← Book details Carbin Ƙwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 17

Sashe 14

Carbin Ƙwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Small Mom kuwa tajima tana sa'kawa da kwance wa kafun wayarta tafara neman d'auki "Captain" tafurta afili kafin tad'aga wayar cikin girma-mawa tace "Allah yatai maki Madugu!"
Dariya yayi daga can side d'in yace "Hmmm Auntymu many'an gari yanzu haka ina airport d'in yobe ko kituro min address ko ataimaka azo ad'auke ni naso nayi surprises d'in ki ne sai wayar Shuwara ya'ki shiga hope tana lafiya?"
Ajiyar zuciya tasauke cike da fargabar da batasan KO na menene ba tami'ke tana fad'in "wata tambaya zan fara amsawa yanzu?"
Murmushi yayi yace "duk wacce kika so amma fa yakamata azo ad'auke ni ko aturo min address kar na bushe"
Gyalen ta tayafa tafuto harabar gidan tana cemai "insha Allah ganinan zuwa bada jimawa ba Shuwara tun jiya tabi wata sister d'in ta kuma insha Allah lafiya k'alau ne"
"Ok saikin k'araso"
"Okey" tare sukai handle d'in kiran,
A parking space d'in ta tsaya tana kallon many'an motocin dasuke jere a wajen kallon bakin get tayi taga security kusan goma sai kai kawo suke acikin gidan baki tad'an tab'e aranta tana ta ayyana abubuwa da yawa, daga bayan ta taji tafiya dasauri ta waiga tana kallon Samran dake sanye cikin fararen suit dasukai mai kyau sosai sajen nan yakwanta luf luf kamar ana bashi abinci kanshi a'kasa cike da tausayi tace "Dr sai ina da safe inace kace yau kana zuwa lecture k'arfe goma ne"
Cikin girmamawa yajuyo yad'an duk'a yace "Mom barka da safiya wallahi wasu ne sukai accident yanzu shine zanje naduba su daga can na wuce schl d'in"
"Ayya Allah yakyauta koza ka ragemin hanyan zan d'auko ba'ko a airport yanzu yana jirana inyaso saimu hawo taxi nida shi mudawo"
Murmushi yayi yace "ba matsala muje sai driver yakaiki inya sauke ni"
Cikin amincewa ra jinjina kai,
Parking lot d'in suka k'arasa driven shi naciki shine yabud'e musu suka shiga yaja,
Saida aka aje Samran a hospital sannan aka nufa airport da small Mom,
Suna zuwa tahango su subiyu da wani mutumi suna face d'in gate wani irin lugude zuciyar ta tasaki batasan lokacin data nuna mutumin ba arud'e tafurta.........✍🏻

*Dan soyayyar ki da fiyayyen halitta annabi Muhammad s.a.w inkin karanta kiyi sharing sauran group d'in da'ki'ke ciki*

_*Wannan littafin na kud'i ne akan farashi me sau'ki inkinaso zaki tura 400 ta 4210014214 lawal shamsiyya eco bank shaidar biyanki ta 07042682333 y'an VIP zasu tura 700 domin samun posting kullum, KO katin waya mtn or airtel ta 07017296839 bana son vtu hoton katin za'a turamin y'an Niger kuma sumin magana ta 07042682333 don jin yanda zaku tura kud'in ku*_

[8/28, 6:45 PM] My Sisi: 🌺🌺🌺🌺
*CARBIN ƘWAI*
```Mai wuyar janyuwa```

*Writing and Story By*
```Ummu Sumayya ```
*Babybintu*
📿📿🥚

*DEDICATED TO*
*NAZEEFI N YAREMA*

*PAGE ELEVEN*

```Second to the last free pages kuna ina habibaties🤸🏻‍♀️ 😍🔥 daga gobe nefa🔥 zata fashe guys wad'anda basu siyaba su hanzarta kar abasu labari domin jin wannan salon kafcen cakwakiyar masarautar Baynuur mai cike da sark'ak'iya nabam mamaki da al-ajabi domin wani kayan sai amale 🔥 idan rana tafaso💥tafin hannu baya kareta zakaran gwajin dafe kenan🤏🏼😎 hanzarta kisiya kisha labari ki kuma k'aru kiyi nishad'i🤸🏻‍♀️ kuna ina ku hanzarta💃🏽```

*Masu son atallata musu hajarsu duniya tasan dake kayan ki su zaga su tsallaka inda ke bakije ba chat me 07017296839*

"Ibrahim!......." Tafad'a azuciyar ta tana wani irin bud'e idanun cikin tashin hankali tab'alle morfin motan tafuto batare datajira yagama parking ba jikin ta na wani irin kakkarwa tafara takawa zuwa garesu saikuma tayi baya yif tafad'i,
Cikin tashin hankali driver yafuto yayi kanta yana salati,
Da mugun sauri uncle suka k'arisa wajen Ibrahim yad'auke ta cak cikin tashin hankali idanun shi na zubarda kwalla yasaka ta amotan dayaga tafuto driver da uncle suka shiga suka bar airport d'in dawani irin space arud'e yake bama driver umarni akan ya'kara gudu dan gani yake kamar ta mutu danko alamun numfashi babu duk wani taimakon gaggawa yayi mata amma ba alamun akwai numfashi ajikin ta jijiyar hannun tane kawai take harbawa kad'an kad'an suna isa hospital d'in yasake d'aukan ta yayi cikin reception yana kiran Dr Dr uncle da driver suna biye dashi suma kaf hankalin su atashe,
Dasauri nurses suka taso aka amshe ta akai emergency room yayin da wata tatafi kiran Dr Samran dake ward duba patient cewa yayi taje wajen Dr Samir zai zo idan yagama duba patient,
Dasauri taje ta kira shi sukaje kan small Mom suka rufu mata ana bata taimakon gaggawa,
Kusan thirty minutes yad'auka kafun yagama duba patient d'in yafuto yanufa emergency ward d'in wani irin bugawa zuciyar shi tayi yasake mirza idanun shi yana kallon Ibrahim dake ta faman safa da marwa abakin emergency d'in da bango yajingina saboda jirin dayake k'ok'arin zubar dashi tabbas wannan Ibrahim ne yagani to ya akai aka haihu a ragaya dama be mutu ba tabbas akwai lauje cikin nad'i juyawa yayi zuwa office d'in shi sabida jirin dayaji abakin k'ofa yaga driver da sakatariyar sa da mamaki yakalle shi amma bai tanka ba ya wuce yana shiga yakwanta akan kujera yanajan hasbunallahu wa ni'emal wakeem gamida dafe kanshi dakemai ciwo sosai,
Driver ne yashigo kanshi a'kasa yace "Allah yataimake ka Hajiyar dakace nakai airport wallahi ina zuwa ban gama daidaita parking ba tafuta tafara tafiya kawai sai fad'in ta naji kaf......"
Dasauri yatashi zaune yana fad'in "what tana ina yanzu?" Ya'karisa maganar yana mik'ewa cikin tashin hankali,
Jikin driver na rawa yace "tana nan asbitin mun kawota yanzu haka abokin ka yanacc......"
Bai jira yaji k'arshen zancen saba yafice fit daga office d'in dawani mugun sauri yana zuwa emergency room yatadda har numfashin ta yadaidata anan gyra drip d'in da aka d'aura mata cikin tsananin tashin hankali da damuwa ya'karisa bakin bed d'in datake kwance yace "meye yasame ki haka innalillahi wa-enna ilaihirraji'un" ya'karisa maganar yana d'ora hannun shi asaman goshin ta yana lumshe jajjayen idanun shi,
Da mamaki duk suka bishi da idanu kafun Samir yasallami nurses d'in yakalli Samran atsanake yace "kasanta ne?"
Kai yagyad'a mai kawai batare dayace mai komai ba dan bakin shi yamai mugun nauyi.

________________________________________________

*BAYNUUR*
Chapter 14 · 0% Book details