kawa da kwance wa take cikin rashin sanin abun yi tanufa turakar Sarki Abdul-Jabbar,
Yana kinshin gid'e yana lazimi sanyen da farar jallabiya ga fruit agaban shi da alama baijima dagama ciba batare datayi sallama ba tashiga tasamu waje tazauna tana fad'in "Yallab'ai sannu da hutawa ya daren? Ashe kuma mun samu k'aruwa to Allah yaraya mana"
Batare daya d'ago ba yace "firstly kije kiyi sallama sannan na amsa miki dukkanin maganganun ki"

Cikin d'an kun k'une dan tasan halin shi tami'ke tafuta tayi sallama tana zama saiga Gimbiya Tahaliyya tashigo sai bazan k'amshi take cike k'asaita take tafiya ahankali ta'karasa ga Mai martaba tana murmushi batare data kalli inda Fulani take ba tace "Barka da warhaka jarumin mu kuma sadaukin mu"
Cikin murmushi yace "Barka dai Gimbiya fatan kin iso lafiya"
Wani fari tayi da ido tana sake matsawa ga sarki tace "Alhamdulillah fatan ba wata matsala?"
Kafun sarki yayi magana sukaji muryan Fulani afusace tana fad'in "Wannan wani irin wula'kanci ne nazo wajen ka kashare ni wata tazo sai fira kake mata gaskiya bazai yiwwuba dole duk yanda za'ai ayi"
Wani murmushi yasaki yana kallonta harga Allah shi yama manta da ita ad'akin kallon shi yamaida ga gimbiya Tahaliyya daketa faman danna waya kamar batasan me Fulani take magana akai ba ahankali yabud'e baki yace
"Kindai san yau ba ranar ki bace kuma kece kika saka doka akan duk ranan girkin daba na wata ba to wacce ba ita bace da girki bazata shiga turaka da dare ba toke meya kawo ki?"

Wani irin b'acin raine yashigeta yahad'e da ba'kin ciki da tashin hankali datake ciki yamata rubdugu lokaci d'aya batare data tanka ba tajuya bagazam bagazam tabar room d'in, tana ta sa'ke saken yanda zata gyrama Gimbiya Tahaliyya zama daga ita har Mai martaba Abdul-Jabbar d'in.

_________________________________________________________

Suna xuwa Jibson guess in yakira Samir yashaida mai cewar gasunan awajen room number kawai yafad'a mai yace yasame shi awajen.

D'an tsaki yaja dan bai cika son zuwa kalan wajen nan ba yafito yafara tafiya ahankali kamar mejin tausayin k'asa gaba d'aya kanshi a'kasa yake kamar me irga step d'in shi sosai yarame ya'kara fari idanun shi sun k'ara girma haka hancin shi kamar biro pink lips d'in shi yayi ja_ja_ja pink pink kallo d'aya zaka mai ka gano rashin kuzarin dayake ciki tundaga yanayin tafiyar sa yana shiga yayi kwana zuwa hanyar dazata sada shi da stairs domin hall d'in yana sama ne, yaxo k'ofar dazai sada shi da stairs d'in har yafara taka d'aya biyu ana uku kawai yaji yayi karo da mutun take wayar shi tafad'i haka itama waccce sukai karon tare wayarta tafad'i duk wayoyin suka gangara k'asa, atare suka d'ago kai zaiyi magana kenan maganan yamak'ale abakin shi.............✍🏼

*Dan soyayyar ki da fiyayyen halitta annabi Muhammad s.a.w inkin karanta kiyi sharing sauran group d'in da'ki'ke ciki*

*Wannan littafin na kud'i ne akan farashi me sau'ki inkinaso zaki tura 400 ta 4210014214 lawal shamsiyya eco bank shaidar biyanki ta 07042682333 y'an VIP zasu tura 700 domin samun posting kullum, KO katin waya mtn or airtel ta 07017296839 bana son vtu hoton katin za'a turamin y'an Niger kuma sumin magana ta 07042682333 don jin yanda zaku tura kud'in ku*
[8/27, 7:35 AM] Ummu Sumayya: 🌺🌺🌺🌺
*CARBIN ƘWAI*
```Mai wuyar janyuwa```

*Writing and Story By*
```Ummu Sumayya ```
*Babybintu*
📿📿🥚

*DEDICATED TO*
*NAZEEFI N YAREMA*
Chapter 9 · 0% Book details