← Book details Carbin Ƙwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 17

Sashe 15

Carbin Ƙwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Afirgice tatashi zaune saikuma tami'ke ganin inda take idanuwa tafara wuwwurgawa da tunanin meye yakawo ta gefen gari duk yanda taso tuna abunda yafaru kasawa tayi dan haka tafara tafiya cike da k'asaita bayan tad'an kakkab'e k'uran ta gyaggyara jikin da takaicin itace ahaka babu mota tafiyar kusan five minutes kafun taga motar ta daidai fadar Barbushe saikuma ta tuna ai wajen shi tazo to meye yakaita can tsaki taja afili sannan tanufa motar ta tana ta sa'ke sa'ken ya akai ta tsinci kanta acan wajen direct fadar tashiga taganshi zaune kanshi aduk'e kamar yanda tasaba taduk'ar dakai tana fad'in
"Shaid'an yatai maki sarkin sarakunan bokayen duniya tsinanne irin tsiya naxo baka ha'kuri ne agafarta min amin rai"
Wani irin kallo Uhaira ta watsa mata kafun tasake gimtse fuskar ta dababu kyan gani tace "Jaririya na gafarta miki dan haka ki kiyaye gaba"
Fad'i tayi a'kasa tace "godiya nake shaid'an sarkin sarakunan bokayen duniya ba'ai kamar kaba bakuma za'ai ba har abada"
Wani irin nishad'i Uhaira taji dan ita aduniya babu abunda zaka mata ka burgeta irin kirari tana son fadanci tun tana y'ar mitsitsiyar ta cikin alfahari tace "sihiri da tsafi gaskiyar me shi yanzu yakike so ayi da sarkin dakuma amaryar tasa akashe sune duka kokuwa yaya kike bu'kata"
Cikin kask'antar dakai tace "so nake asama Gimbiya mantuwa tayanda bazata ta'ba gayama sarki abunda taji ba sannan akara cusa ma sarki tsanar ta kamar lokacin baya yazamana kome aka tattauna afada daya dawo zai gayamin inaso amin abunda Sarkin k'ofa da sallama Jakadiya da Talba zasu dinga jin tsoro na domin naga kamar sun fara gano ni sannan inaso ad'aura na sarki cuta yayita rashin lafiya kafun akashe shi yanda baza'a zarge niba kafun yamutu mushawo kan Ja'afar dazarar ya mutun kaga babu matsala sai na d'aura shi akan mulki naci gaba da juya Baynuur"
Wata shegiyar dariya Uhaira tasaki kafun tace "angama tukwicin aikin ki jinin jaririyar surukar ki matar Ja'afar"
Babu damuwar komai tace "godiya nake shaid'an sarkin sarakunan bokayen duniya ba'ai kamar kaba bakuma za'a ta'ba yiba har abada tsinanne d'an tsinnaniya"
Turb'une fuska Uhaira tayi tunafa wannan kirarin Barbushe akemawa ba itaba cikin tsawa tace "la'annniya irin tsiya tashi kibamu waje"
Dasauri tami'ke zata juya Uhaira tadaka mata tsawa tace "ke annamimiya wacce bata ba gafara da baya baya zaki futa kona sa D'an Tsito yashanye miki jinii yanzu nan"
Jiki na kakkarwa tajuyo tafara tafiya da baya baya kafun takai motar ta tafad'i yakai sau biyar dasauri tafad'a motar tana sauke ajiyar zuciya kafun tamata key tabar wajen wani nishad'i na shigan ta afili tafurta "Tun da aka hana d'ana mulkin Baynuur na rantse da k'arfin tsafin Barbushe saina mulki Baynuur mulki irin na zalince saina maida duk wani ahalin Gimbiya Tahaliyya da Sarki A-jabbar bayi na" tafad'a tana buga sitiyarin motan da k'arfi,
Tana isa gidan tafuta amotar cikin k'asaita take takawa har zuwa sashin ta,
Kiran sallar la'asr ne yatadar da Gimbiya Tahaliyya inda ta sillo wanka sannan tashirya tsaf cikin alkyabba fara wacce akamata ado da pink d'in zare sosai tayi kyau sallah tafarayi kafun tafuto cikin k'asaita take d'aga ma kuyangin dake ta gaisheta hannu zama tayi tana mi'ke k'afafun ta amintaciyar baiwarta tafara mammatsa mata k'afan tana fad'in "Allah ya'kara ma Gimbiyar Baynuur lafiya da nisan kwana me albarka Allah yakare mana Gimbiyar masarautu biyu kidad'e kiyi k'ark'o Gimbiyar mu me share mana kukan mu"
Murmushi tasaki cikin k'asaitar ta da ajinin ta take cikin ginshira takai fork d'in data cako Apple d'in da aka yanka mata bakin ta tauna shi tayi ahankali tana lumshe ido saida ta aje fork d'in sannan takalli wata baiwa dake can gefe azaune tace "Agaya ma jakadiya nace aje sito ad'ebo kaya ararraba ma duka bayin gidan nan sannan araba sabbin uniform ga duk bayin gidan nan aba Suhaima shadda yadi goma goma guda biyu da atamfofi biyar"
Dasauri duka bayin suka zube suna godiya kafun kunyanga tafuta dan cika umarnin Sarauniyar,
Can wajajen magrib babu kowa a palourn daga Gimbiya sai Amintaciyar baiwarta datake ta godiyar kayan da aka bata kamun ta nisa tace "Allah yataimaki Gimbiyar mu akwai wani mummunan abu da ake shirin k'ulla mikifa!"
Juya kanta tayi tana kallon suhaima anazarce kafun ta bud'e baki tayi magana Jakadiya tashigo da gudu raf raf tazube tana maida numfashi tace "ranki shid'ad'e mummunan labari ki gafarce ni ga me martaba can yafad'i ba yanda yake
Amugun rud'e tami'ke tana fad'in "innalillahi wa-enna ilaihirraji'un meyas....." Tadafe kanta daya mugun sara mata kawai itama sukaga tayanke jiki tafad'i dasauri sukai kanta cikin tsananin tashin hankali

_________________________________________________

Minal ce da wata k'awarta Fatima zaune agaban wani boka tana ta rusa kuka wata gigitacciyar tsawa boka yadaka musu wacce tasa dukkan suka shiga hankalin su fuskar shi ad'aure data kara mai muni yace "shin mekuke bu'kata yanzu inbaku da abunda za'a muku k'ofa abud'e take"
Jikin Minal har rawa yake tace "katai maka min boka ina son Samran inban mallakeshi ba zan iya rasa raina"
Wata shegiyar dariya yafashe da ita wanda tasa kaf dajin ya amsa hanjin cikin su yay mugun kad'awa suka sake natsuwa,
Saida yayi me isarsa kamun yad'aure fuska yace "Hanya d'aya ne zan baki abunda za'ai kije kiyi za'ai auren amma auren bazai wuce kwanaki goma ba zai warware sabida wani al'amarin dake tun karo shi wanda ni kaina banganshi ba nikuma zan k'ara mai k'arfin sha'awa yanda gobe idan ankaiki zai kusance ki kinga koda yadawo hayyacin sa yasake ki idan ciki yabayyana za'a tilasta shi yadawo dake daga nan saimuci gaba da sauran ayyukan ammafa ki kiyaye!"
Jiki na kyarma tace "na amince zanyi duk yanda kace"
"Wannan abun da za'ai mai idan har akasamu akasi agoben komai zai rushe miki za'a samai sha'awa mai tsanani tayanda kowacece indai macene tazo garesa zai aikata akanta ki kula kuma bashi da makari na baki!"
Dasauri tagyad'a kai tace "na amince"
Wani abu yami'ka mata yace taje yau tsakiyar dare tatashi ta tub'e tashafe jikinta sau goma da maganin intayi na farko yabushe tasake yi karta kuskura maganin yata'ba gaban ta saida yamata kashedi sosai sannan yasallame su yace abin biya na aiki shanuwa zasu siya ba'ka da zanin mahaukaciya sukawo bakin jejen su tafi godiya sukai mai sannan suka taho,
Wata shegiyar ajiyar zuciya Minal tasauke tana kallon Fatima dake driving a kwazazzaban dajin dasuka k'urmusu kansu afili tafurta "Fatima na gode Allah yabarmu tare bisa amana gaskiya ban ta'ba tunanin haka daga garekiba"
Murmushi Fatima tayi tace "Ayya rashin sharing experience ne yasa aka kawo war haka da tuni kinjima da mallakan Samran ai kece kin cika k'arya akan soyayyar ki dashi banda hakaba waye Samran d'in da yanzu anjima da wuce wajen"
Ajiyar zuciya tasake sauke wa tace "na gode Fatima ban san haka abun yake ba amma komai yazo k'arshe"
Tattaunawa suka ci gaba dayi harsuka iso gida inda suka shiga gidan tare suka baje a d'akin Minal d'in dake cike da k'awayen ta dasuke ta firan auren da za'a d'aura gobe zama sukai aka dasa sabuwar fira anata shewe shewe cikin nishad'i.
Kusan k'arfe 2:20 tafarka tana fad'in "Ibrahim dama baka mutu ba oh ya Allah Shuwara where are you ga Abban ki bai mutu ba come closer kiganshi kafun na farka daga mafarkin n...." Wani irin zabura tayi Samran yamaida ta..........✍🏼

*Dan soyayyar ki da fiyayyen halitta annabi Muhammad s.a.w inkin karanta kiyi sharing sauran group d'in da'ki'ke ciki*

*Wannan littafin na kud'i ne akan farashi me sau'ki inkinaso zaki tura 400 ta 4210014214 lawal shamsiyya eco bank shaidar biyanki ta 07042682333 y'an VIP zasu tura 700 domin samun posting kullum, KO katin waya mtn or airtel ta 07017296839 bana son vtu hoton katin za'a turamin y'an Niger kuma sumin magana ta 07042682333 don jin yanda zaku tura kud'in ku*
[8/30, 1:04 PM] My Sisi: 🌺🌺🌺🌺
*CARBIN ƘWAI*
```Mai wuyar janyuwa```

*Writing and Story By*
```Ummu Sumayya ```
*Babybintu*
📿📿🥚

*DEDICATED TO*
*NAZEEFI N YAREMA*

*LAST FREE PAGE*💃🏽😍

*PAGE TWELVE*
Chapter 15 · 0% Book details