← Book details Carbin Ƙwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 17

Sashe 3

Carbin Ƙwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cike da nishad'i yashiga dajin danshi arayuwar shi yana matu'kar son farauta kamar me bayan yagama yawata wa acikin dajin yau farautar tazo mai da sa'bani bai samu abunda yadace yafarauta yakoma dashi masarautar ba dan shi abun kuny'a ne yakoma da k'aramar dabba masarautar amatsayin abunda yafaruto atushen wata bishiya yazauna yaci y'ay'an itatuwan da'aka sakamai amatsayin guzurin shi sannan yahuta yayi sallah yasake nausa wa cikin dajin amma cikin ikon Allah yau bai samu komai ba haka yajuya yakoma masarautar da yammaci direct yaje ya aje dokin fadawa nata mai kirari shiko saboda tsabar k'asaita ko d'aga kai yakalle su baiyi ba haka yanufa side d'in shi cikeda gajiya wanka yafara yi yashirya cikin wani tattausan yadi fari shara shara turare yafesa sannan yad'aura alkyabba fara mai ratsin blue wacce tai masifar yimai kyau takalmi halp cover blue yasaka cikeda k'asaita izza da nuna shi jinin saurauta ne yake tafiya wani b'angare dake cikin gidan sarautar yanufa y'ar tafiya kad'an ya iso Masha Allah shima ya had'u sosai tun daga balcony bayi keta zube wa suna kwasan gaisuwa amma ko kallo basu ishe shiba har yashiga babban palourn daya k'awatu matu'ka da kayan more rayuwa daganin palourn kasan mamallakiyar sa jinin saurauta na yawo ajikinta duba da yanda kilisai da tum tum sukaima palourn k'awan'ya ahankali yayi sallama wata dattijuwa fara mai tsananin kama dashi ta amsa murmushi shimfid'e afuskanta tace
"Barka da dawowa magajin sarki fatan farauta tayi dad'i"
Fuska yad'an b'ata sannan yasamu waje yazauna yana kallonta gamida furta
"Wash Momma nagaji" yafad'a yana nutsewa amany'an sofan dasuka ma palourn k'awany'a batare da ya bata amsar tambayar data mai ba,
Dariya tayi wanda yabayyana ainihin hak'oran gwala gwalan dake jere abakinta guda hud'u tad'an d'aga murya tace
"Kuluwa ki kawo ma magajin sarki abinci yanzu"
Wata dattijiya ce tafuto taduk'a agabanta tana sauraran umarnin ta kafun tafurta
"Angama ranki shidad'e" ta'karisa maganan cikeda girma mawa sannan tajuya tabi wani corridor da alama dai anan kitchen d'in yake
Lumshe idanun shi yayi kamar me barci
Bata wani jima ba tadawo da k'aton tray wanda aka shak'o da kayan ciye ciye da had'add'iyar jelop d'in shinkafa data wadatu da kayan lambu sai ruwan y'ay'an itatuwa da aka matse su akasa sugar kad'an zuba mai komai tayi jikin ta nata karkar wa da alama dai atsorace take kar uban gidan nata yace tayi laifi saida tagama zuba mai komai sannan cikin girmama wa tace
"Atashi lafiya ranka shi dad'e"
Tajuya tabar palourn cikin sauri
Kusan ten minutes sannan yafara tsakurar abincin kamar baya son ci Momma nata kallon TV lokaci lokaci takan kalle shi tasaki wani k'ayataccen murmushi
Kusan mintuna talatin yakwashe yanacin abincin kafun yasha ruwan y'ay'an itatuwan dashi ne yace adinga had'a mai dan baicika son drinks ba yafison natural saida yakammala tsaf sannan yatsinkayi muryan Mamma tana fad'in
"Mai martaba yace yana son ganinka bayan sallar magrib"
D'an zaro many'an idanun shi yayi yana rolling d'insu kafun yace
"Allah yasa ba wani laifin za'a ce nayiba" ashagwab'e ya'karisa maganar kamar wani k'aramin yaro
Cikin fara'ar daba tacika yiba tace "babu abunda kamai alkhairi ne inkazo kaji"
Shiru yad'an yi kafun yamotsa labb'an shi yace "Allah yakaitace no
Yana fad'in hakan yami'ke yana kallon Rolex watch d'in hannun shi yace "Uhmm bara naje nayi sallah lokaci yagaba to"
"Adawo lafiya magajin sarki"
"Allah yasa" yafurta ahankali sannan yabar palourn cikin k'asaita

*UHAIRA*

Bayan tatashi sama cikin iska tanufa *BAYNUUR* kafin ta'karisa birnin saita sauka awani daji domin tahuta takuma fara tunanin abunda yadace tayi domin d'aukar fansa ga wannan alhli na masarautar Baynuur kafun tahalaka su ta mulki garin mulki irin na xalunci
Tana sauka awani tsauni saiga wata iska mai tsananin k'arfi tanufo inda take, take wajen yayi duhu k'asa ta soma girgixa UHAIRA ta tsaya tana kallon iskar har tasauka agabanta sannan wani k'aton ba'kin aljani yabayyana agabanta cikin hayak'i da wata mummunar suffa mai tsoratar wa sannan yafad'i agaban UHAIRA da jinjinar girmamawa yace
"Daraja taki ce sarauniyar matsafa ta duniya nazo ne nataimaka miki akan abunda kike shirin yi nad'aukar fansa akan masarautar Baynuur"
Cikin rashin yarda tadube shi dakuma mamaki tace
"Waye kai kuma ya'akayi kasan labarina da abunda nake shirin aikatawa har kake shirin taimaka min?"
Aljanin nan yayi kaki yatofar da wani abu kamar garwashin wuta sannan yaduba matsafiya UHAIRA yace da ita.

ლ(́◉◞౪◟◉‵ლ)

Tajima acikin motan kafun tamata key tabar gidan bawani nisa tsakanin su cikin minti Ashirin ta Isa gidan, Granny takira awaya tafad'a Mata tana bakin get
Get man Grannyn takira awaya tafad'a mai akwai bak'uwa yabud'e mata tashigo
Building ne kamar aturai mai matu'kar girman gaske yak'awato da fulawoyi daga gefe ga lambu nan da swimming pool gunun ban sha'awa security ne azube kusan goma kowane sanye da kayan police no
Ahankali takashe motan tafito tana tafiya cike da ta'kama tanufa ainihin cikin gidan
Bakowa aciki sai k'amshin air freshener daya had'u da sanyin air condition suka bada wani sansany'an sanyi mai had'e da iska lumshe ido tayi saboda sanyin AC d'aya bugeta directly tawuce bedroom d'in Granny tana k'wala mata Kira
A'kofa sukaci karo dattijuwa k'yak'yawar bafulata na Wanda tsufa bai b'oye k'yawun taba saboda hutun daya bayyana atare da ita,
Murmushi kwance bisa fuskarta take kallonta tace "lale lale marhabin da minalli barka dazuwa muje palour kinji d'iyar albarka"
Kai ta sunne suka nufa palourn, har k'asa tadu'ka tagaida granny, itako granny sai washe ha'kora take me aikinta takira tace takawo Mata abun motsa ba'ki
Kafun kace kwabo tuni ancika gaban Minal dakayan motsa baki, ahankali take cin samosa suna fira da Granny tana tambayanta mutanen gidan su tana bata amsa, haka suka kasance har yamma sannan suka shiga kitchen kamar yanda tasan SAMRAN Yana son Sinasir da miyar alayyahu dan haka tazage tashirya Mai komai cikin tsari sai biyar takammala taje d'akin Granny tasake she'ka wanka already tazo dawani kayan tasauya tayi heavy make up sosai tayi kyau kamr kasaceta lolz.
Shida daidai yadawo agajiye yanufa side d'in shi saida yayi fresh up sannan yanufa side d'in Granny dan yagaisar da ita kamar yanda yasaba,
Suna zaune akan carpet suna ta'ba fira jefi jefi Amma gaba d'aya hankalin Minal nakan k'ofa burinta kawai taga SAMRAN domin tunda taji diran motan shi taso zuwa Amma Granny tahana ta dole taha'kura,
Koda yashigo kallo d'aya yamata yakauda kanshi gefe ya'karasa wajen Granny yakwantar da kanshi a shoulder d'inta cikin shagwa'ba yace
"Uwar gida ran gida wallahi nagaji sosai gashi magrib takusa kuma yinwa nakeji yanzu yaza'ayi??" Cikin tsantsar sangarta ya'karisa maganan yana wani lumshe idanu,
Dariya tayi tace "to nidai kad'agani kafun nabaka amsoshin tanbayoyin ka ragon dacta kawai"
Murmushi yayi wanda yabayyana sihirtaccen k'yawun shi har two dimple d'inshi suka lotsa yace "Granny Dr ake cewa ba dacta ba"
Wata uwar harara tamaka mai kafun tace
"To ni bazan iya fad'in hakan ba yanzu dail bakaga Minal bane?"
Cikin d'an shafa sajen daya k'ara ma fuskan shi kyau sannan ya yamutsa fuska kamar bazaiyi magana ba saikuma yace
"Yes bangan taba" yafad'a Yana waigawa alamun Yana neman inda Minal d'in take
"Kaci kaniyarka d'an nema ga yarinyar arziki nan agefena Kuma nasan kaganta ai" cikin d'an b'acin rai ta'karasa maganan,
Cikin kwantar dakai yace "haba uwar gida ran gida meye na'bacin har haka amaganan nan fisabilillah inace ni yakamata yarinyar nan tagaisar Amma wai nine za ace bangan taba ahaka KUKE cewa na aureta Bata girmamani gaskiya dasake" ya'karisa maganan yana jingina kai da kujeran dayake kai
Cikin lallami Granny tace "to uban Y'an son girma sannu wanda yayanke ma k'asa cibiya ke Amina gaisar dashi azauna lapiya"
Minal datun shigowar warshi tayi mutuwar zaune kallon shi kawai take domin ita komai yayi birgeta yakeyi firgigi takalli granny tace "me kikace granny?"
Kafun granny tayi magana yaja tsaki gamida mi'kewa yabar palourn cikin sauri dan bai son ta tsayar dashi.
Cikin rashin jind'ad'in abunda yayi Granny tabud'e baki da niyyan ba Minal ha'kuri Amma saita tari numfashinta tace
Chapter 3 · 0% Book details